Chapter Nine

670 70 0
                                    

Yau asabar ta kasance ranar da amjad da sabah zasuyi practice na basketball dinsu. Samha tayi tayi da amjad akan ya fasa zuwa buga basketball dasu sabah. Murmushi kawai yayi yace "c'mon baby, it's just a friendly match. Kawai fa practice zamuyi dasu. Babu komai a ciki".

Da kyar dai ya samu ya shawo kanta tace toh taji amma tare zasu je gym din. Yace babu matsala. Ta kirasu khady a waya tace su shirya su zo gym din makaranta. Akwai match da za'ayi, Amjad da su sabah zasu buga basketball.

"Sabah da amjad kuma?" Khadie ta tambayeta.

"Kedai kawai kuzo ke da amina, idan kunzo zan baku labarin komai".

Tace to sai sunzo ta katse wayar. Cikin dan kankanin lokaci ta gama shirita ta sauko kasa ta fadawa anty fanneh zataje school ta dawo. Anty fanneh tace mata toh sai ta dawo.
Amjad ne yazo ya dauketa a gida suka tafi makaranta tare. A hanya ma sai mishi korafi samha takeyi akan practice din da zasuyi, shi kam ya dinga bata baki har suka isa makaranta. A gaban gym yayi parking motarsa, ya fito ya kira sauran yan team dinshi suka ce mishi suna ciki, yace toh gashinan zuwa.
Su na shiga ciki suka tadda yan team nashi sanye da uniform dinsu na basketball. Amjad yaje suka gaisa shima ya shiga changing room ya saka nasa uniform din. Su khady ne suka shigo suka hango samha zaune kan kujerun dake saman benen gym din da akayi don zaman yan kallon wasan. Tare suka haura saman matakalla suka sameta.

Khadija ce ta fara tambayarta abunda ke faruwa. Nan samha ta zayane musu komai. Amina ce ta girgiza kai tana fadin "lallai sabah dinan sai a hankali, sai kace wani shaidan. Meye matsalar shi ne wai?"

Khadija ce tace " ku barni dashi kawai, ni ce maganinsa. kwana biyun nan na zuba mishi ido ne naga iya gudun ruwansa amma zan gyara masa zama ne". Ta karasa maganar tana hucci.

Dariya samha tayi tana fadin " ku kyaleshi kawai. Ni bazan biye mishi ba. Zai gaji ne ya bari".
Suna cikin maganarsu sai ga sabah da abokanansa sun shigo cikin gym din. Kowa yayi shiru aka zuba musu ido ana kallonsu. Yanayin shigarsu ma daban yake. Fuskarsu a daure tamau kamar basu taba dariya ba suka karaso cikin gym din, sabah na gaba su shinoh na biye dashi a baya. Amjad ne ya karaso fuskarsa dauke da murmushi yazo shima yan team dinshi na biye dashi a baya ya mika hanu suka gaisa dasu sabah.

Amina ta duba su samha tace " ya naga su sabah sun shigo sai kace wani yaki za'ayi, Kalla fa yana yin su."

Daman tunda su sabah suka shigo samha taji hankalinta ya tashi, tana tsoron abunda zai biyo baya sanadiyan buga wanan kwallon. Zufa ne ya soma karyo mata duk da AC da aka zube cikin gym din suna aiki.

Cikin yan mintuna coach din ya sanar dasu za fara wasa su shirya. Dayake gym din babban wuri ne har yawanci dalubai sun shishigo sun zazauna suna son su kalla wasan. Coach ya hura whistle alamun su fara bugawa. Nan da nan wasa ta barke kafun kace meye sabah ya kwace kwallon daga hanun amjad ya saita ta cikin raga ta shige. Nan da nan yan kallon daga department dinsu sabah suka sa ihu suna murna.
Amjad yayi curuss yabi sabah da kallon mamaki don shi a tunanin sa sabah bai iya bugawa ba shiyasa ma yazo ya sameshi daya koya masa.
Amma ya kawar da mamakinsa gefe shima ya zage jiki ya fara bugawa cikin zafin nama, su shinoh ma ba barsu a baya ba don kafun kace meye, ko minti goma ba ayi ba da fara bugawa har su sabah sunci score bakwai su amjad suna na biyu.
Hankalin samha ya tashe ta dubi amjad wanda yaketa faman zufa shida yan team dinshi suna kokarin su kwace ball din daga wajensu sabah amma hakan ya citura. Samha da khadija hankali a tashe tare da sauran daluban department dinsu suka dinga ihun kiran sunan amjad daya samu ya kwace ball din daga hanunsu sabah. Haka sukayita bashi karfin guiwa. Ba jima ba coach ya hura whistle alamun za'ayi first half kowa yaje ya huta kafun a zo a cigaba. Haka aka tsayar da wasan, suka bar fillin wasan. Amjad ya koma gefe ya bude bottle water daya ya fara sha, zufa nata karyo mishi ta ko ina a jikinsa, shima sabah komawa gefe yayi ya bude ruwa ya soma sha shima sai faman zufa yakeyi. Kwantaciyar sumar dake bisa kansa duk ta hargitse. Amjad ne ya dube shi yace " ya naga kai da team dinka kun dage sai faman buga basketball dinan kukeyi sai kace ba friendly match ba. Kuma ai nazata baka iya bugawa sosai ba, kamar yanda kamun bayani".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now