Chapter-Eighty

691 57 1
                                    

Abu kamar wasa fa Mami taki fur tace sam bata yarda ba. Sabah ya mike a fusace yace zai dauki matarsa ya bar musu gidan gabadaya, sai da Abba ya daka mishi tsa'wa tukuna ya koma ya zauna. Aka shiga rarashi kowa sai bawa Mami hakuri akeyi. Da kyar dai aka samu ta da'an sauko tace zata amince amma bisa sharadi da'ya sai dai idan Sabah zai kara da Shafa, yar wurin Uncle Mubashir.

Sabah yana jin haka can kasan ransa yace "wlh babu wanda zai tilasta masa karo wata macen. Samha kadai ta isheshi"

"Haba Mami, ki duba kiga duka duka yaron nan guda nawa yake? Ina zai kai mata biyu fisabilillah?" Uncle Mubashir ya tambayi Mami cike da takaici.

"Wani kuruciya ne a tare dashi yanzu? Mutumin da har ya iya dirkawa mace ciki zaka dangantashi da yaro? Ai ya wuce tunaninka yanzu.Don haka tsab zai iya zama da mata biyu. Yarinyar nan dai Shafa ta jima tana mun magiya akan tana sonshi, kuma yar'uwarshi ce don haka yar'gida za'ayi."

"Mami, shafah ya'ta ce. Kuma ni gaskiya ban shirya mata aure ba yanzu. Karatu nake so tayi". Uncle Mubashir ya fa'da cike da takaicin mami.

Kowa dai ya lura batason had'in Sabah da Samha ne kawai. Tafi son ya auri zabinta. Abba zaiyi wata magana uncle ya dakatar dashi yace su barshi da ita, Sai da Uncle yayi da gaske tukuna ya samu ta da'an sauko Amma tace ko ba yanzu ba ko nan gaba Sabah ya shirya sai ya kara da shafah. Sabah zai musanta Abbah yace dashi yayi hakuri abi komai a hankali. Uncle yace zasu je gida da Mamin su sake tattaunawa har ya samu ya shawo kanta. Abbah yace toh, haka suka bar gidan Mami sai faman zuba ruwan bala'i take tana fadin ba'a dauketa da daraja ba.

Bayan tafiyan su Mami, Anty Fanneh ta mike ta haura sama, Abba na kokarin mata magana ko tankashi batayi ba ta shige dakinta cike da tsananin da'cin rai da bakin ciki. Itama Samha wasu zafaffen hawaye ne suka cigaba da zubo mata, ta mike jiki babu kwari ta nufa da'kinta. Sai bayan la'ssar tukuna Sabah yaje da'kin Samha don ganin ya take. A kwance ya sameta akan gado idanunta a lumshe, tunanin duniya duk ya isheta, da'ga jiya zuwa yau ta kara yin wani irin rama ta fita hayacinta.

Hankalinsa yayi matukar da'gawa ganin yanayin da take ciki tana faman zubda hawaye. Wani irin tausayinta ne ya kara ji yana fuzgarsa . A hankali ya soma takowa har yazo ya tsaya bakin gadon yana kare mata kallo da fararen idanunsa. Kallo da'ya tayi mishi ta kau da kanta tana tunanin yanda za'ayi ta fada mishi ya sauwake mata kawai, yabi umarnin Mami. "Toh cikin jikinki ya za'ayi dashi zuciyarta ta tambayeta? wani irin zafi Samha taji kirjinta na mata don tasan tabbas dabadin matsanancin son da take yiwa Sabah ba, babu abunda zai sa ta tafka irin wanan babban kuskure game da mahaifiyarta.

Tsugunawa yayi a gefenta yasa hannu da'ya ya juyo da fuskarta tana fuskantarsa, kura mata ido yayi yana cigaba da kallonta damuwarsa da'ya a yanzu shine wanan hawayen da take faman zubda. A hankali yakai hannunsa ya soma share mata hawayenta sa'anan ya kira sunanta muryansa kasa kasa "Samha..."

Wani irin yanayine taji ya ziyarceta dataji ya kira sunanta. Tana jinsa amma taki ansawa sai da'ya kira sunanta a karo na biyu ta dago manyan idanunta masu cike da ruwan hawaye ta zubesu akansa. "Yanzu meye damuwarki.. i thought this secret marriage shine damuwarki toh yanzu komai ya fito filli sun sani. Uncle yayi musu bayani komai ya daidaita. Yanzu meye kike asaran hawayenki haka?"

Wani irin takaici ne taji ya lulubeta tace " babu abunda ya daidaita Sabah.. duba halin dana jefa Ammina saboda son zuciyata. Ga Mami tace ita sam bata yarda da wanan auren ba, cikin jikina bana halal bane. Ya kakeso nayi da rayuwata Sabah.,Ina dana sanin aika...."

Cike da zafin rai Sabah ya katseta da " don't even say it... karki kuskura kice kinyi nadaman abunda ya faru, because ni I don't. I'll never regret meeting you in my life, tun lokacin dana fara dora idanuna akanki, naji a jikina cewa you're the one for me. Kece kika kawo mun haske cikin rayuwata, ban'taba tunanin zanso wata ya'mace kamar yanda nake sonki ba. Nasha gaya miki indai akanki ne a shirye nake dana ba'ta da kowa, and I don't mind who i hurt in the process. Abba da Anty basu da wata damuwa indai akan auren mu ne, just give them some time zasu sauko. Mami kuma borinta na da'an lokacine don daidai nake da ita, she can't dictate my life for me, ba ita zatayi mun zaman aure ba."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now