💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 81By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Ba karamin burge ta dakin yayi ba, suna shiga ya saki hannun ta ya shiga bandaki, gefen gado ta zauna yana fitowa ya nufi wardrobe din sa wasu kayan bacci ya fito dasu masu shege kyau akan gado ya ajiye. Dagata yayi yace
"Bari na shirya matata."Kafada ta make, ganin ta kasa sakewa ya mika mata rigar yace
"Shikenan ki shirya bari na baki waje minti biyu."Ya fada ya juya ya bar dakin. Rigar ta d'aga ta juya ta kara juyawa, da kyar dai ta saka, ta dauki mayafin ta ta rufe jikin ta.
Yana shigowa yai arba da ita, takure waje daya, dan murmushi ya saki tare da lumshe ido ya karasa ya rumgume ta, hawaye ne suka soma fita daga idon ta saboda tina irin wannan makamanciyyar ranar da ya shude wanda a lokacin baya ta kasance cikin zumudin tarbar Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, ranar farin cikin su, a ranar ya koma ga mahallacin sa, hakika duk abinda ya faru da ita jarabawa ce kuma ta sani sau'ki ne a rayuwar ta, da hakan bai faru ba da bata san yadda zatai rayuwa ba Yaa Haidar ba, amman da ta bar gida taje wani waje tai rayuwa ta samu sassauci daga abinda take ji na rashin Yaa Haidar tin da gashi a yau har zuciyar ta ta aminta da wani ta bashi gurbin soyayyar ta, sai dai ta sani ba zata taba mantawa da Yaa Haidar ba kuma ba zata taba daina masa addua ba, take taji zuciyar ta na kara rauni na tuna abubuwa masu yawa, sosai Yaa Haidar ya rude da ganin halin da take ciki, tambayar ta ya hau yi amman sam ta kasa magana sai hawaye dake zuba a idon ta, wata irin rumgume yai mata wacce take nuna tsananin so da kulawa ga abinda ake so, kansa dake wuyanta yana shakar wani kamshi da ya rasa wane iri ne ya gama cika masa ciki, sai furzar sa yake, ya dago yana kai bakin sa dai dai kunnen ta ido ya bude a hankali numfashin na sauka a cikin kunnen nata wanda ya fara haifar mata da wani irin yanayi, ido ta lumshe, kan ya fara magana cikin kunnen nata a hankali yana fadin
"Kin tuna Aliyu ne? Addu'a ya kamata kiyi masa ba kuka ba. Kinji?"Wani abu taji yana wayo a jikin ta, ido ta runtse hawaye na cigaba da zubowa, tabbas ta tuna Yaa Haidar amman kuma bai kamata a wannan lokacin ba a wannan yanayin da suke ciki, so take tai masa bayani amman ta kasa ta gaza motsa bakin ta ma bare ta fada masa wani abun, ganin yadda take kukan yasa ya kwantar da ita a saman gadon yace
"Am sorry i don't means to hurt you Baby, in barki ki ta begen Yaa Aliyun ko?"Mikewa tayi ta fada jikin sa tana wani kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta, a wacan karon taso taga wannan tsayin daren tare da Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, duk burin Yaa Haidar na irin wannan daren Allah bai nufa zai gani ba, dagota yayi yana kallon fuskar ta, kirjin sa ta kwantar da kansa ta zagaye shi da hannayen ta,
"Bansan me yake damun ki ba da kike kukan nan haka ko duk akan Haidar din ne?"Saukar hawaye mai dumi yaji a kirjinsa tace
"Yaa Haidar don Allah da gaske kana sona?"
"Ashe duk yadda nake fada miki na ina sonki baki taba yarda ba tunda har kike kokonto Maryam ban taba jin son wata mace bayan Mami da Ummi na ba sai a kanki, ban ta'ba soyayya mai zafi ba sai akan ki, ke kadai nake so Maryam ki yadda dani kece kadai buri na da farin ciki na. Yes naso Maryam amman ita sai bayan auren mu, sai da naga yadda take da hankali da kyautata min, amman ke fa? Ranar da na fara daura ido na akan ki Allah ya d'auran son ki da kaunar ki, ina son ki, ina kaunar ki, ina bukatar matata, ina bukatar soyayyar ta, baki ba zai iya furta miki adadin irin son da nake miki ba. But my reaction in this nyt can tell u how much i love you."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...