Chapter seventy-three

625 58 6
                                    

Abba shima ya karasa shigowa ya nemi wuri ya zauna aka soma gagaisawa. Anty Fanneh na zaune a gefen shi tayi wani irin haske tayi fresh saboda kulawan data dinga samu na musammam ga kuma shigan cikin dake jikinta.

Mami sai faman reretata take don ba karamin murna tayi ba lokacin da Abba ya sanar da ita Anty Fanneh na dauke da ciki. A fadanta zata samu jika na uku kenan daga wajen babban da'anta Mu'azzam.

"Ai indai mace Fanneh ta haifa toh kuyi kap kap da diyarku don Jabbar bazai kyaleta ta huta ba" Gabadayansu suka sa dariya don sun san halin Jabbar sarai.

Samha ce ta mike taje ta dauko jakan  Anty Fanneh ta tayata haurawa da kayanta sama, Anty fanneh tana kishingide akan kujeran zaman mutum uku tana kallon diyarta ko zata ga wani canji a tattare da ita, amma sai taga normal tana abubuwanta kamar yanda ta saba. Nan ne kuma hankalinta ya da'an kwanta.

Bafi 10 minutes ba sai ga Samha ta sauko, wanan karan bakar Abaya ce a jikinta sai mayafin data yafa, hannunta rike da jakar makarantar ta tace musu ita zata wuce, a tare sukace mata toh adawo lafiya. Already Sabah ya fita ya tayar da motarsa kirar benz CLA 250 (2018 Model) farar ce sol motar. Tun 2019 Abba ya siyar masa a matsayin gift na 24th birthday dinsa. Bai cika hawanta ba saboda shi ya gwamace duk inda zashi ya tafi da power bike dinsa.

Tana fita harabar gidan ta hangoshi zaune cikin mota, ya jingina bayansa akan seat idanunsa a lumshe tamkar mai bacci. A hankali ta karasa taje ta bude murfin seat din gaba ta zauna sa'anan ta rufe murfin motar. Wani irin kamshin dadi mai hade da signature perfume dinsa dana motan ne ya gauraye wurin, ga sanyin Ac da yake tashi a motar.

A hankali ya bude fararen sexy eyes dinsa masu dauke da yalwan gashin gira dana ido ya zubesu cikin nata, gira da'ya ya da'ga mata yana karewa kayan jikinta kallo sa'anan ya jinjina kai yace "very good, shiyasa nake kara sonki kanwata, akwai ki da ladabi da biyaya." Bai jira yaji ansar da zata bashi ba ya duba agogon hannunsa yaga har goma ta wuce yace "kinyi latti, bari muyi sauri muje na saukeki"

"Kaifa? Yau bakada lectures ne?" Ta tambayeshi.

"Exam dinmu ya kusan gabatowa na final year. Time table dinmu is already out so we're done with all lectures" ya bata ansa yana jan motar security yazo ya bude musu gate suka bar harabar gidan.

Yana driving hanunsa daya nakan steering dayan hanunsa kuma na tsarke cikin nata yayi entwining dinsu tare, zoben daya bata gata nan sai kyeli takeyi a tsakakanin fararen yatsunta.

A hakan suka karasa makarantar yaje yayi parking a gaban department dinsu. Ko ina shiru sai few students da suke roaming about sauran kuma suna cikin various departments dinsu suna receiving lectures.

Juyowa yayi yana dubanta yana karewa fuskarta kallo ya hango gashinta ta gaba yana lekowa ta inda gyalenta bai gama rufewa ba, hannu yasa ya mayar da gashin sa'anan ya gyara mata zaman gyalen. Duk wanan da yakeyi tana zaune ta tsura masa ido tana kallonsa.

Murmushi ya sakar mata yace "kinyi kyau kanwata" hade da tallafo fuskarta cikin hannayensa ya manna mata soft kiss akan lips dinta, a hankali ta lumshe idanunta tana jin wani irin dadi hade da matsanancin sonsa yana kara ratsa jikinta.

Hannunsa ya daura a saman laps dinta yana shafawa a hankali sa'anan ya rada mata a kunne "karfe nawa zaki gama lectures yau?"

"Sai 2:30pm". Ta fada muryanta hade da numfashinta na fita sama sama a dalilin yatsunsa dake yawo a sansan jinkinta.

"Okay i'll come pick you up by then. Ki kulan mun da kanki. I love you".

"I love you too and i'll miss you" ta fada mishi hade da fadawa jikinsa ta rungume tsam tana shakar daddaden kamshin turaren jikinsa. Wani irin so take yiwa Sabah wanda ita kanta bazata iya misaltawa ba. Duk gabobbin jikinta sun ansa cewa shine ruhinta, shine jigon rayuwarta kuma shine muradin ranta. Sunkai kusan 5 minutes suna rungume da juna daga bisani suka da'ago, idanunsu tsarke dana juna ya da'an sunkuya ya sumbaci goshinta yace "take care baby".

