Chapter Twelve

578 69 0
                                    

Samha tana zaune a kasa sai faman rapsa kuka takeyi. Sabah ne ya karaso inda take durkushe ya tsaya yana dubanta sa'anan yace " yanzu kukan meye kike haka sai kace an miki mutuwa?"

Samha ta dago tana dubansa duk fuskarta ta bace da hawaye, bude bakinta tayi tana fadin " meyasa zaka mun haka Sabah? Meyasa ka fadawa amjad haka. Kasa yanzu yayi wa kalamanka wata fasara ta daban."

" wa? Wai dan na fada mishi nidake zamu zama dangerous siblings? Ai gaskiya na fada mishi. Gwanda ya sani tun wuri".

Mikewa samha tayi daga inda take zaune, hade da ta watsa mishi wani irin kallo sa'anan ta kama hanya ta tafi ta barshi tsaye zuciyarta na mata wani irin kuna. Gabadaya samha ji tayi abun duniya ya ishe ta a ranan. Tun a school take ta faman kiran layin Amjad yaki dagawa, Kiran duniya tayi mishi amma kememe yaki daga wayarta. Daga baya ma kashe wayan yayi gabadaya. Duk tabi ta sukurkuce ta rasa meke mata dadi.Ko data isa gida a ranar ma kin fitowa tayi taci abinci tace ma Anty fanneh bata jin yunwa.

A daren ranar dai ko runtsawa batayi ba. Washe gari ma data je school tasa ido ko zata ganshi amma ko alamunsa bata gani har aka gama lectures bata ji duriyansa ba. Suna gama lectures ta fara duba sauran lecture halls din department dinsu ko zata ganshi still babu alamun sa. A ranar dai babu inda bata je nemansa ba, har library inda ya saba zuwa karatu ta duba bata ganshi ba. Ko data hadu dasu khadie suma suka lura da yanayinta kamar babu lafiya suka sata a gaba suna tambayarta abunda ke damunta. Nan ta zayane musu duk abunda ya faru a jiyan. Shiru sukayi suna mamakin karfin hali irin na Sabah.

Bayan kwana uku da faruwan abun, samha tana zaune cikin aji, ko walwala babu a fuskarta, duk tabi tayi wani iri, kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Khadija da amina suna zaune a gefenta suna kokarin janta da hira, suna cikin maganarsu sai ga Amjad  ya shigo cikin ajin, sanye yake cikin yellow sweater da black jeans. Yau kwana nawa kenan samha bata daura idanunta a kansa ba, sai taga har wata yar rama yayi cikin yan kwanakin. Suna zaune suna kallonsa har ya karaso cikin ajin, Koh kallon inda samha take baiyi ba ya nema wuri a gaba ya zauna. Ciro littafi yayi daga cikin jakarsa ya fara rubutu, amma gabadaya tunaninsa a hargitse yake. Babu abunda ke masa yawo aka inbanda kallaman Sabah daya ce mishi shida samha zasu zama dangerous siblings. Wanan kalamun ba karamun tadda mishi da hankali yake ba idan ya tuno su.

Wani irin zafin kishi ne ya tunduke shi daya tuno da yanayin daya riskesu a ranar. Biro din daya rike a hanu yana rubutu dashi bai San sanda ya danata da karfi ba ta karye a hanunsa. Bayan an gama lectures, samha tanaso taje ta tunkareshi amma tana tsoron abunda zai biyo baya idan tayi hakan don tasan amjad ba karamin fishi da ita yayi ba. Haka suka shafi kusan sati basu magana da juna. Samha sai dai ta tura mishi da text tana rokon shi daya yi hakuri ya yafe mata, amjad yana gama karanta text din sai ya goge daga cikin wayarsa koh replying dinta baya yi.

Yau ta kasance ranar litinin da safe, bayan an gama lectures, su samha suna saukowa daga steps, amina ta dubi samha tace "wai samha kin daina zuwa gym ne?"

" me zanje in musu a gym kuma bayan amjad ko ganina bai son yi" ta tambayeta.

" kin manta har yanzu ke team manager dinsu ce?".

" team manager koh baiwar sabah? Ai ya mayar dani Yar aikensa na musaman a gym dinan"

" yanzu ba wanan ba" khadie ta katse su.
" kamata yayi samha kisan yanda zaki shawo kan amjad ki bashi hakuri. Haba yau kwana nawa kenan? nasan idan kika sameshi kika mishi bayani zai fahimce ki."

Ajiyar zuciya samha tayi sa'anan tace " nasan yanzu amjad zai yita min kallon wace batada kamun kai. Da farko na rubuta mishi love letter yanzu kuma ya gani rungume a jikin wani.

"Ai dole yayi miki kallon wace batada kamun kai" khadie ta bata ansa.

Duban ta samha da amina sukayi cike da mamakin maganarta.
" haba khadie, ya zaki fadawa samha haka? Da wane kikeso taji?" Amina ta tambayeta.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now