Page 5

415 21 1
                                    


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 5

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Yai murmushi zai magana kenan yaji Mama tana kiran sa
"Farouk."

Da sauri ya juya, ya karasa tace
"Me kake anan?"
"Daman zan anjiye ta ne."

"Ban yadda ba."
Ta fada ta wuce su, ya karaso yana ya'ke yace
"Sis Mama tace zan kai ta unguwa, kuma ba hanya daya bane da na ajiye ki mun wuce."

"Ah haba ba komai Yaya nagode."
Ta nufi bakin gate yace
"To ai kya bari na samo Malam Bala driver ya kai ki ko?"

"Dan Allah Yaya kada ka damu yau so nake na fita ni kadai,  yanzu Ummi ma take magana akan koyar driving nace kace zaka koyan gwara ka koyan kaga da sai dai na dauki mota kawai na fice."
"Haka ne bari na baki kudin mota."

Kai ta girgiza tace
"A'ah Ummi ta bani."
Ya zaro kudi ya mika mata yace
"Na Ummi da ban na Yaya daban."

Amsa tayi tace
"To Yaya nagoge."
Ta juya sai ga Baba Anas nan Yaa Farouk yace
"Yauwah."

Ta juyo tace
"Ni dai na tafi."
Baba Anas ya fito yace
"Ba dai fita zakiyi ba Hajiya?"

"Baba 'yarka dai."
"To 'ya ina zuwa?"

"Unguwa."
"Bari na kawai Hajiya sai nazo na kai ki."

"A'ah da ka barshi."
Farouk ne ya kalle ta yace
"Wai kin taba fita ke daya ma tukkuna."

"Kaji ka Yaa Farouk da wata magana."
"To ai naga kullum driver ke fita dake."

"Shiyasa nake so in fara yau, kan na fara driving ko?"
"No tinda ya dawo ki hakura kawai."

"Ya zanyi da Yaa Farouk ka zama kamar me?"
Yai murmushi Baba Anas ya dawo ta shiga suka bar wajen. wani karamin super market ta gani tace
"Baba mu tsaya anan ma."

Ya karasa yai parking ta fito tana kallon wajen, kamar ance ya waigo ya hange ta ta fito a mota wannan yasa ya karaso shima yai parking motar sa,  ciki ta shiga ya fito yabi bayan ta, tana shiga tayi wajen turarurruka, wani turare da ta dade tana nema ta gani ta dauka tana mai jin dadi dan taji dadin sa lokacin da Yaa Aliyu ya siyo mata duk lokacin da sukaje shopping sai ta duba sai dai bata sake ganin sa ba sai yau, tama dauka ta tafi bangaren su pad, ta durkusa ta dauki Virony da Moppid mai talatin da uku uku, tana cikin duba jikin su dagowar da zatayi suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa don rass ta ganesa, da sauri ta juya tare da ajiye pads din hannunta, kin juyowa tayi har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, duk da ta juya masa baya tana jin kallon da yake mata, tafiya ta farayi kawai sai taji wannan muryar tasa mai dadi yai mata sallama
"Assalamu alaikum"

Wani iri taji ta amsa a hankali ido ta runtse jin kamshin turaren sa, wanda ya kashe mata jiki, ya zagayo gabanta, yace
"Ya kika?"
Ba tare da ta kallesa ba ta
"Ina yini?"
A kunyace. Yai murmushi yace
"Ya exam?"

Shiru tayi sai ya kara murmushi yace
"Oh baki gane ni ba?"
Dagowa tai ta dan kalle shi yace
"Ko da yake tin jiya nasan kin gane ni ma."

Ji tayi ya gundure ta to me zatai masa daga ya taimaka mata sai yana bibiyar ta ko dai aljanni ne.
"Ni ba aljani bane kawai dai Allah ya hada mu da farko, sai jiya na ganki yanzu ma zan shige na ganki nace bari nazo naji ya exam?"
"Alhamdulillah."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now