💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 31By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
HML MY SISTER HASSANA ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN
Har karfe hudu ba Alkasim ba wayar Yaya Fadima, wannan yasa hankalin Ammi ya dan tashi, amman kuma sai tai zaton ko Alkasim ya riga ya bar gidan Yaya Fadiman ya tafi wani wajen, ita kuma tana can tana aiki kila shiyasa bata kira akan zuwan Maryam din ba.
Tunanin mafita take akan Maryam, tin da tayi sallah isha'i ta kasa tashi a wajen, ji tayi zuciyar ta ta karye so take ta tashi ta kira Fadima amman sai taji ta kasa tashi ta rasa me take ji, sallamar Alkasim shi ya katse mata tunanin da take, ta amsa ya shigo ya zauna a gefen gadon nata yana fadin
"Daga dakin Maryam nake naga bata nan ina ta shiga?"Kallon sa tayi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tace
"Dazu bayan kun kawo ta Abbin ku yace bai yadda ta zauna masa a gida da cikin da bai san uban sa, lallai sai taje ta nemo masa mahaifin yaron sannan ta zo a yanke musu hukunci.""What? Abbi me yake so yace? Yana so yace Maryam mazinaciya ce?"
Kai ya hau girgizawa yana fadin
"Ko duniya zata taro akan cewa haka ni ba zan yadda ba, me Maryam ta sani?""Na shiga rudani da damuwa amman nace zan tura ta can Saudiyya wajen Ummun ku."
Kallon Ammi yayi yace
"To yanzu Abbi da yace ta bar gidan ina take so taje, meyasa idon Abbi ya rufe akan alamarin nan, ai dole abi komai a sannu bai ga halin da take ciki bane?"Tagumi Ammi ta sauke, ya mike yace
"Ina yanzu ta tafi?"
"Gidan Fadima tin dazu nace ta tafi."Da sauri ya juyo yace
"Tin yaushe?"
"Baku dade da kowa ta, yazo yai maganar lokacin ko azahar ba ai ba ta tafi.""Ammi har bayan la'asar ina gidan Fadima fa, kuma Maryam sam bata je ba."
Ido Ammi ta zaro tace
"Bangane bata je ba, daukon waya ta na kira dai naji ko taje daga baya."Wayar sa ya zaro ya fara neman layin Fadima tana dauka tace
"Tin dazu nake so na kira naji ya jikin Maryam ka same shi?"
Shiru yayi can yace
"Bata zo gidan ki ba?""Wa din?"
"Maryam."
Ya bata amsa. Kai ta girgiza tace
"Bata zo ba nan tace zata zo."Wayar ya kashe ya kalli Ammi cike da damuwa yace
"Ammi bataje gidan Fadima.""Anya Alkasim ko dai bata son ta fada ne dan Abbi yace kada taje masa gidan iyaye ko ya'ya tashi maza kaje ka gano min dan Allah."
Mikewa yayi ya dauki mukullin motar sa ya fita a gidan da sauri mota ya shiga ya nufi gidan Fadima.Ba kowa a falo sai Ilham dake kallon TV ya shiga ya zauna ta karaso tana fadin
"Uncle ina yini?"
"Lafiya lou daughter ina Momyn ki?""Yanzu Dady ya dawo ta shiga ciki."
"To Aunty Maryam tazo yau?""Uncle an sallamota a asibiti, zan bika na dubo ta."
Fadima ce ta fito turus tayi ganin Alkasim tace
"Yaya lafiya?""Ammi ce ta aiko ni."
"To me ya faru?"
"Akan Maryam ne tace nazo na gani ko kin boye ta ne?"Zama tayi cike da mamaki tace
"Bangane ba fa."
Fada mata komai yayi salati ta saki tace
"Na shiga uku to ina ta tafi wallahi Yaya Alkasim batazo ba ai sai bayan la'asar ka tafi kuma wallahi tin fitar ka ba wanda ya zo gidanan."Da sauri ya mike yace
"Bari naje gidan Yaya Ummulkhairi Allah yasa can ta tafi."
Ya fita can ma da yaje ba Maryam ba alamun ta, gidan Yaya Zainab ma, wannan yasa ya kira Aisha bayan sun gaisa yace
"Maryam tazo nan ne?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...