Page 55

304 14 2
                                    


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 55

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Ta shiga kitchen ta wanke ta fito dauke da lemo mai sanyi ta zauna tana ci Inna na bata labari tana ji tana dariya hade da lumshe ido dan dadi nama bata farga ba taji sallamar mutum dankwallin ta dake ajiye akan kujera tai saurin dauka ta yafa a jikin ta, tin kan ya shigo kamshin sa ya danno kai.

Dakin ya shigo, sanye yake da dogon bakin wando da farar riga, mai dogon hannu, ba a inda idon sa y fada sai akan Maryam, kai ya dauke ya karaso gaban Inna ya ajiye mata ledar da ya shigo ya juya ya nufi kofa Maryam tace
"Sannu da zuwa."

"Yauwah."
Kawai ya fada ya sa kai za fita, Inna tace
"An gode Allah maka Albarka."
"Amin!"

Ya amsa tare da ficewa. Inna ta tabe baki tana fadin
"Duk jikoki na nafi son yaran nan amman shi matsala wani lokacin miskilanci da nukufarci ji dai yadda ya ke magana kamar bai so. Dubi dai yanzu fura ya kawon da nono kusan kwarya guda dan yasan ina so."

Ta fada tana leka ledar da ya ajiye mata. Murmushi Maryam tayi, Inna tace
"Wallahi shima yana so na,  da sam ba haka yake ba yaro mai fara'a da son mutane amman daga mutuwar matar sa duk ya koma haka, nayi nayi suyi masa aure sunki, da sun masa da kila ya koma yadda yake Allah dai ya bashi mai tausaya masa da son sa kamar matar sa. Ina fada miki yar yayar Babar sa ce acan turai suke inda Najwa take karatu in kinga yadda suke soyayya a da sai sun burge ki, wallahi ban taba ganin Aliyu da ita sunyi fada ba tana da sanyi hali da hakuri yarinyar kirki mai tarbiyya da son mutane ga kyauta to Allah ya fimu son ta shekarar su biyu bata haihu ba sai da ta samu ciki kuma ya hau bata wahala, haka aka sha fama ke dauke matar sa yai ya kai can uwa duniya sai da cikin ya isa haihuwa da kyar ya kawo ta gida ashe rabuwar ta kusa lokacin basu kwana ashirin ba ta tashi da nakuda ina fada miki,  ta sha wuya baki ga yadda ya tashi hankalin sa ba ke kace shi ke nakudar haka sukace ba zata iya haihu da kanta ba shine fa za a shiga aiki,  ba ai aikin ba Allah ya amshi a barsa kan ai wata wata yaron yabi uwar zo kiga Aliyu wallahi kamar ba zai rai ba ya daina ci ya daina sha ga tunani ai fa nan ciwo yai raf dashi, ciwon nan da yanzu ba tsoho ba babba ya kama shi wai hawan jini,  mu dai Allah raba mu dashi ace yaro sai kaji shi da hawan jini ai duniya ta zama abinda ta zama, ina fada miki ga ulcer yaro sai ya hau tsamurewa da kyar da addu'a da rokan Allah, Aliyu yake rayuwa amman da tini shima mun rasa, to fa shikenan tin lokacin ya canja ko magana bai fiya so ba yafi son ya kadai ta abinci kuwa kina ganin sa zandamemen nan sai Aisha ta saka shi a gaba da lallashi, da komai kamar jariri, ai ita dai Aisha yar albarka ce, ta iya riko, kinga yadda ta riki Aliyu kuwa ko uwar sa bata rike shi kamar yadda ta raine shi ba, ita dai tana son yara amman Allah bai bata zaunanne ba, kinga fa haka ta samo mana wani yaro Abubakar wanda na fada miki yana auren yar autata suna can Canada da ya'ya  su har hudu, ai Aisha Allah ne kadai zai biya ta, ta kula da Aliyu da matar sa, ke yau suna gidan ta gobe suna gidan su basu da wajen zama tsayayye ita ke dawainiyya da su, ai kuwa itama taji mutuwar haka da rokan Allah fa aka fara samk kan sa, to kinji fa tin rasuwar matar sa ni ban 'kara ganin sa cikin nishadi ba sai haihuwar ki da yadda yake wa yaron ki, dan Allah da iyayen zasu dau tawa ai da an masa aure ko shima zai ga gudan jinin nasa ko? Ace yaro ya girna amman ba aure ga farouk nan ma yana koyi da dan uwan nashi."

