Chapter Twenty-Nine

515 66 0
                                    

Samha bata bashi ansa ba, ta zira harshenta ta dan laso lips dinta na kasa, sai taji zaki kamar na cake.

Ta juyo tana dubansa sa'anan tace " ya naji kana tasting kamar cake?"

Bai bata ansar tambayarta ba yace "ki jira next stage din, sai na samu lafiya tukuna" Sabah ya fada yana kashe mata ido daya.

Data gano inda zancen nasa ya dosa, bata san sanda tasa ihu ba tana rufe kunnenta ba, ta fita ta bar masa dakin. Shikam Sabah, dariya ya bita dashi, yana girgiza kansa.

Samha sai faman kunkuni takeyi tana magana can kasan ranta, " rana daya bazai wuce ba da bai sakani jin haushi, ko takaici ko kuka ba". Ta karasa maganar tana jan tsaki.

Tana isa dab da dining ta hango ragowar cake din data bashi cikin plate alamun yaci ya rage. Ranta ne taji ya danyi mata sanyi ta karaso ta dauki daya daga cikin fruits din dake saman cake din tasa a baki ta soma ci. Tana gamawa ta haura sama zuwa dakin da Alhaji muazzam ya bata yace nata ne, tana shiga ciki wani irin nauyi taji jikinta na mata, nan da nan ta fada kan gado ta soma bacci.

Sai zuwa yama missalin karfe biyar ta farka, ta fada bayi ta wanke fuskarta sa'ana ta fito daga dakin ta soma saukowa kasa zuwa parlour, abunda ta hango ne yasa ta dakata ta tsaya tana kallonsu.

Sabah ta gani sanye cikin kayan sanyi, blue sweater, da kuma bargo ya lulube kasan jikinsa dashi, yayi kicin kicin da fuska ya bata rai, ga Alhaji muazzam a gabansa rike da kwanu daya dama masa quacker oat a ciki sai fama yake dashi daya bude baki ya karba kamar wani karamin yaro. Sabah sai faman kakaucewa yakeyi yaqi karba.

Alhaji muazzam ya sake debo oat din ya kawo cokalin daidai bakin Sabah yana fadin "Haba baby boy, bude baki mana kasha ko da kadan ne, kaji please. Ban sanka da kunya haka ba fa".

Sabah ji yayi kamar ya kwala ihu don takaici, Samha ta dan labe a bayan step tana kallonsu, tana kokarin rike dariyan da yake neman kubuce mata.

Ganin Sabah yaki tanka masa yasa ya ajiye cokalin yana fadin " menene kuma baby boy? Ina jin bakada lafiya fa na yanke na bar duk abunda nakeyi na dawo. Kayi hakuri nima ba'ason raina bane nake tafiya ina barinka kai kadai ba, don haka yanzu gani na dawo gida, karka ji komai. Oya ahh, bude baki ka karba". Ya fada yana kokarin kara tura masa cokalin oat din a baki.

Sabah ya sake bata rai kamar hadari ya taso ya soma fadin " Abbah wai dan Allah meye haka, ni ka kyaleni, ciwo na zai karu" ya fada yana kawar da kansa gefe.

"Haba Sabah, please open up". Alhaji muazzam ya cigaba da masa magiya.

"Wayyo Allah! Abbah dan Allah mana, nace bazan sha ba".

"Please Sabah..."

Samha dataga abun nasu bana karewa bane yasa ta karaso inda suke tazo suka gaisa da Alhaji muazzam, daga bisani ta fada mishi zata wuce gida tunda jikin Sabah ya danyi sauki.

Alhaji muazzam ya juyo ya soma bata hakuri yana fadin " kiyi hakuri Samha, na barki da jinyan Sabah. Bansan taya zan fara miki godiya ba."

Samha murmushi kawai ta sake tana fadin " Babu komai Abbah"

Wani irin kallo Sabah yake binsu dashi bai ce komai ba. Alhaji muazzam ya ajiye kwanun oat din ya juyo yana fuskantar Samha sa'anan yace " Samha nagode sosai, kuma ina farin ciki da Sabah ya sameki a matsayin kanwarsa."  Yana gama fadin haka, wayarsa ta soma ringing ya tashi ya bar musu wajen dan ya ansa kiran.

Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Samha dajin kalaman Alhaji muazzam tayi shiru tana tunani, " kayi hakuri Abbah, ban jin zan iya zama irin wanan kanwar da kake hango wa Sabah"  ta fada can kasan ranta, tana tuno da abunda ya faru dazun a dakinsa. Kiss din dayayi mata ne ya soma mata yawo a ka, ta sunkuyar da kanta kasa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now