Chapter sixty - one

419 47 0
                                    

Babu shiri Sabah yayi parking motarsa a gefen hanya zuciyarsa na masa wani irin tafarfasa.

Madinah ce ta juyo tana dubansa cike da mamaki don yanda ya taka birki yayi parkin a gigice ba karamin tsoratata yayi ba.

Gani tayi ya hada rai murtuk, ya kurawa wani direction ido, ko kyaftawa bayayi.

Kallon inda ya kurawa ido tayi taga Samha tsaye tare da Sameer.

Sameer wanda yazo ya tsaya a gaban Samha, zuciyarsa na bugawa da karfi ya soma fadin "Samha....."

Samha itama kallonsa takeyi da manyan idanunta tace "na'am".

"Samha akwai abunda ya jima yana damuna a cikin zuciya, na jima ina dawainiya da wanan abun kuma i think lokaci yayi daya kamata na bayanata ko zuciyata zata samu sukuni".

Shiru yayi yana kallonta daga bisani ya cigaba da fadin "Samha na jima ina nadamar abu guda daya, ina nadamar rashin kasancewa tare daku alokacin da Allah ya dauki ran mahaifinki. Kamata yayi ace ina tare dake, ina share miki hawayenki, na yaye miki duk wani kadaici da zaki tsinci kanki ciki a sanadiyar rashin mahaifinki. Samha tun lokacin dana tafi banida wani tunani sai naki, a koda yaushe kina nan cikin raina."
Ya karasa maganar yana kokarin kamo hanunta ya rike.

Haba Sabah yana ganin Sameer ya kamo hannun Samha ya rike, jininsa ne ya kusan hawa, nan take jikinsa ya hau tsuma ya soma rawa, Bai san sanda ya bude murfin motar ba da karfi, ya fitto yana hucci kamar wani mayunwacin zaki. Madina na ganin ya fita itama cikin sauri tabi bayansa ta fito daga cikin motar hankalinta a tashe.

Inda Samha da Sameer suke tsaye Sabah ya soma nufa gadan gadan. Kan titin ya hau ko dubawa baiyi ba ballanta yaga motar dake tahowa tana sharara gudu akan titi.

Ai kuwa Madina na ganin motar ta sake wani irin razananen kara tana kwalawa Sabah kira daya kauce a hanya.

Amma inaaa, it's too late.

Karar da Samha taji ne yasa ta juyo a firgice taga Sabah yana tahowa ga kuma mota ta taho zata bugeshi. A razane ta kwada mishi kira "Sabah!!!..."

Sabah juyowa yayi yaga motar data nufoshi gadan gadan, nan take ya zaro ido yayi freeze ya tsaya kirjinsa na bugawa da karfi don already ya rigada ya sadakar.

Madina ce ta biyo bayanshi a guje ta hankadeshi daga kan hanyar, driver din daya taho a guje, kokarin tsayar da motar yake, yaja wani irin dogon birki, cikin ikon Allah motar ta tsaya dab da Madinah dake kwance yashe a kasa saura kiris motar ta hau kanta.

A rikice Sabah ya karaso inda Madina take kwance a kasa yana fadin "Subhanallah Madinah? Meya sameki? Are you alright".

Samha da Sameer suma suka karaso a guje, suma hankalinsu a matukar tashe, ganin jinin dake kwarara daga kafar Madinah ne yasa Sabah bai tsaya wata wata ba ya dauketa cak ya karasa yaje ya sakata cikin mota sai asibiti.

Samha da Sameer suma suna binsu a baya. Tare suka isa asibitin nan Sabah ya fito da ita suka shiga ciki ya soma kiran attention nurses din.

Nan da nan aka karbi Madinah aka shiga da ita ciki.

Tunda aka shiga da Madinah, Sabah yaketa faman zarya yana kaiwa da kawowa hankalinsa a matukara tashe. Tunani kala kala ne yake masa yawo aka yana addu'a Allah yasa ba wani serious ciwo taji ba.

Bayan kusan minti talatin suna tsaye a hakan Samha tace bari ta shiga ta dubasu.

Bayan shigan Samha ciki, Sameer yazo ya tsaya dab da Sabah yana fadin "ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abunda ya sameta, mu cigaba da mata addu'a kawai".

Wani irin kallo Sabah ya watsa mishi yana hararansa sa'anan ya kauda kansa gefe bai ce komai ba.

Ganin haka ne yasa Sameer yaja bakinsa yayi shiru ya koma gefe ya cigaba da tsayuwa. Suna cikin haka, can sai ga Samha ta fito hanunta rike da Madinah wace take tafiya tana dingishi, ga katuwar plaster an manna mata a kafan.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now