Page 66

356 20 8
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 66

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Washe gari Kamu da Yini, bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta zo tayi ma Maryam very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani lace mai tsadan gaske da Abba yayi mata an mata dauri da head din kayan, ko tsinke ba a taba ba a lefenta ba, gaba daya kayan da zata yi fitan biki Abba ne yayi mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Muhammad da Step mum dinsa Momyn Jawahir duk sun zo, da friends dinsu duk sun zo suma, da Ummi da Mami da Momy lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka, Mama ma ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya basu Mami mamaki sai dai basu ce komai ba. A haka aka cigaba da shagalin biki, Ummi na lura da Maryam throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa. Bayan anyi kamu angwaye suka zo sosai Muhammad yai kyau sai sheki yake da tashin kamshi, abokan sa sosai sukai masa kara, shi kansa ya gane Maryam bata cikin haiyacin ta a haka aka tashi taron yana kara lallashin ta.

*
Washe gari haka akai dinner mai kyau da tsari wacce ta hada manyan mutane yan boko.

10pm har an tashi dan Ummi tace bata son ai abun dare nan, suna dawowa Ummi ta ja Maryam dakin Aliyu wanda rabon Maryam dashi wajen sati daya, wanda ko wajen shagalin bikin ta bata ganshi ba.

Ummi ce ta zauna ta kamo hannun Maryam ta zaunar tace
"Maryam ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have any problem da baki son fada min ne?"
Maryam ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Ba komai Ummi...."

Sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara taruwa idonta, Ummi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace amarya ke yi da zulumin barin gida ne ke damun yar tata, ko kuma tana tsoron rayuwar da zata shiga a cikin wadan da bata sani bane, da haka sai ta jawota kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Maryam dai sai gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ummi ta rumgumeta tace
"Bana son wannan kukan Maryam, today is ur happy day, ki saki ranki please"

A hankali Maryam tace "Na daina"
Ummi tace "Good ki koma daki ki kwanta ki huta kinji."
Kai ta gyada sai kuma Ummi tace
"Zauna ina zuwa dan nasan ba kici komai ba."

Shiru tayi, Ummi ta fita. Aliyu ne ya shigo dakin cike da damuwa ya fada saman kujera yana mai lumshe idon sa sheshekar kukan da ya jiyo yasa ya mike da sauri yana kallon ta. Sanye take cikin kayan dinner ta wanda yake wani dakakken army green ne an daura mata head shima army green ba karamin kyau yayi mata ba da yake fara ce sai ya kara fito mata kyan ta, ga make up din da akai mata kamar a dauke ta a gudu, ko a wajen dinner haka Muhammad ya dinga yaba yadda tai kyau, yan uwan sa ma sosai suke fadin Muhammad yayi dacen mata.

Kamar tasan kallon ta yake ta dago wanda tana dagowa suka hada ido, da sauri ta mike ta karaso inda yake zaune a kasa kan carpet ta zauna tace
"Yaya me yake damun ka? Kaga yadda ka koma kuwa?"

Murmushin karfin hali yayi ya jinginar da kansa da kujera tare da lumshe idanun sa, tace
"Yaya."

Ta kasan idon sa ya kalle ta yace "Na'am."
"Yaya me yake damun ka?"

Kai ya hau girgizawa, cikin tausayawa hawayen dake idon ta suka zubo tace
"Kagan ka kuwa Yaya ka rame sosai kalli fa."

Murmushi yayi kawai tace
"Please Yaya ka fada min me yake damun ka i promise to help you throughout insha Allah."
Ido ya lumshe yace
"It's too late"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now