💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 43By
*MARYAM S INDABAWA*Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
*Wannan shafin naki ne, Zarah Muhmmad Sani Kibia (My Habibty) ina godiya, Allah ya bar kauna da zumunci Allah ya baki zuri'a masu albarka ya kara muku fahintar juna tsakanin ki da mijin ki Amin.*Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli kayan abincin da ba abinda ta taba, rufewa yayi ya koma ya dauki ledar maganin ya hada ruwan da zai saka mata ya hada allura da wacce ya zuba a ruwan ya saka mata. Tana bacci taji shigar allurar a hannun ta ya saka mata ruwa, bude ido hawaye na zubo mata dan zafin da taji yace
"Sannu!"
Ido ta lumshe tana ji yace
"Gyara na miki allura!"Idon ta ne yai raurau dan tasan faman da suke da Yaa Haidar a gida ma kenan in bata da lafiya.
"Bafa da zafi zan miki ba!"
Ya fada yana kallon ta.Kalaman Yaa Haidar kenan in zai mata allurar yace ba da zafi zai mata ba. Juyawa tayi ya dage hijab din ta doguwar ta bayyana ta ciki ya zura allura ya zira mata wata yar kara ta saki sai kuma ta fashe da kuka a zuciyar ta take kiran Ammi, Ammi nah! Yatsa ya saka yana mulmula wajen sannan ya mike a hankali ya koma wajen da yake zaune.
A hankali yasaka zuwan ruwan saboda yabi jikin ta sosai. Wannan yasa tin hudu har shida leda na biyu ko rabi bai yi ba. Wayar sa ya dauka ya kira Ummi. Ummi da ke hanyar komawa gida ta daga kira ta na fadin
"Ba dai kun dawo ba na nan ba?"Maryam ya kalla sannan yace
"Aah muna asibiti ruwa nake kara mata daga wannan ya kare zamu taho sai bayan magariba."
Ya fada yana kallon agogon hannun sa dan lokacin shida har ta gota.
"Ya dai jikin nata?""Ummi da sauki!"
"To Allah kara sauki. Allah dawo daku lafiya.""Amin!"
Ya kashe wayar ya shiga yai alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da akai isha'i. Nurse din da yasa ta kula da ita tana zaune ya shigo ta mike da sauri. Ya kalle ta yace
"Ta tashi ne?""A'ah!"
Ruwan ya kalla yaga saura kadan bai fi minti biyar ba zai kare. Zama yayi a kujera yana danna system din sa. Bayan minti hudu ya mike ya karaso wajen ya zare mata ruwan sannan ya koma ya cigaba da aikin sa.Karfe takwas ya rufe system din sannan ya saka a jaka ya mike ya nufi bakin gadon nata.
"Maryam!"
Ya fada zuciyar na bugawa. A hankali ta motsa tana bude idon ta. Kai yai saurin kaudawa yace
"Tashi mu tafi ko?"Kayan abincin gaba ta ta kalla ta zuro kafar ta kasa ta sauko ta zauna a gaban abincin tuwon da bata ci ba ta bude ta fara ci sai dai batai loma uku ba amai ya taso ta yunkura zata tashi ya rike ta yana fadin
"Ki daina tashi a gujen nan fa."Kan ta kwace jikin ta ta dinga kwara aman anan wajen. Sai da ta gama ya daga ta suka shiga ta dauraye bakin ta sannan ya kira nurse yace a gyara office din a bawa messenger sa key.
Maryam yasa daya daga cikin nurse din ta kamo messenger sa ya dauki jakar system din sa da magunguna ya bi bayan Aliyu. Mota ya shiga ya zauna messenger ya bude gidan baya ya saka masa kayan nurse din suka karaso da Maryam ta bude dayan side din ta saka ta rufe mata kofa tace
"Allah kara sauki!"
Kai ta gyada Aliyu ya amsa da
"Amin ya Hayyu ya Qayyum!"Sannan ya tada motar yana motsa bakin sa dake tasbihi a haka suka fuce daga asibitin yana driving cikin nutsuwa da sannu da sannu suka karasa gida. Yai horn mai gadi ya leko ya bude masa yana daga masa hannu da masa sannu da zuwa. Wajen da yake parking ya karasa yai parking sannan ya fito ya bude mata kofar mota ya kamo hannun ta, suka nufi sashen Ummi.
Yana karasawa bakin main falon Ummi ya jiyo muryar Inna na fadin
"To sai yaushe zasu dawo tin safe fa ta fita!"
"Inna nasan suna hanya!"Bata rufe baki yai sallama. Ummi ta amsa tana mikewa da sauri ta karaso ta kama Maryam ta karasa da ita kan kujera ta kwanta. Ummi ta kalle ta tace
"Sannu!"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...