Chapter sixty - five

431 46 0
                                    

Madina zaune take a dakinta da zoben a gabanta ta kura masa ido, gabadaya ta gagara samun nutusuwa a cikin ranta sai faman tunani takeyi.

Wayarta ce ta soma ringing a kusa da ita, ta dauko tana dubawa. Bakuwar number ta gani ta daga kiran ta kara a kunne.

"Madina kina gida?"

"Eh ina gida, wake magana?"

"Shinoh ne. Ki fito gamu a kofar gida".

Mamaki ne ya cikata tana tunanin meye zai kawosu shinoh kofar gidansu.

Mikewa tayi ta dauko gyalenta ta sanya sa'anan ta fito.

A kofar gida ta tadda su suna tsaye, murmushi ta sakar musu suka soma gaisawa tace " ya naganku cikin daren nan, wani abun ne ya faru?".

Kame kame suka soma yi suna da'an sosa geya, wanan ya kalli wanan, wanan kuma ya kallo wancen duk sun kasa hada ido da ita.

Madina ta kallesu daya bayan daya cike da tuhuma tace "ku fada mun mana, wani abun ne ya faru?"

Zack ne ya fara magana cike da i'ina yana fadin "eh toh daman akan Ss..sabah ne".

Madina ta da'an saki ajiyar zuciya tace "indai wanan ne already na rigada nasan cewa yanada wace yakeso".

Shiru dukansu sukayi suna kallonta, Abba ne ya da'an buge zack da kafada yayi mai allamu daya cigaba da mata bayani mana.

Zufa ne ya soma karyo wa Zack don baima san ta inda zai fara ba, don yana bala'in jin tausayin Madinan.

Bai san sanda ya runtsa idanunsa ba ya furta "Madina inaso ki sani cewa Sabah bazai taba yin aure babu soyyaya ba".

Shiru Madina tayi tana kallonsa daga bisani tace "wace Sabah din yakeso.... nasanta?"

Shiru sukayi basu bata ansa ba.

Sai data sake maimaita kanta tukuna shinoh yace "kiyi hakuri, bazamu iya fada miki ba don bamu son muyi hurting dinki".

Abba yace "dukan mu nan muna sonki".

"Kuma koda kin cire Sabah a ranki, nine nan zan fara tambayarki ki zama budurwata". Shinoh ya karasa maganar yana sakar mata murmushi.

Dariya Madina ta soma yi, shima Zack yace "dabadin inada budurwa ba already, babu wanda ya isa yasha gabana wajen kwato soyayyarki".

Murmushi ta sakar musu sa'anan tace musu "ina zuwa."

Bude gate din gidansu tayi ta koma cikin gida bafi 3 minutes ba sai gata ta fito hanunta rike da chocolates ta soma mika musu daya bayan daya.

Godiya suka mata hade da sai da safe, shinoh ne ya dan taba ta yana nuna mata hasken wata hade da zahra sai faman walkiya sukeyi a sararin samaniya, sa'an ya juya suka tafi.

Madina tafi 5 mins tsaye a wajen tana kallon sama tana kokarin ta fahimce abunda Shinoh yake nufi daya nuna mata Zahra da wata.

Cike da sanyin jiki ta juya ta shige cikin gida ba tare da ta samu ansa ba.

****************

Washe gari da safe, Anty fanneh tana kitchen tana faman soye soye tare da sophie a kitchen.

Samha zaune take kan dining tayi shiru tayi zurfi cikin tunani.

Wayar Anty Fanneh ne ya soma ringing, Samha ta mike zata je ta dauko, daidai wurin matakalan taci karo da Sabah shima ya sauko kenan yayi shirin tafiya makaranta.

Kirjinta ne ya harba ta tsaya tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, idanunsu ne suka tsarku cikin juna cike da so da tausayin junansu.

Anty Fanneh ce ta karasa cikin sauri taje ta dauki wayar nata ta kara a kunne.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now