Page 15

463 19 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 15

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


Washe gari, tin asuba da ta tashi bata koma ba saboda bata sababa dan ba kyau ma.  Zaune take  akan sallaya tana azkhar, Ash kalar hijab ne a jikin ta wanda yai mata kyau ya fito da aihin kyan ta dan ba karamin kyau hijab yake mata ba. wayar ta dake kan madubi ce tayi kara, karasa azkhar tayi wanda kan ta dauko ta katse, wani kiran ne ya kara shigowa.

Hannu ta sa ta dauko ta duba sunan taga an saka *My* Ido ta lumshe ta danna received, ta kai kunnen ta tana fadin
"Assalamu alaikum!"

Aliyu dake zaune a kan three sitter sanye da wando three quarters sai riga marar nauyi a jikin sa. Gashin kan sa ya kara bakikirin sai sheki yake, jin sautin muryar ta yasa ya lumshe idon sa yana mai shafa sumar kan sa hadi da sakin murmushi, a hankali yace
"Wa'alaikum salam My princess! Da fatan kin tashi cikin koshin lafiya?"

"Alhandulillah Yaya na, kaifa ya ka tashi ya daren ka?"
Numfashi ya sauke yace
"Yadda yake kullum My love, kullum dake nake kwana dake nake tashi kullum in ta mafarkin ki, Baby ina kewar ki sosai da sosai fa."

"Nima haka Yaya nah!"
"A'ah fa Baby bai kai nawa ba, Baby ni dumin jikin ki ma kawai nake so na dan ji a nawa."

"Yaya nahhh!"
Taja sunan wanda yasa abinda yake ji ya kara daduwa duk jikin sa yai sanyi. Kasa magana yayi sai lasar leben sa na kasa tare da lumshe manyan idon sa.

"My Hayyattt!"
"Uhmm!"
Kawai ya iya fada. Murmushi tayi ta mike ta koma kan gado tace
"Ya dai?"

Murya ya shagwabe Kamar zai kuka yace
"Ba kece ba!"
"Me nayi My?"

"Uhmm uhmm Baby I need you."
Murmushi tayi tace
"Haba Miji nah kwana nawa ya rage yau friday kaga remain one week a daura na kasance da kai sai abinda kake so zan maka."

"Why not now Baby!"
"Please Yaya nah kayi hakuri seven days ne."

"Wallahi gani nake Kamar seven years ne."
Murmushi tayi, yace
"Oh dariya ma kike min ko?"

"No no kawai dai."
"Shikenan ba ruwa na dake!"

Ya fada a shagwabe sannan ya kashe wayar. Dariya tayi ta fara neman layin nasa, kin dauka yayi ta kuma kira sai da ta kira sau uku sannan ya dauka, tana jin ya dauka ta saki kukan wasa, ai nan da nan hankalin sa ya tashi, ya hau tambayar
"Menene Baby? Meya faru? Dan Allah ki daina kukan nan, fada min menene?"

Kukan ta kuma saki tana fadin
"Ba kai bane!"
"Ni kuna Baby me nayi?"

"Fushi kake yi dani!"
"Ni na isa, ba zan taba fushi da Matata ba, please stop crying kinji da wasa nake fa na kashe ne dan ki dan kwanta ki huta kinga safiyya tayi ko?"

Dariya tayi tace
"I love you My! Sai anjima!"
Ta fada ta kashe wayar daga shi har ita murmushi suke wanda su kadai suka san ma'anar sa.

Kwanciyya yayi yana karatun Alkur'ani ita kuma mikewa tayi ta nufi kitchen. Ammi ta gani da me taya ta aiki, har kasa ta durkusa tana gaishe da Ammi ta amsa tana fadin
"Har kin tashi ko baki koma ba?"

Kai ta gyada mata ta gaishe da Baba Ramma Mai aikin su ta amsa tana kara taya ta murnar kammala karatu ta amsa tana godiya.

Baba Ramma tace
"Kinga Maryam je ki kwanta nasan tinda kuka fara jarabawa ba wani baccin kirki kikai ba ai Ina jin kin ma daina shiga kitchen sai na gidan ki."

Kasa tayi da kanta, Baba Ramma tace
"Jeki abinki ki huta kinji!"

Kai ta gyada ta juya ta fita, gidan sai kamshi yake dan an share anyi mopping an saka turaren wuta sai kamshi. Ido ta lumshe ta nufi bangaren Abbi.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now