Chapter Thirty

625 51 0
                                    

Washe gari da safe Alhaji Muazzam ya sauko kasa ya tarar da Sabah zaune a parlour yana kishingide a kan kujera yana buga game a wayarsa, Alhaji muazzam ya dubeshi yace " Baby boy, ka shirya yau zamu fita outing".

Sabah shiru yayi kamar bai ji shi ba "Sabah ko baka ji abunda nace bane? Cewa nayi ka shirya yau zamu fita tare dasu Samha da Aminta".

Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa'anan yace "Gaskiya Abbah nikam bazani ba, kuyi tafiyar ku kawai".

"Haba baby boy, na yau kadai ne fa".

"Wai Abbah idan zaku fita mun dinga binku kenan sai kace wasu yara kanana. Kai da ita ku fita mana abinku. Ai ba sai mun biku ba". Ya fada yana cigaba da buga game dinsa a waya.

Alhaji muazzam ya sauke ajiyar zuciya ya zo ya zauna kusa dashi ya soma rarashi yana bashi baki har ya samu ya lalabashi ya amince amma yace daga yau bazai kara binsu ko ina ba. Alhaji muazzam ya amince yace babu matsala. Shi kanshi Sabah ya fada ne kawai amma can kasan zuciyarsa yasan saboda Samha zataje ne shiyasa ya sauko ya amince zai bisu ba wani abu ba.

Bangaren gidansu Samha itama Anty fanneh ta sa Samha a gaba tace sai lallai ta bisu fitan da zasuyi, tace tunda dan'ta Sabah ma zai bisu bataga abunda zai hana itama Samha fita dasu ba.

Ba'a jima ba suka gama shiri, Alhaji muazzam ya fito ga bodyguards dinshi na biye dashi, Sabah yana ganinsu yaki kememe yace indai dasu za'aje ya fasa tafiyan. Alhaji muazzam yace toh shikenan, ya dakatar dasu yace ba sai sun bisu ba, shi zaiyi tukin ma da kansa. Watar katuwar bakar SUV ce mai shegen tsada da kyau Alhaji muazzam yaja suka bar gidan. Ko dasuka isa gidansu Samha, Samha da Amminta ne suka fito suka tadda su, Kuma sunyi kyau sosai.

Sabah yana ganin Samha wani irin bugu yaji kirjinsa ya soma yi kamar ko da yaushe a duk sanda ya daura idanunsa a kanta, don tayi mishi kyau sosai, amma ya danne ya kau da kansa gefe yayi kamar bai ganta ba, Samha ta bude kofar seat din baya ta shiga ta zauna. Itama Anty fanneh ta shiga gidan gaba. Sabah ne ya gaisheta sama samah, ta juyo cike da farin ciki ta ansa gaisuwan nasa. Haka suka dau hanya tamkar family guda abun sha'awa suka soma tafiya. Familyn yan' gayu kenan.

Suna cikin motan, Samha sai faman satan kallon Sabah takeyi da gefen idannunta, shi kam shiru yayi cikin zurfin tunani bazaka ma ce yana cikin motar ba.

Alhaji muazzam ya dubi Sabah daya hada fuska ta mudibin gaba ya soma fadin "yau wace rana zamu fita tare da Sabah. Sabah amusement park fa zamu, banga kana murna ba".

Sabah shiru yayi ko tanka mishi baiyi ba, Anty fanneh dariya kawai tayi, Alhaji muazzam ya juyo yana duban Samha sa'anan yace "kefa Samha? Da fatan Ammi bata takura miki na fitowa yau ba?".

Samha murmushin karfin hali kawai ta kirkiro don gabadaya a takure take a back seat dinan, ga Sabah daya mata banza tamkar wasu kurame haka suke zaune a bayan.

" Babu komai Abbah, ai nima na jima banje Amusement park ba. nasan it'll be fun idan muka je".

Alhaji muazzam yaji dadin abunda ta fadi yace " toh ai shikenn, yayi kyau daman ina tunanin ko zaki fita da kawayenki ko wani abu tunda yau public holiday ne babu lectures."

Anty fanneh ce tari saurin capkewa tana fadin " Ai Samha bata fita ko ina, ita fa daga makaranta sai gida. Gata kuma da kokarin aiki don bakaga aikin data taya ni dashi a gida jiya ba. Ai ita kam bata damu da fita ba, shiyasa ma na matsa mata nace sai lallai ta biyo mu".

Sabah dariya ya soma yi a gefe yana fadin "Allah sarki wata dai tana fama da rayuwar kadaici". Haka ya dinga waka yana mata dariya kasa kasa. Samha tayi kicin kicin da fuska tana turo baki.

A haka suka karasa randle avenue na cikin Apapa GRA suka shiga park din wanda yake dauke da dunbin jama'a kasancewar ranar public holiday kuma yawanci sun kawo yaransu da iyalensu don su shakata.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now