Chapter Twenty - Six

528 57 0
                                    

Karan karfen dataji ya sauka a kasa ne yasa Samha ta bude idanunta. Ganin abunda yake faruwa a gabanta ne yasa ta kara zaro idanu.

Sabah ta gani ya cakume kwalar Zack sai faman zabga mishi naushi yakeyi ta ko ina yana fadin "Bakada hankali ne Zack? Kasheta kakeso kayi ne ko me? Toh idan daman kana rike dani ne a zuciyarka to ka fito filli ka tunkareni ba wai ka biyo takanta ba". Sabah ya karasa maganar yana cigaba da kai mishi duka da naushi ta ko ina.

Zack dayaji duka, azaba iya azaba ya bude baki a wahale ya soma fadin " Aliyah ta taso tun muna yara tana dawainiya da sonka har zuwa yanzu amma kai ko ajikinka. Meyasa bazaka sota bane eh?"

"So kake na sota saboda inajin tausayinta ne ko meye?! Ana so dole ne wai?!" Sabah ya tambayeshi a tsawace.

"Kai kadai Aliyah takeso, ka tausayamata ka sota ko da kadan ne".

"Toh baza'a sota din ba. Kai har waye da zaka bude baki ka fadamun abunda ya kamata naso? Me ka sani game da so?". Sabah ya tambayeshi yana zaro mishi idanunsa da suka kankance saboda tsabar masifa da tashin hankali.

Cikin zafin nama da karfin hali zack ya mike ya tura Sabah ya kai mishi naushi a ciki yana fadin " kaima me ka sani a game da so?! Babu wanda ka taba so a rayuwar ka Sabah, don haka kaima babu abunda ka sani a game da so" zack ya fada yana kara kaiwa sabah naushi a ciki.

"Kai kuma a garin ku haka ake nunawa mutum so? Bakada hankali". Wani irin wawan naushi Sabah ya kai mishi a fuska, har sai da yaji wani irin duhu ya rufeshi ya fadi a kasa, Sabah bai tsaya nan ba haka yabi takanshi ya dinga zuba mishi ruwan naushi ta ko ina. Zack sai mutsu mutsun azaba yakeyi ya kasa kwatan kansa.
Samha dake tsaye cikin ruwan tana kallon abunda ke faruwa a gabanta, hankalinta a tashe ta soma fadin " Dan Allah ya isa hakan ku bar wanan fadan da kukeyi".

Sabah ko ta kanta bai bi ba haka ya dinga dukan Zack. Juyowa yayi ya hango karfen da Zack ya riko yashe a kasa. Idanunsa ne suke rufe, zuciya ya dibeshi ya mike daga kan Zack yaje inda karfen yake yashe a kasa ya dauko ya sake nufo inda zack yake kwance a kasa, yana zuwa yayi saitin kanshi zai buga mishi karfen.

Samha na ganin abunda ke shirin faruwa wani irin bugawa kirjinta yayi bata san sanda ta karaso a guje ba tazo ta juya baya ta rufu akan Zack tana kokarin kareshi.

Sabah har ya dago da karfen zai bugawa Zack, sai ganin Samha yayi a gabansa tana kokarin kare Zack, cak ya tsaya ya dakatar da abunda yake shirin yi. Ruwa na zubowa ta ko ina a jikinsa ya tsaya yana kallonta.

A hankali Samha ta dago tana dubansa, kanta ta girgiza mishi alamun kar yayi haka, ta soma fadin " Sabah karka yi haka,don idan ka aikata hakan bazai taba haifar da da' mai ido ba, nasan ka sarai bazaka taba yafewa kanka ba idan hakan ya faru. Kaji please Sabah".

Sabah shiru yayi yana processing kalamanta, daga bisani ya jefar da karfen a kasa. Hanu yasa ya dagota daga inda take tsugune ya juyo da ita yana fuskantar Zack ya soma fadin "Zack wallahi wallahi kaji nayi maka rantsuwar musulmi ko, idan na sake ganin ka tunkare Samha da niyan taba koda gashin jikinta ne, toh sai nayi maka mumunar ila, don haka daga yau sai yau, ka fita daga harkanta, don idan kayi wani abu da har ya taba lafiyanta bazan taba yafe maka ba".

Yana gama fadin haka ya juya ya soma tafiya hanunsa rike da Samha wace taketa faman waigowa cike da damuwa tana duban Zack dake kwanace a kasa ruwa nata faman dukansa.

Bayan sunyi nisa wani irin razananen kara Zack ya sake yana zubda hawayen nadama . Aliyah ce ta karaso ta tadda shi a kwancen itama hawaye ne ke zubowa bisa kuncinta ta tsaya tana kallonshi.

Sabah da Samha har sunyi nisa suna tafiya still Sabah yana rike da ita, Samha ta kira sunanshi a hankali tana dubansa "Sabah?......"

Sabah shiru yayi bai ce komai ba daga bisani ya soma fadin "Dazun saura kadan na ji miki ciwo, ban san ya akayi hakan ta faru ba".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now