💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 62By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Aliyu tinda yai parking yake kallonsu, Muhammad yace
"Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa"
shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali yace
"Ko bakya so?"Tayi murmushi tana girgiza kai yace
"Bakya son yan gidanku su san ni kenan?"
D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni zan shiga ciki dan nasan su Ummi yazo dauka""Ohk"
gate ta nufa tana satan kallon Aliyu da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Muhammad kuma ya nufi inda yake, sauke glass Aliyu yayi ya bude motar ganin Muhammad, ya fito yana kallon direct cikin ido, Muhammad ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Aliyu ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Muhammad yace
"I am Muhammad Auwal"Aliyu ya gyada masa kai kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace
"Aliyu Suleiman."
Muhammad yace
"Masha Allah it's nice meeting you"Aliyu yace
"Same"
Muhammad yace
"Alright zan koma, zamu rako ango sai da safe"Aliyu yace
"Ohk."
Suka kara musabaha sannan ya juya ya tafi, cikin mota ya shiga ya zauna, su Ummi suka fito ya kalli Ummi yace
"Ummi Maryam fa?""Tana ciki sai abokan ango sunzo zasu kawo su."
Kallon Ummi yayi yace
"Why?""Ai ba sa bar ta ita kadai ba ko?"
"Ita da waye a ciki?""Ita da Basma ne."
"Ummi please suzo mu tafi kawai me zasuyi mata dare nayi kalli agogo fa tara saura, sai yaushe kuma zasu zo please Ummi.""Shikenan."
Ta juya ta shiga. Tana zuwa ta same su a zaune tace
"Yayan ku yace ku taso mu tafi."Mayafin Najwa ta bude tace
"Ummi dan Allah su bari su karaso."
Kai Ummi ta girgjza tace
"Me zasuyi miki, tinda sun gyara ko ina kuma ba abinda zasuyi miki kawai su taso nasan suma suna hanya dare yayi kiyi hakuri kinji."Kuka Najwa ta saka Ummi ta kalli su Maryam tace
"Ku tashi mu tafi"
Suka mike suka ce
"Sister sai gobe."Ko kula su batai ba tana kuka suka fita. Maryam na fita ta shige baya, Basma ta shiga gaba, sai da Ummi ta lallashi Najwa sannan suka fito suka tafi gida.
Bayan gama bikin Yaa Aliyu bai kuma damunta ba sam gaisuwa ke hada su, bayan biki da sati daya su Momy da Basma da Yaa Aliyu suka fara shirin tafiya.
Yau a gidan Sitti ta yini, dan tinda aka gama biki bataje ba da dare tana shirin tafiya sukaji sallamar Yaa Aliyu, ya shiga ya zauna suka gaisa da Sitti, Sitti tace
"Ai nazata zaka tafi baka zo mun gaisa ba.""Haba dai Sitti, in banzo ba ai ba zan tafi ba kenan."
Tai murmushi tace
"Uhmm nayi mamakin zuwan ka bayan nasan kai baka fiya son taro ba amman kana wata kasa ka dawo.""Akwai wani abu da nake so nayi ne Sitti kuma nayi kinga sai na koma."
"Sauran wata nawa ka dawo?""Nan da wata takwas."
"To ni dai fatana kana dawowa kai aure kaji."Yai murmushi yace
"Sitti kenan. Bari na tafi."
"To dan nayi maganar aure ko, Maryam tana ciki tafiya zatai sai ku tafi tare ko?"Ya mike ya fita, ta kira Maryam tace
"Kije ku tafi tare."
Tace
"Sitti sai da safe."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...