Chapter Thirty- Eight

419 48 5
                                    

Da dare misalin karfe bakwai da rabi, Anty Fanneh tana kitchen tare da lami ana dafa abincin dare.

Samha tana parlour tana shirya dining. Tana cikin aikinta taji an soma ringing din door bell din parlourn.

Ta karasa taje zata bude don a tunaninta mai gadi ne. Tana budewa taga mutum ya shigo ciki kai tsaye yana fadin " akwai abinci kuwa, yunwa nakeji". Ya fada yana karasawa cikin parlourn ya nema wuri ya zauna.  Samha ta bishi da kallo.

Anty fanneh ne ta shigo cikin parlourn taga Sabah. Fuskarta ta barke da murmushi tana fadin " ha'an Sabah yau kaine a gidan namu?".

"Eh wlh anty, ina wuni."

"Lafiya lau, ya gida. Ya mahaifin naka dasu Hajiya".

"Lafiyan su lau". Ya fada mata.

Anty fanneh tace " Abinci ma yayi bari a zubo maka, Samha kawo mishi ruwa ya fara sha tukuna".

Samha ta ce "toh Ammi".

Samha ta karasa wajen fridge taje ta dauko mishi ruwa da class cup ta kawo mishi.

Tsayawa tayi tana kallonshi. Wani irin tausayinsa ne taji ya kamata ta soma fadin
"Sabah ya kake ji yanzu".

Sabah ya dago yana dubanta sa'anan yace "Ban gane ba. Wani abun ne ya faru?"

"Maganar project dinku mana da akayi crashing".

Anty fanneh ce ta karaso parlourn hannunta rike da plate din abinci tana fadin " yawa ya ake ciki da maganar case din, mahaifinka ya kirani dazun yake fada mun abunda ya faru".

Sabah ya dan nesa sa'anan yace "wani ne kawai yake kokarin yayi framing dina. Amma Abba yasa anayin bincike akan lamarin".

"Toh ta Allah ba tasu ba insha Allah duk wanda yake kokarin ya bata ka asirinsa zai tonu".Ta fada tana kokarin mikewa tace tana zuwa. Nan ta sake komawa kitchen din.

Sabah ya juyo yana duban Samha da murmushi manne bisa kyakyawar fuskarsa sa'anan yace " kanwata ban San cewa kinada farin jini haka ba".

Gaban Samha ne ya fadi ta juyo tana dubansa sa'anan tace "ban gane ba, wani irin farin jini kuma?"

"Ah toh naji wai wani kyakywan guy yana bibiyenki a makaranta".

Samha ta soma girgiza masa kanta, ta bata rai kamar zatayi kuka tace " wlh ba haka ne, karka wani sa kanka cikin damuwa, bana son..."

"Toh ai ban damu ba, ko na fada miki na damu ne?" Sabah ya katse ta.

Samha maganar da take kokarin yi ne ya mutu a bakinta jin abunda ya fadi. Jikinta yayi mugun sanyi.

Sabah ya lura da yanayinta ya dan saki murmushi sa'anan yace " Ai babu wanda zai taba sonki fiyye ga yanda nake sonki kanwata. You're mine". Ya karasa maganar yana kallon Cikin kwayar idanunta.

Wani irin farin ciki ne ya lulube Samha da jin kalamansa bata san sanda ta sake murmushi tana sunkuyar da kanta kasa ba. A haka suka cigaba da hiransu cike da farin ciki da walwala.

**********************

Washe gari a school, Sabah ya kirawo su Zack suna tsaye suna kallonshi ya bude project dinshi a cikin laptop, ya kurawa design din ido ya soma fadin "da ku yarda, da karku yarda, duk uwasu daya ubansu daya, amma wanan shine first time dina na aikata hakan". Yana gama fadin haka nan da nan ya danawa project dinsa permanent delete.

Cike da mamaki da tashin hankali suka bishi da kallo, Zack ne ya dubeshi yace "Sabah lafiyan ka kuwa, akan me zakayi deleting na wurin naka? Shi kadai ne fa ya rage a group dinmu da za'a ayi submitting.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now