"Take care too" ta fada mishi sa'anan ta fito daga motar ta daga mai hannu ta shige cikin department din nasu.

Shi kuwa yaja motarsa ya tafi.

Bayan sun gama lectures, khadie da Amina suka fito tare da Samha suna kokarin karasawa cafetaria. Duk tsawon tafiyan da sukeyi suna hira, khadie tayi shiru bata ce dasu kala ba. Daman tunda suka shigo sukaga alamun kamar bata cikin walwala. Ba kamar da, da kullum zaka ganta always lively.

Amina ce ta soma tambayarta "ya khadie lafiya kuwa? Naga tunda muka shigo baki wani walwala ba yanda muka saba ganinki ba. Meke faruwa ne?"

Shiru Khadie tayi bata ce komai ba daga bisani ta sauke katuwar ajiyar zuciya tana fadin "wlh bazaku gane bane, ina cikin damuwa da tashin hankali".

"Na me kenan?" Suka tambayeta a hade fuskokinsu dauke da damuwa.

"Daddy ne zaiyi retire kwanan nan, kuma so yakeso mu koma kano da zama, ni harga Allah nafi son zaman mu anan banso na koma arewa wlh. Nafi sabawa komai nawa anan, musaman ku, ga Amjad kuma, taya zan soma fada masa zamu bar gari. I can't leave him, bazan iya rabuwa da Amjad ba". Ta karasa maganar cike da damuwa muryarta tamkar zatayi kuka.

Shiru sukayi suna jinjina lamarin daga bisani Amina tace "why not Daddy ya bari mu karasa final exams dinmu, besides zaki iya fadawa Amjad yaje ya gabatar da kanshi a gida kilan Daddy zai iya yin la'akari da wanan, ko ba komai ke dashi zaku cigaba da kasancewa tare duk inda kuke."

"Gaskiya kam khadie, Amina is right. Ki gwada fadawa daddy hakan kiji me zai ce". Samha ta fada.

Shiru khadie tayi tana nazari daga bisani tace "toh shikenan, i'll try".

Tare suka cigaba da tafiya kowa da abunda yake masa yawo aka. Khadie ta da'an dubi Samha tace "Samha nifa nayi noticing kamar you've changed kwana biyun nan. Ba yanda na saba ganinki ba".

Gaban Samha ya tsinke ya fadi amma tayi sauri ta tattaro wa kanta nutsuwa tace "me kika gani?"

"Kawai dai... there's this new glow and aura around you ne. I can't point it out".

Dariya kawai Samha tace "kai khadie... ba wani, ni danake gani ma duk na rame saboda stress. Kinsan kwana biyun nan bana samun hutu saboda kwanciyar Ammi asibiti".

"Haka ne, ya jikin nata yanzu? Amina ya kamata ko yau ne mu kuma zuwa mu duba jikin Ammi" khadie ta karasa maganar tana duban Amina.

Amina zatayi magana, Samha tayi saurin katseta da "an sallameta, yau da safe ita da Abba dasu Mami suka dawo gida".

"Hmm zanso naga wanan kani ko kanwa a wajenku keda Sabah. Nasan babyn zaiyi kyau sosai, saboda ba Ammi ba, ba VC ba".

Dariya sukayi a tare, banda Samha wanda idan ta tuno abunda ke kasa sai taji gabanta na wani irin mahaukacin faduwa. Ko kawayenta tasan bazata iya fada musu cewa gashi abunda yake tafe ba, yau an wayi gari ta zama mata a wajen Sabah, wanda a' da take masa kallon batada makiyi daya kaishi a duniya gashi kuma wai yau shine yayanta kuma miji gareta. Haka Allah yake abunsa.

Da yamma misalin Hudu da rabi, Sabah yazo yayi picking dinta a school, basu wuce gida ba, kai tsaye wani hadadden restaurant ya kaisu sukaje suka ci abinci. Bayan sun gama ci, sauran smoothie dake gaban Samha ta soma kurba a hankali, Sabah dake dane dane a wayarsa ya fake idonta ya soma mata hotuna har kusan kala goma bata sani ba. Guda daya ya zaba wanda take kallon gefe kuma tayi kyau sosai yayi amfani da a matsayin screensaver dinsa.

Dagowa tayi tana dubansa tace "me kakeyi?"

"Babu komai" ya bata ansa kai tsaye hade da ajiye wayar gefe ya tsura mata mayatattun idanunsa.

"Inaso ki tare dani a sabon gidana". Taji ya fadi from nowhere.

Cikin sauri ta da'go tana dubansa tamkar yayi magana da wani yaren amma ta kasa cewa komai.

"Kin da'go kina tsare ni da ido, kin dai ji abunda na fadi, you're my wife now so you have no option".

"Sabah wasa dai kakeyi ko?"

"I'm damn serious".

"Toh me kakeso mu cewa su Ammi?"

"Kafun nan duk yanda ake ciki zasu sani. We can't Keep hiding forever" ya fada mata in a cool and calm tone.

Manage please...i'm so tired 🥱
Goodnight.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now