💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 65By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Dagowa tayi tana kallon sa, ya dage mata gira yace
"Yes common tell me."
Idonta ta saukar kasa tace
"Yaya bansan me yake damu na ba, kwanakin nan duk banajin dadi bana jin nishadi bana jin farin ciki, rayuwa kawai nake yi Yaya."Ta karasa maganar murya na rawa saboda yadda kuka ya taho mata kan ta ta hade da kujera tana sakin kukan ta, ya taso ya durkusa a gaban kujerar da take yace
"A yadda na san ki, kina da addini da karatun Alkur'ani shin kina kan yi har yanzu?"Dagowa tayi tana kallon sa dan yadda yai maganar cikin damuwa, duk da tasan Aliyu na son ta, ido ta lumshe hawayen dake cikin idon ta ya gangaro, a hankali yace
"Bana son damuwar ki, in har na ganki cikin damuwa ina daura alhakin damuwar akai nane, in da yadda zanyi naga na cire miki ko wacce irin damuwa yanzu taso muje kinji.""Ina zamu?"
Mikewa yayi yace dauko mayafin ki ya juya ya sauka, a hankali ta mike tana tafiya da kyar ta shiga ta dauki mayafin ta tayi rolling, ta saka flat takalmi ta fito, a hankali take tafiya har ta fito falon nasu yana tsaye rike da mukullin mota, Ummi ya kalla yace
"Ummi zamu fita?"
"A dawo lafiya."Maryam ta karasa ta zauna kusa da ita, Ummi tace
"Menene?"
Kai ta langwabe tace
"Jikin ne?"Kai ta girgiza, Ummi tace
"To tashi kije yana jiran ki."
Mikewa tayi ta daga mata hannu tace
"Sai mun dawo.""Allah ya kiyaye hanya."
"Amin."Ta fita, a wajen motar sa ta same sa tsaye ya bude mata gidan gaba ta shiga ya zagaya ya shiga cikin mota ya bar gidan, Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo, wani murmushi ta sakar masa shima ya mai da mata, dan tina wajen, wajen ya kawo ta kusanin lokacin haihuwar ta, lokacin taji dadin wajen ya debe mata kewar wajen, shima Maryam matar sa yake kawo wa wanda tin da ta mutu bai kuma zuwa ba sai da ya kawo Maryam wancan karan sai wannan karon.
Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo murmushi shimfide a fuskar ta tin a haka ta samu nutsuwa da ragin damuwar ta sosai da sosai.
Yana kallon ta yace
"Mu shiga park ki hau lilo?"
Kai ta gyada suka nufi wata hanya suka shiga, a bakin kofa ya tsaya ya biya suka shiga, liluka ne kala kala a wajen ta shige ta barshi tsaye yana kallon ta ita ce hau kan waccan ita ce ta sauka a ta hau kan wancan a haka suka kwashe sama da awa daya, wanda suna fitowa suka shiga wani waje lemo aka kawo musu da menu sukai selecting abinda suke so, aka kawo musu sai da suka gama sannan suka fita suka fara zagaye wajen sune shiga can fita can haka sukai sha yawo sai da suka gaji suka shiga wani wajen suka zauna lemo aka kara kawo musu da menu na abinda suke so basu zabi komai ba dan a koshe suke, lemon kawai suke sha, ya dago ya dan kalle ta yace
"Fada min me yake damun ki?"Fuska dauke da murmushi, ta kalle shi tace
"Ka kawar min da komai."
"Nagani amman before fa?""Yaya ban sani ba, na fada maka yanayin da nake tsintar kai na a ciki, Yaya wani lokacin ji nake kamar nai ta kuka, a jiya na shiga rudani na wani mafarki da nayi, ban gane komai ba naso na tina amman na kasa komai ya gudar min amman abun ya tsaya min a rai."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...