💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 29By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
HML LAYUZA KABIR ADAM ALLAH SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURIA MAI ALBARKA. AMIN
A asibiti Fadima da Yaa Alkasim ne zaune sunyi shiru suna tunanin kowa da abinda yake tunani. shigowar Ammi ne ya sa suka mike da sauri ta kalle su, ta kalli Maryam tace
"Ya jikin nata?""Da sauki!"
"Ki tashi Abdullah ya kai ki gida!"
Ta fada tana kallon Zainab."Ammi baya gari kuma na nemi alfarmar ya barni na kwana tare da Maryam."
"Shikenan kije gida ni zan kwana da ita.""A'ah Ammi ni zan kwana kije ki huta dan Allah!"
Zama tayi ta zuba ma Maryam ido tace
"Tin yaushe take baccin?""Bayan fitar ku jikin ya tashi shine akai mata allura."
"Shiru Ammi tayi. Yaa Abdullah ya karasa yana kallon kanwar tasa da ta rame sosai tausayi ta bashi dan haka sai ya juya ya fita kawai dan zuciyar sa ba karamin karyewa tayi ba. Sai goma suka tafi suka bar Fadima a wajen ta.Ammi na komawa gida ta nufi bangaren Abbi wanda dawowar sa kenan. Zama tayi tace
" Kaci abinci ne?"
Dagowa yai ya aika mata da wani kallo wanda ya bata mamaki.Kasa shiru tayi tace
"Na jima ina jiran ka dan ina so muyi maganar akan Ummi "
Ummi take kiran Maryam wani lokacin saboda sunan mahaifiyar sa ne."Ai yar kice duk abinda kika yanke ya dace!"
"Bangane ba Abbi!""Kome tayi da sanin ki!"
"Wai kaima ka yadda da tana da cikin?""Saboda me bazan yadda, naje asibiti yafi biyar ana min test ana fada min positive. Ke zan fara tambaya cikin waye a jikin ta, kada kice min na Haidar ne!"
"Innalillahi wainna illahir rajiun Yanzu ni kake zargi akan cikin jikin Ummi, zan sani na boye maka shin me ka dauken da Ummi ne? Naga kafi kowa sani na da Ummi kasan halin mu dan me kuma zaka daura mana laifi baka taba kawowa ko fyade akai mata ko wani abu ba.....""Kinga ko kina son ki kare ta, in fyade ne wata uku dayi bata fada ba a haka tasan tana da ciki aka daura mata aure da yaron nan, Allah yaso baya raye da wane hali zai shiga kinsan dai yadda yake son ta."
"Dan Allah ka daina fadar haka wa ka sani wanda ya taba zuwa zance gun Ummi. Haidar ne kadai mane min ta inma tuhuma za ai shi za a tuhuma.""Na fada miki kada ku daurawa yaro nan, yana can kwance cikin kabarinsa cikin salama, kada kisa a tashe shi ana tambayar sa dan Allah!"
"Amman Alhaji.......""Dan Allah Amina ki kyale ni, tashi kije yanzu bana son magana ki kyale ni da abinda nake ji. Wai yau ni a cikin gida na 'ya ta take dauke da cikin da bamu san uban sa ba. Allah nagode maka Allah ka yafen in wani laifi nayi ka jarabcen da wannan masifar!"
Ammi kallon sa ta tsaya yi yana gama fadin addu'a yai ciki. Hawaye ne ya zubo mata lallai suna cikin tashi hankali da gaske dai da cikin nan. Mikewa tayi ta koma bangaren ta, ta zauna kawai ta rasa abin yi har wajen sha biyu idon ta biyu daga baya ta tashi ta dauro alwala tazo ta tada sallah.Kwana tayi akan sallaya tana addu'a akan lamarin yau ko da cikin shege ne a jiki Maryam dole ta tausaya mata dan yarinyar tana jin jiki amman dan me Abbi ya yadda da Aliyu ya kasa yadda da 'yar cikin sa. Ita bata zargin Maryam da son zuciya amman to ta ina ta samu ciki dan me bata fada musu ba shin a ruwa ta sha ko me dole dai sai an tara ake samun ciki to ita a ina ta tara da kuma wa har ta samu ciki.........
*
Da safe da ciwon kai Ammi ta tashi na tsananin damuwa ko abinci su Baba Ramma ne sukayi. Yaa Alkasim ya amsa ya tafi asibiti. Akan sallaya ya samu Maryam dan sai wajen takwas ta tashi tin jiya da akai mata allura sallolin ta, ta rama ta zauna tana addu'a ga Allah da kuma Yaa Haidar wanda a ko da yaushe bata taba mantawa dashi a cikin addu'ar ta. Yaya Fadima ce ta gaishe da Yaa Alkasim sannan Maryam ta dago ta daga hannu ta gaishe shi. Ya amsa yana fadin
"Ya jikin?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...