Chapter Twenty - Three

551 56 1
                                    

"Me kazo yi a gidan nan?" Ta tambayeshi ko kalonshi batayi ba, don har yanzu tana cike da jin haushinsa.

"Abba baya nan yayi tafiya. Nazo cin abincin dare".

" kazo cin abincin dare? Wai tsaya ma tukuna, ya akayi ka shigo cikin gidan nan kai tsaye?" Ta tambayeshi.

"Mai gadi ya bude mun gate, kuma nazo naga kofar parlour a bude shiyasa na shigo kai tsayen".

"Kuma hanunka na maka ciwo baka iya kwankwasa kofa azo a bude maka ba" Ta karasa maganar tana harararsa.

Shima hararar ya watsa mata ya juya zai bar kitchen din, tazo tasha gabansa tana fadin " ina kuma zaka? Ai Ammi bata gida, bata dawo daga aiki ba. kuma babu abincin da aka dafa a gidan nan, shiyasa na daura indomie. Idan zaka iya jiran indomie toh sai ka jira. Yanzu zata nuna".

"Oho dai, koma meye kika dafa zan ci, nidai na gaya miki kar ki cika mata ruwa, don bazan iya cin jagwalgwalo ba. Zan shiga parlor na kalla Tv. Idan ya nuna sai ki sanar dani." Yana gama fadin haka ya gyada kai yayi hanyar fita daga kitchen din.

Samha takaici ne ya ishe ta, tabi bayansa da ihun tana fadin " wai bazaka daina yi kamar nan ne gidan ku ba".

Bai juyo ya kalle ta ba ya bata ansa da "ki dai ji da abunda kike dafawa, karki cika ni da surutu." Yana gama fadin haka ya fice daga kitchen din.

Wuri ya samu ya zauna akan daya daga cikin three seater's din kujerun parlourn, ya daura kafarsa daya kan daya yana kadawa a hankali, yana kallon programme din da ake nunawa a Tv.

Samha ce ta leko ta hango shi zaune yana kallon tv  hankalinsa kwance, kamar bashida wata matsala. Harara ta galla masa tana fadi can kasan ranta " Dubeshi yanda ya zauna yana kada kafafu kamar babu abunda ya faru dazu. Wato bai ma damu da halin danake ciki ba" tsaki taja ta cigaba da aikinta.

Bafi minti biyar ba, Samha ta gama dafa indomie ta juye a kwanu guda biyu, ta kwaso tazo ta jera akan dining.

Karasowa cikin parlourn tayi ta sanar dashi cewa abincin ya nuna, ta juya ta koma wurin dining ta nema wuri ta zauna.  Mikewa yayi shima ya zo ya nema wuri ya zauna. Har ya dauki cokali zai fara cin abincin, samha ta katse shi da " ka bari abincin ya dan huce mana, kaga akwai zafi".

Harara ya galla mata yana fadin " Meye haka kuma kina abu saikace ke kika ajiyeni. Kefa kanwata ce bafa uwata ba"
Yana karasa maganarsa ya dauki cokalin ya soma cin abincinsa.

Samha ajiyar zuciya ta sake ta dauko cokali itama ta soma cin abincin. Shiru ne ya ziyarcesu, kowane da abunda ya damesa. Shi kam sabah ko ajikinsa sai faman cin abincin dake gabansa yake.

Samha kallonshi tayi sa'anan ta bude baki ta soma tambayarsa " ya jikin Aliyan?"

Sabah ya juyo ya dubeta ya bata ansa da " Zata rayu tunda goshin tane ya dan fashe da bakinta sai kuma kafarta data dan goce, munje nurse ta dubata so karki damu bazata mutu ba".

"Amma sabah, Aliyah tana yawan cin duka sosai, Wanan ba shine karo na farko da hakan yake faruwa da ita ba ko?"

"Ah lallai zack ya iya zuba, wani sa'in ban san meyasa yakeda surutu haka ba".

Samha shiru tayi daga bisani tace " yace idan kaga Aliyah cikin matsala sai inda karfin ka ya kare don baka son kaganta cikin damuwa".

Sabah har ya kai abinci bakinsa sai kuma ya dakata dajin kalamanta. Shiru yayi yana nazari daga bisani ya soma fadin " A duk lokacin danaga Aliyah tana cikin damuwa koh makamanci haka, hankalina tashi yakeyi. A da lokacin muna kanana, Aliyah tamkar ni take, bata son mutane kwata kwata, kuma bata bari wani yazo kusa da ita, kuma abun sai yazo ya hade mata da rashin kunya, wanan rashin kunyar shine yake yawan janyo mata take samun matsala da mutane."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now