Concise

468 21 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Aliyu kuwa ba abinda yake sai ambaton sunan Allah da tasbhihi ga Allah yana fadin
"Alhamdulillah, Yah subahanallah! Subahanallah!! Allahu Akbar! Subhnallahu wabihamdihi subhnallahu azim, Astagafurillah, Lahaila wallakuwata illa billah........"
Sune kalaman da yake iya maimaitawa da alamun a gigice yake.

Maryam kuwa Cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa tare da riƙo damatsan hannunsa ta saki kuka mai cike da rauni sabida ta fara galabaita shi kuwa baiji bai gani bare ya sararamata,

"Kiyi hakuri ki yafen Maryam *Matata* , Maul ayn *Matar Haidar* ki yafen Allah yai miki albarka ya albarkaci rayuwar ki da zuri'ar mu, sam banyi dan son rai na ba, babu yadda zanyi ne, kiyi hakuri, ke jaruma ce *MATAR HAIDAR* ki daure kinji. I love u, i really love you Matata. Kece kadai sirri na kece kadai hasken idaniyya ta kece kadai jigo na, kece kadai garkuwa ta, uwar ya'ya na. Ina son ki da kaunar ki har ban san adadi ba. Allah ya yafe mana ya hadamu a aljanna. Amin......"

Haka ya dinga mata addu'a da sumbatu tin tana jurewa har taga abin ba na karau bane, dan haka Kuka ta kuma sawa tare da ruggumeshi gam-gam a jikinta, tana fadin
"Wash, wash, Wayyo ashh na gaji Yaa Haidar, baya nah uhmm uhmm."

Aliyu kuwa a kiɗime yayi mata wata irin fitinenneyar kuma gigitacciyar rumgume, a hankali ya raba jikin ta da nasa ya koma gefe sai kuma ya lumshe idonsa saboda, wani irin fitinenne zazzaɓi mai masifar zafi da suka ƙasusuwan jikin daya rufeshi a take a lokacin ɗaya gaba ɗaya jikinsa karkarwa ya fara.





*
Bangaren Ammi suka fara shiga suka gaisheta da godiya Yaya Fadima tai musu jagora bangaren Yaa Muhammad.

Suna shiga ya dinga baza ido dan ya gano Maryam a tsakiyar Aisha da Rukayya ya hango ta an rufe mata fuska da sauri ya karasa ya rumgume ta tsam a jikin sa yana fadin
"Alhamdulillah finally jama'a sun shaida abin boye, Maryam ta zama *Matar Haidar* farin cikina, hakika ko yau na mutu buri na ya cika mutane sun shaida ke din Matata ce."

Yan dakin suka hau Kabbara suna fadin
"Allahu Akbar Allah ya bada zaman lafiya ya bada zuri'a mai albarka."

Fuskar Maryam ya dago yaga hawaye hannu yasa ya goge mata yace
"Kice Alhamdulillah Maryam komai ya faru dake mai kyau ko akasin haka kice Alhamdulillah Allah zai kara miki sama da abinda kika sama."
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
Ta furta tana jin wani sanyi a zuciyar ta.

Haka aka dinga daukar su picture masuyi nayi masu vedio nayi anan suka jima dan sai uku sannan suka tafi kamar kar su rabu ya tafi yana daga mata hannu itama haka. Wanda yana tafiya taji zuciyarta, ta tsinke gaban ta na faduwa.




*
Maryam na ganin Ammin ta mike ta fada jikinta tana kuka. Ammi tace
"To menene na kukan?"
Mamah ta kamo ta tace
"Ki daina kuka zai tashi kinji!"

Ta kwantar da ita a jikin ta, ta kalli Aliyu tace
"Sannu!"
Kai ya gyada kawai yana kallon Maryam dake kuka. A haka sukai masa sannu dukka amman shi ido da hankalin sa na kan Maryam. A hankali ta dago tana kallon sa. Ya mika mata hannu kin tashi tayi sai da Mamah tace
"Tashi kije mana!"

Ta karasa ya matsa mata gefen gadon ta zauna ya daura kan sa akan cinyarta ya kamo hannun ta daya ya daura akan cikin sa. Wani numfashi ya sauki sai kuma ya fara salati dan yadda cikin ya murda masa. Nan Maryam ta fara tofi Alkasim kuwa da sauri ya mike ya fita a dakin dan kiran likita tare suka dawo da likita yazo yace su fita, har Maryam ta mike amman Aliyu ya kamo hannun ta Doctor yace
"Yi zaman ki."

"Yi min tofi *Matar Haidar* "
Ta dauki ruwa ta karai masa tofi ta bashi ya amsa ya sha sannan ya lumshe ido ya mike zaune ya rumgume ta a jikin sa. Fita doctor yayi ya barsu su kadai a dakin.

Shiru sukai sai numfashi da suke saukewa can yace
"Allah miki albarka *Matar Haidar* "
"Amin Yaa Haidar nagode."

" *Matar Haidar* ki yafe min zan tafi na barki zan tafi wajen Manzo na, fatan na ki amshi duk kalar jarabawar da zata zo miki da kalubalen rayuwa wata rana sai labari." Hannu ya saka ya shafa cikin ta yace........



*Antty*

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now