💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 46By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ya mike ya fita tabi bayan sa tare da rufe dakin ta da key. Bangaren Ummi suka nufa ba kowa a falo wannan yasa Inna ta nufi sama tana fadin
"Suna sama kenan. Ni benen nan sam bana son sa ciwon kafa kawai zai saka mutane mu da bamuyi rayuwa dashi ba yaya bare ku da baku da abin yi sai gini da bene kamar tsuntsaye."
"Ke inna kin fiya mita wallahi ina ruwan ki to ai ba bangaren ki akayiwa benen ba."Lokacin suka karaso bakin kofar ta tura kofar tare da sallama. Aliyu dake zaune ya mike ya nufi kofa, Inna na shigowa ya fice Farouk ya sama bakin kofa ya shige sa ya sauka, da kallo ya bisa. Inna tace
"Kana ina Umaru?"
Ya shigo dakin yana ya mutsa fuska, Inna ta zauna gefen Maryam, tan fadin
"Sannu ya jikin?"
Da hannu tai alama da sauki. Inna ta juyo ta kalli Farouk ya hade fuska yace
"Ya jikin?"Bai jira ta basa amsa ba ya juya ya fita. Inna tace
"Ja'iri yazo ya cikani da tambaya akan ta dan me ba zan ce yazo ya duba ta ba shi ko tausayin ta ma bai ji?"
Ummi tace
"Kinsan Farouk ai kyankyami gare sa.""Mene abun kyankyami a gun Maryam?"
"Amai yaji tanayi kinsan sa ai!""Oh ni yasu aman ma sai kyankyami menene a cikin sa. Allah ya kyauta to."
Inna ta kalli Maryam tace
"Kinga har tai bacci Allah sarki me taci?""Ba abinda taci!"
Mikewa Inna tayi tace
"Bari naje na samar mata abu kan ta tashi.""To Inna muna godiya!"
Ta fita, a falo ta samu Aliyu zai fita tace
"Wai me kake gani game da jikin yarinyar nan ni dai da zaka bi tatawa da an gwada na hausa.""Dan Allah Inna kiyi hakuri kar kice zaki ta bata abubuwa ki barta haka nima ina kula da ita kuma naga abun nan ciki ne in lokacin karshen wahalar yai ai zai wuce amman gamje gamjen nan duk bai da amfani sai yazo ya haifar mata da wata matsala kuma."
"Hmm ai shikenan amman da haka uwar ka har ta haife ka shin me ita ya same ta, a lokacin wallahi ba asibitin da muke zuwa duk yadda Suleimanu yaso na hana kuma ya hanu sai ni ke bata na gida kuma da ta tashi haifar ka duk gidan nan ba yaro kato mai lafiya kamar ka amman wai kai ke kushe maganin gargajiya anya kuwa Ali, wai kai bokan turai wannan sun sauya kane kawai."Bai tanka mata ba har ta gama ta fita ya koma ciki ya zauna a falo yana danna waya. Sitti ya gani akan allon wayar tana kira dan murmushi ya saki ya kai wayar kunnen sa yana fadin
"Matata!"
"Hmm Ali kenan ya gidan ya aiki?""Ina yini Sitti?"
Ya dai dai ta magana cikin girmamawa.
"Alhamdulillah ya gida da aiki?""Alhamdulillah!*
"ya mai jikin?"
"Da sauki Sitti but wallahi Sitti tana wahala sosai ba abinda take ci fa.""Ya kuke barin ta haka ina Hajiya Hauwa ita ba zata dan mata wani abu da zataji dadin ci ba."
"Haba Sitti, me Inna zata iya zata bata abinda zai cutar da ita ne tana girka komai ta bata bayan yarinyar tana bukatar abun gina jiki ne amman ita tana bata traditional thing wanda ba abinda zai kara mata."
"Ai nasan za a rina Ali. Nasan zaka aikata haka amman banda abin ka mu a da din aka ce maka cimar mu bata kara lpy a jiki ne? Ku kuke ganin bama hada abun da zai gina mana jiki amman wa ya kai mu cin abun da zai gina mana jiki. Kaga mu bama rabuwa da kayan lambu wanda kai kan ka ko a likitan can kasan yana daya daga abinda aka fi so muci sosai. Duk abinda zamuyi sai mun saka wake ko yar gyada a ciki banda nama da kifi to me kuma za a fada mana in har kana so yarinyar nan tana samun abinda zataci ka lallaba Inna tasan me zata bawa masu irin matsalar ta kaji ko?"
"Sitti....."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...