Chapter Seventy-Nine

658 54 4
                                    

Kallo cike da tsantsar mamaki da al'ajabi hade da tashin hankali Abba da Anty Fanneh suka shiga bin Samha dashi suna jiran suji ta karyata abunda Sabah ya fadi.
"Da gaske ne abunda kunnuwansu sukaji ya jiyo musu ko kuwa karya ne?"

Abba ne ya dubi Sabah yayi kokari ya hadiye abunda yaji ya tasar masa yace "Sabah.... what are you saying? Da gaske kai kayi cikin dake jikin kanwarka ko kuwa kunnuwa na ne suka jiyo mana ba daidai ba?"

A hankali Sabah ya da'go kansa ya zube fararen idanunsa kan mahaifin nasa yana jin yanda kirjinsa ke tsananta bugu, numfashi da kyar ya janyo sa'anan yayi releasing a hankali yace " eh Abba, cikin jikin Samha nawane kuma inason abuna"

Kalmar innalillahi wa innalillahi raji'un daga Anty Fanneh ne ya dakatar da sauran magana daga bakin Sabah.

"Samha kina jin abunda Sabah yake fadi? Wai cikin jikinki nashi ne kuma yana son abunsa? Innalillahi yau wace irin bakar rana ce gareni? Me zancewa duniya? Da wani ido duniya zata kalleni? Ya Allah karakasa wanan abun ya kasance gaskiya.." numfashin Anty Fanneh ne ya soma fita sama sama sai faman sumbatu takeyi.

Abbah kuwa yana tsaye ya kurawa Sabah ido yana kallonsa cike da matsanancin mamaki. Kwakwalwarsa ne ya shiga carji da tunanin yanda akayi suna zaune gida da'aya wanan abun ya faru? Ya akayi cikin? Garin ya? Su kuma suna ina? Tambayar da Abba ya shiga yiwa kansa kenan bai samu ansa ba.

Samha ce ta mike cikin sauri taje ta durkusa gwuiwowinta duka biyu a gaban Ammi tana fadin "Dan Allah Ammi kiyi hakuri ki gafarceni wlh bada...."

Wasu irin gigittatun maruka har guda biyu Anty Fanneh ta dauke Samha dasu tana fadin "Tashi ki bani wuri yar iskar yarinya maciyar amana kawai! Abunda zaki saka mun dashi kenan bayan duk wahalar dana sha dake?! Me zancewa dangin mahaifinki? Me duniya zasu fada akaina?"

"Abba dan Allah kayiwa Anty magana ta bar dukanata haka, ina matsanancin son Samha Abba, kuma na rigada na fada muku cikin nan nawa..."

Shima marin da Abba ya daukeshi dashi ne yasa ya tsayar da maganar da yake kokarin yi. "Dan ubanka kana sonta shiyasa kayi mata ciki? Kasa abunda ka aikatawa kuwa? Nasan Samha bazata taba aikata hakan ba in ba dole ba, tursasta mata kayi". Wanan shine karo na farko da Abbah ya ta'ba daga hannu ya taba lafiyar jikin da'an nasa don ya ciyo shi sosai.

Sabah cike da tashin hankali yake duban mahaifin nasa yace "Abba wlh ba tursasa mata nayi ba... Abbah Samha matata ce"

"Matar ka....?"

Abba bai iddasa maganar da zaiyi ba sukaga Anty Fanneh ta yanke jiki zata fadi, Abbah yayo kanto a gigice ya rukota ya soma jijigata. Nan take Samha da Sabah suma suka yo kanta suna kiran sunanta, samha na kuka kamar ranta zai fita ta kamo hannun Anty Fanneh cikin nata hawaye na bin kuncinta.

"Ammi...! Ammi..!! Dan girman Allah ki tashi Ammi na tuba karki mutu ki barni. Idan wani abun ya sameki bazan ta'ba yafewa kaina ba!" Sosai Samha take kuka tana jijigata.

Cikin sauri Sabah ya mike ya fice daga dakin, within 5minutes sai gashi nan ya dawo da likita da wata nurse suna biye dashi a baya. Likitan na ganin yanayin da Anty Fanneh take ciki ne yasa suka shiga bata taimakon gagawa, da kyar aka samu numfashinta ya dawo.

Gabadayansu a wajen sun gigice sun di'mauce, kallo da'ya zaka musu kasan suna cikin matsanancin tashin hankali, barin Samha da takeji gabadaya duniyarta ta tsaya cak.

Numfashi Anty Fanneh ta shiga saukewa tana ajiyar zuciya jikinta na wani irin kirma tare suka shiga jera mata sannu.
Anty Fanneh tana ha'da ido da Abba ta sake fashewa da matsanancin kuka numfashinta har kagewa yake, sai da Abba ya yiwa likitan magana aka zo aka bata alluran bacci tukuna kuka nata ya lafa. Har lokacin Samha bata daina kuka ba, Abbah ya juyo yana duban Sabah dake tsaye a gefe jiki a sanyaye.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now