Page 39

287 18 2
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 39

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Abuja
Kallon Abba Ummi tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace
'Inna ina zaton yarinyar tayi losing memory dan bata iya tuna komai na rayuwar ta sai mutum biyu Ammin ta da Yaa Haidar da ta fada min. Wanda Yaa Haidar din shine mijin ta!"

"Allahu Akbar. Allah yasa ba irin halin Aliyu nan gidan ne dashi ba. Yanzu ya jikin yarinyar?"
"Inna likitoci sunyi mana bayani yarinyar tana bukatar kulawa sosai. Dan tana cikin hatsari wannan abun shi yafi damu na, na rasa ya zanyi ya zan ajiye ta. Dan garari kawai take a cikin garin Bauchi bata san garin da kowa dake cikin garin ba bata tina kowa da komai a rayuwar ta ta baya."

"Ikon Allah wannan wacce irin jarabawa ce ace ka rasa komai naka da mijin ka ga ciki ga bakasan inda kake ba."
Abba yace
"Shine Aisha ta nemi alfarma akan tana son ta karasa kula da yarinyar har lokacin da Allah zai sa ta tuno yan uwan ta."

"Hakan yana da kyau!"
"To shine yau Aliyu yayi mana booking flight muka taso har yarinyar."

Ido Inna ta zaro tace
"Kuka taho da ita ina?"
Kallon kallo akai da Abba da Ummi. Abba yace
"Nan gidan!"

"Yanzu Shehu baka ganin ba matsala ka dauko yarinyar da baka sani ba ka kawo cikin iyalin ka. Haka fa kukayi mana shekarun baya. Shin kuka sani ko aljanna ce ma. Ni da farko na ji tausayin ta kuma na yadda da labarin amman kuna cewa kun kawo ta kuma sai naji tsoro nake ganin anya da gaske ne kada fa ta cutar da mu."
"Inna ta kenan da mukai haka a shekarun baya yanzu wa yafi ki jin dadin sa. Naga ya dauke ki kamar yadda kike a wajen mu. Kuma Inna ina ce ke kan ki baki taba kawo laifin sa ba tinda muke sai a yanzu kuma haba Inna. Nasan Inna ta ba abunda take tsoro a duniyar nan daga mutun har aljanna. Allah kadai take tsoro. Kuma nasan Inna ta akwai tausayi imani da taimako nasan zata taimakawa ko wanene dan Allah shi zai biya ta in ma ya cutar da ita dan kansa. Nasan Inna zata taya mu rikon yarinyar nan tsakani da Allah ko Inna ta?"
Abba ya karasa yana lankwasar da kan sa da neman taimakon Inna.

"Daman ai ni bana tsoron kowa, kuma ina son taimako yanzu me zance sai dai nace Allah ya bamu ikon rike ta da amana, Allah yasa ta tina da gida ya sauke ta lafiya."
Baki Abba da Ummi suka hada suna murmushi suka ce
"Amin Inna."

"Ya jikin nata?"
"Da sauki sai dai ba abinda take iya ci."

"Allah sarki haka za ai jinya ba cin abinci bari maza na tashi na samar mata abu da zata dan ji dadin bakin ta."
"To Inna me za a kawo?"

"Ba abunda za a kawo dan jiya Aliyu yayi min cefane kayan da nake bukata."
"To Inna godiya muke."

Ta mike ta nufi kitchen tana fadin
"Bari na shiga kan a kira magariba."
"To Inna muma mun tafi sai anjima!"

Suka mike suka fita. Ummi tace
"Ni nasan daman Inna sai tace wani abu!"
"Amman kuma ai kinsan tana da saurin sauka ko?"

"Haka ne kasan ta ai wata rana ta nuna tana son abu wata ranan akasin kowa mai laifi ne in tai niyya."
"Haka ne amman ku da yaran ku zaku taimaka mana mu rabu lafiya."

"Kai ma kasan muna iya kokarin mu."
"Haka ne."

Abba ya nufi gate din da zai sada shi da masallacin gidan Ummi kuma bangaren dake kusa da nasu iri daya ta shiga. Da sallama ta shiga sashen amman ba a amsa ba ciki kawai ta shiga. Hajiya Barira na zaune tana kallo. Ummi tai murmushi ta kalle ta tace
"Sannu da gida Hajiya!"

"Yauwah!"
Ta amsa ba tare da ta kalli inda take ba. Kai ta dauke tayi sama itama bata bi ta kanta ba. Tana zaune a daki hannun ta rike da waya ta jiyo muryar Ummi na sallama. Da sauri ta dago tana fadin
"Ummin Aliyu ashe yau din dai kuna tafe!"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now