Chapter Thirty - Three

532 62 8
                                    

Bayan tafiyan Sabah, cikin sauri Samha ta dawo inda yan'matan suke tsaye tazo ta tsuguna ta kwaso letters din, hakuri ta sake basu sa'an ta kara gaba tabi bayanshi.

Tana zuwa restroom bata sameshi ba, su Zack ta tadda, nan suka sanar da ita cewa yana wajen senate taje can zata sameshi.

Tana isa senate building , nan ta hango shi kishingide akan daya daga cikin seats da aka zube wajen flowers din jikin senate building, ya lumshe idanunsa kamar yana bacci.

Tana karasowa inda yake kwance ta tsaya tana kare mishi kallo daga bisani tayi gyaran murya tana fadin "Ga sakkoninka nan na kawo maka".

Sabah ya bude idanunshi a hankali ya zube su cikin nata yana kallon cikin kwayar idanunta. Bai ce mata komai ba illa hanunsa daya mika mata alamun ta bashi letters din.

Babu musu Samha ta mika masa, nan ya gyara kwanciyarsa ya soma karanta sakkonin dayan bayan daya. Samha tana tsaye tana kallonsa sai faman kaiwa da kawowa takeyi, duk tabi ta rasa sukuni kirjinta na bugun uku uku.

Sai daya gama karanta sakkonin tass ya dan sake murmushi ya dago yana dubanta  sa'anan yace " wai ku mata gani kukeyi waenan shirmen da kuke rubutawa zasuyi tasiri akan mutum ne ko meye?"

Samha shiru tayi tana kallonsa daga bisani ta bashi ansa da "eh mana. Kai yanzu daka karanta baka ji komai ba?"

Sabah ya bata ansa da " Mai zai hana, ko wani sako dauke yake da kalamai masu sanyaya rai".

Gaban Samha ne taji ya fadi nan take kuma ta soma jin wani iri tace " da kanata yi kamar baka so yanzu kuma ka canza ra'ayi ne ko me?" Ta tambayeshi tana kawar da kanta gefe. Kar dai sakkonin da'ya daga cikinsu ya kwanta masa a rai ne? Ta tambayi kanta gabanta na faduwa.

Sabah ya katse mata tunani da " toh kefa da kike tayi kamar wata babbarsu duk kinbi kin tayar da hankali akansu. Yanzu me naki a ciki idan nace na canza ra'ayin"

Samha bata damu tace "sai ka fada mun, da kake karanta letters din ya kaji?"

Sabah shiru yayi yana nazari daga bisani ya dago ya bata ansa da "kishi na dinga ji"

Murmushi Samha ta sake tana maimaita abunda ya fadi "kishi ka dinga ji?"

Sabah ya mike daga inda yake zaune ya karaso yazo ya tsaya dab da ita yana fadin " A lokacin da nake karantasu, ba abunda ke mun yawo aka illa tunanin irin feelings din da kika dinga ji game da Amjad a lokacin da kike rubuta mishi wanan letter din"

Samha ta marairace fuska ta sunkuyar da kanta ta soma magana a shagwabance" wai dan Allah kai baka mantuwa ne? Abunan fa ya rigada ya faru tun baya shekaru aru aru, sai ka dinga dauko maganar daya rigada ya wuce"

Sabah shiru yayi ya kura mata ido yana kallonta bai ce komai ba. Samha ta kara marairacewa tana fadin "toh shikenan naji, da farko tunanina ne yasoma zuwa wani direction idanuna sun rufe ban san me nake tunani ba".

Still shiru yayi yana kallonta bai ce komai ba. Dataga Kame kamen nata bazaiyi tasiri ba yasa ta soma fadin "badai hakuri kakeso na baka akan wanan abun ba? Toh shikenan kayi hak.....".

"Lafiyan ki?" Ya katse ta "kin wani sunkuya Kinata faman kallon kasa, taya zakiga hasken gabanki?"

Samha a hankali ta dago ta zube kyawawan idanunta cikin nashi. Shima kallonta yakeyi sa'anan yace "kina ganin hasken yanzu?"

Samha murmushi ta sake idanunta kyam a kansa don ta rigada ta gano nufinsa. Wato yana nufin shine hasken gaban nata kenan. Murmushin fuskanta ne ya dadda karuwa ta cigaba da kallonsa tana jin feelings dinta akanshi yana dadda karuwa.

Dayaga kallon ya soma yin yawa ne yasashi fadin "oya kallon ya isa haka, kin wani bude idanu kinata faman bin mutum da kallo. Taya kike so nayi kissing dinki a hakan?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now