Idon Maryam har yayi ja jin labarin Aliyu maikon kwallar dake kwarmin idon ta, ta saka hannu ta goge tana fadin
"Allah mata rahma. Ina rashin masoyi babban damuwa ce ni gani nan na rasa nawa na rasa iyaye na, na kasa sanin kowa nawa sai ku."

Maryam ta fada tana fashewa da kuka. Inna tace
"Haba yar nan ke kuwa kada kiyi kuka wani yazo ya zata wani abu nai miki dan Allah kiyi hakuri, ke kuwa kike da masu son ki,  wallahi zan iya rantse miki da Allah ina jin ki tamkar jika ta dan haka ki bar kuka komai kike so ki fada min ni nai miki alkawarin kula dake da miki duk abinda nake so kinji?"

Kai ta gyada tace
"Ban taba haduwa da mutane masu karamci kamar ku ba kun min komai duk da baku sanni ba Allah ya saka muku da gidan aljanna nagode sosai da sosai."

"Ba komai yiwa kai ne kai kasan halin da naka zai fada a ciki? Ki daina kukan to."
Hawaye ta goge Inna ta cigaba da mata hira tana sata dariya har ta dan sake amman abun na damun ta dan labarin Aliyu ya taba mata zuciya.

Fura Inna ta dama musu har da madara da kwakwa Maryam ta saka afirij dan ta dan yi sanyi sannan ta fito tai alwala dan an tada sallah magariba sallah tayi tana zaune tana addu'a har akai isha'i sukai sallah sannan ta mike tace
"Inna zan tafi sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Har ta kai kofa Inna tace
"Oh zo ki anshi furar ki."
Ta dauko jug Inna ta zuba mata da yawa sukai sallama. Ta fita, ta kusa zuwa sashen Ummi sai ga Farouk nan kallo daya yai mata ya gane tana da damuwa ba kamar dazu da ya ganta ba dan haka ya tsaya kallon ta can kuma yace
"Lafiya dai ko?"

Dagowa tayi dan ita bata san dashi ba. Kai ta dauke tace
"Ba komai."
"To sai da safe."

Suka bar wajen yai bangaren Inna ita kuma tai bangaren su. Tana shiga ta samu Ummi da Aliyu, Haidar a hannun Aliyu yana jijjiga shi, sama tayi Ummi da Aliyu suka bita da kallo Ummi tace
"Lafiya kuma?"

Hannu ya daga alamar 'Waya sani.' Haidar ya kalla yaga yai bacci ya mikawa Ummi yace
"Ummi a kwantar dashi, daga nan kiji me yake damun ta?"

Amsar sa tayi tai sama. Dakin Maryam ta shiga taga bata ciki, motsi taji a toilet ta kwantar da Haidar tare da dauko masa kayan baccin sa ta saka masa ta lullube shi sannan tai masa addu'a zaman jiran fitowar ta tayi. Bata jima ba ta fito daure da towel da hijab a saman kan ta.

Ummi ta kalla ta dan saki murmushi ta nufi doruwa ta dauki kayan baccin ta,  ta koma ta saka sannan ta fito hula ta saka akan ta ta nufi gadon tana fadin
"Ummi, Abba bai dawo bane?"

"Ya dawo menene?"
"Na ganki a zaune anan ne."

"To me zanje nai masa?"
Murmushi Maryam ta saki tace
"A'ah ba komai wai nace yaci abinci ne?"

"Yaci nasan yanzu ma ya kwata zauna muyi magana."
Zama tayi a gefen ta Ummi ta kamo hannun ta tace
"A duniya a halin yanzu baki da sama da Haidar to amman Haidar ba zai iya tambayar ki damuwar ki ba, ni din dai nice makusanciyar ki fiye da kowa a yanzu dan haka ki fada min me yake damun ki?"

"Ummi ba komai. Ni ba abinda yake damuna. Me zai damen ina dake?"
"Kin tabbata?"

Kai ta gyada tace
"To Allah ya dafa bari naje na kwanta kiyi addu'a sannan kiyiwa mai gidan nawa."
"To Ummi."

*Allah ya jikan mu ya sa muyi kyakyawan karshe. Amin*

*Antty*

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now