chapter thirty-four

469 44 2
                                    

A ranar Samha na dawowa daga makaranta, Ammi tace ta Shirya zasu je gidansu Sabah su gaishe da surukarta wato Hajiya Bilkisu.

Samha jikinta ne yayi matukar sanyi data ji cewa zasu gidansu Sabah su gaishe da kakanshi kuma tasan wanan zuwan da zasuyi, na so ne a gana kuma a samu a tsayar da maganar aurensu.

Jiki a sanyaye Samha tace "toh Ammi".

mikewa tayi ta shiga bayi tayi wanka, ta fito ta soma shiri cike da sanyin Jiki. Bakar Abaya ta sanya hade da bakin gyale, fuskarta babu makeup don powder kadai ta shafa.

Bayan ta gama ta sauko kasa ta tadda Anty fanneh zaune kan kujera tayi jugum sai faman tunani takeyi.

Cikin sauri Samha ta karaso ta nema wuri ta zauna kusa da ita tana tambayarta "Ammi? Ya kuma naga kinzo kin zauna kinyi tagumi. Meya faru?"

Anty fanneh ta saki ajiyar zuciya sa'anan ta dago tana dubanta tace "Samha ban San meyasa nake tajin faduwar gaba a game da haduwar nan da zamuyi da mahaifiyar Abban Sabah ba. Kuma na samu labari cewa matan tanada tsauri dayawa. Anya zamu shirya da ita kuwa? Ni fa dabadin Abban Sabah ya matsa mun da muzo mu gaisa da ita ba. Babu inda zani"

Samha ta suke nanauyar ajiyar zuciya sa'anan tace "Ammi ki kwantar da hankalinki, insha Allah komai zai tafi yanda akeso. Baza'a samu wata matsala ba".

Itama Samha jikinta ne ya karayin sanyi data tuno kalaman Jabbar a game da soyayyar dake tsakaninta da Sabah. Cike da sanyin jiki ta cigaba da kallon Ammi tana fadi can kasan zuciyarta "Ammi kiyi hakuri, ni kaina ban san ya akayi hakan ta faru ba na fada tarkon son dan' wanda zaki aura. Son Sabah ya rigada ya gama kama ruhina, yayi mun kamun kazan kuku, ban san taya zan cire sonshi a raina ba. Ki gafarce ni Ammi don ina fargaban abunda zai faru nan gaba".

Ammi ce ta katse mata tunanin da takeyi ta mike tana fadin "Baby, kin gama shiri? Driver din gidansu na kan hanya shi zai zo ya dauke mu".

Samha tace mata a shirye take, bafi minti goma ba sai ga kiran Alhaji muazzam nan ya shigo wayarta, ta daga yace mata gasu nan sun iso. Haka suka fito tare samha na biye da ita a baya suka shiga mota.

Driver ne da Alhaji muazzam zaune a seat din gaba, Samha da Anty fanneh suna zaune a baya. Suna isa gidan, mai gadi ya bude musu gate suka shiga sukayi parking.

Alhaji Muazzam ya fito yazo ya budewa Anty fanneh kofar bayan ta fito. Murmushi ya sakar mata, itama ta dan sakar masa amma still cike take da fargaban haduwa da mahaifiyar nasa.

Shima ya lura da hakan, nan ya soma binta da baki yana janta da wasa yana kokarin kwantar mata da hankali har suka karasa ciki, Samha na biye dasu.

Sallama sukayi suka shiga cikin parlourn. Babu kowa a ciki suka karasa suka samu wuri suka zauna. Alhaji Muazzam yace musu Hajiya tana sama.

Yar aiki ta shigo ta kawo musu kayan motsa baki ta jera musu a gabansu sa'anan ta koma kitchen.

Alhaji Muazzam ne ya haura sama. Samha ta matso kusa da Anty fanneh ta kamo hannunta tana shafawa a hankali ta soma kokarin kwantar mata da hankali.

Can bayan minti biyar suka soma jin sautin saukowa daga saman matakala. Wata dattijiwar mata ce wace akala zata kai shekara saba'in zuwa sama ta sauko, Fara ce sosai matan kuma tana da kyau don daga gani tayi tashen kyau lokacin kuruciyar ta. Sanye take cikin wata tsadaden lifaya, ga fararen glasses manne bisa fuskarta. Hajiya Bilkisu kenan, mata ce wanda ake ji da ita sosai a garin eko,  yar boko ce sosai don har P.h.d ne da ita tazama proffesor har tazo tayi retire.

Karasowa tayi cikin parlourn tazo ta samu wuri ta zauna akan daya daga cikin kujerun.

Anty fanneh da Samha suka gaisheta cike da girmamawa "Sannu da zuwa hajiya, kin zo lafiya. Ya mutanen gida?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now