Chapter fourty-two

426 43 6
                                    

Saukan dutse a kasa da kuma karan da Samha ta sake ne yasa Sabah ya bude idanunsa.

Ganin Jabbar yayi a durkushe a kasa, ya rike kirjinsa sai faman nishi yakeyi da kyar.

Hankali a tashe Sabah ya durkusa ya rukoshi yana "Jabbar! Jabbar!!"

Amma ina Jabbar har ya soma fita cikin hayacinsa don numfashinsa sai sama sama yakeyi yana fita da kyar.

Samha itama hankalinta a tashe ta soma salati tana tambayar Sabah abunda ke damun Jabbar.

"Asthma dinsa ne ya tashi" Sabah ya fada mata duk yabi ya rikice, bai tsaya wata wata ba ya dauki Jabbar cikin sauri yayi dashi parking lot inda yayi parking din motansa yaja sai asibiti.

Suna isa asibitin nan da nan likitoci suka karbe shi aka kaishi emergency.

Sunyi kusan hour daya suna tsaye a waje suna jiran likita ya fito yayi musu bayani.

Samha ce ta dubi Sabah wanda duk yabi ya tadda hankalinsa, gabadaya ya gagara samun sukuni.

"Sabah ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abunda zai sameshi, zai samu sauki bi izinillah". Samha ta fada mishi.

Ajiyar zuciya ya sake yayi shuru bai ce komai ba.

Sake kiran sunanshi tayi tace "Sabah......"

juyowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka kada sukayi ja saboda tsabar tashin hankali, ga kwantaciyar sumar kansa da duk tabi ta hargitse. Hannu yasa yana shafo sumar a hankali yana kallon cikin kwayar idanunta ya soma fadin " Samha bazaki gane irin tashin hankalin danake ciki bane a yanzu, idan na rasa shi ban san yanda zanyi ba. A da ina tunanin Jabbar ya kwace soyayyar mahaifiyar mu zuwa gareshi don tun muna yara ta fifitashi akaina kuma tafi bashi kulawa saboda rashin lafiya dayake yawan fama dashi. Da wuya ayi sati ciwon nashi bai tashi ba, kullum tana kan hanyar asibiti. A lokacin ban fahimce hakan ba don haushinsa kawai nakeji ina tunanin shi tafiso, amma dana girma nayi wayo sai na gane cewa ba hakan bane. Ina son dan'uwana har can kasan raina dukda dai bana nuna masa hakan, a duk sanda na ganshi cike nake da nadamar abunda ya faru tsakanina dashi muna kanana. Na san yanzu haka cike yake da tsanata". Sabah ya fada yana kawar da kansa gefe.

Cike da tausayinsa Samha ta karaso tazo ta tsaya a gabansa tana kallon cikin kwayar idanunsa ta soma fadin " Sabah nasan duk waenan abubuwan da suka faru tsakaninka dashi duk yaranta ne ya janyo hakan, yanzu duk kun girma. Jabbar dan'uwanka ne na jini. Bazai taba tsanarka ba asalima nasan a yanzu haka yana cike da kwadayin son ganin dan'uwansa a kusa dashi. Sabah ina so kayi mun wani alkawari na cewa bazaka sake kyaran dan uwanka ba, ina so ka janyo shi jikinka, kar ka sake barin aji kanku. Kuma bi izinillah Allah zai daga kafadarsa, zai samu lafiya. Addu'a kawai zamu cigaba dayi masa".

Suna cikin wanan maganar likita ya fito daga dakin da aka kwantar da Jabbar. Cikin sauri Sabbah ya karasa yana tambayarsa lafiyan jikinsa.

Likita yace ya kwantar da hankalinsa sun samu sun shawo kan abun, yanzu haka ma idanunsa biyu. Godiya sukayi mishi a tare shida Samha likitan ya juya ya tafi.

Sabah ya tsaya yayi shiru yana tunanin shiga cikin dakin. Samha ta bude baki zata mishi magana kenan sai ga dr Sageer nan ya taho cikin sauri yana tambayansu abunda ya sami Jabbar don yaji labarin cewa an kwantar dashi a asibiti.

Sabah banza yayi dashi ko tanka mishi baiyi ba ya kawar da kansa gefe. Samha ce ta bashi ansa da yana cikin dakin.

Cikin sauri Dr sageer ya bude kofar dakin ya shiga, nan ya tadda Jabbar kwance a kan gado idanunsa biyu.

Karasowa yayi yana fadin "Jabbar ya jikin naka, garin ya ka bari ciwon naka ya tashi. Baka fita da inhaler dinka bane? ". Dr Sageer ya tambayeshi fuskarsa cike da damuwa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now