💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 20By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Ya fita ya kamo hannun ta haka suka karasa wajen aka shiga da ango da amarya yau sosai wajen ya hada manyan mutane dan abokan Aliyu duk sun zo yau dan gobe daga juma'at za a daura aure dan haka an kara samun ba'ki masu kwana.
An gudanar da biki yadda ya dace cikin nustuwa, girma da ilimi kowa abin ya burge shi, an yanka cake an sha rawa da hutu kamar ba gobe. Suna daga zaune ta hango Yaa Alkasim sit din su daya da Aisha suna ta hira murmushi tayi tace
"Allah tabbatar da alheri zan so ki zama cikin zuri'a ta."Rukkayya ta gano da abokin Aliyu suma zaune tace
"To ni kam da Yaa Ahmad nai miki kamu Allah ya hada kowa da rabon sa.""Tunanin me kike *Matar Haidar* "
Kallon sa tayi tana murmushi nan masu huta suka samu abin yi, tai kasa da kai tace
"Tunanin *Miji na* nake""Gani wane tunani na zaki, ki ta kallo na kawai!"
Ta kara dagowa sai tayi saurin yin kasa da kan ta a kunyace.Sai wuraren sha daya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Aliyu ya dubi Maryam wacce duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Key ya amsa wajen Abokin sa. Yace
"Ka tafi zan mai da Matata daga nan a gida zan kwana sai da safe kawai.""Allah tashe mu lafiya."
Sai da yaga tafiyar kowa sannan ya dawo cikin hall din wanda Maryam ce kadai a ciki. Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji dan yadda yake dan murza hannun nata cikin yanayin tsokanar mutum.Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin direba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan cinyar sa. A haka ya tayar da motar ya soma tuki cikin nutsuwa.
Shiru tayi jin yadda yake mata tsoro da fargaba dan tini wani lokaci da ya wuce da haka ta faru, dan haka kanta ta jingina a jikin kujera kawai ta zubawa titi ido. A hankali yace
"Tunanin me kike yi ne"Ta dan rufe idonta ta bude tace
"Babu komai"
muryar nan tata a sanyaye.
"Are you sure, har tunanin abinda nake miki da wanda zai biyo baya?"Fuska ta marairaice ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda abun baya ya dawo bata sabo dal tin jiya ma ta fara tuna abubuwan bare yau da taga sauran kwana daya ta zama mallakin sa kowa ya shaida tasan Aliyu zai iyai mata komai duk kunyar sa akan ta zai iya yin komai.
"Bana so ina ganin ki cikin tsoro Baby na."
Ajiyar zuciya ta sauke yace
"Zamuje gida zan baki sakon da na ajiye miki a daki na.""Da ka bari gobe ko Yaa Abdullah ka bawa ya kawon."
Kai ya girgiza yace
"Ke da kanki zaki amsa."A haka ya karasa cikin gidan su da mai gadi ya bude masa gate har bakin part din sa ya kai motar sannan ya fita ya zaga ya bude mata ta marairace masa fuska tace
"Dare fa Yayi Yaya ka bari gobe.""Wai meyasa kike min musu ne *Matar Haidat* ba kyau dai kin sani ko?"
Yana fada yai ciki ransa a dan bace.Compound din ta tsaya kallo ba kowa dan haka da sauri ta nufi wajen gate sai kuma ta tsaya tana tunani can ta juyo tana girgirza kan ta, ta nufi kofar dakin nasa. Baya falo dan haka ta nufi bedroom zaune ta ganshi ya cire rigar sa da babbar riga daga shi sai singlet da dogon wandon kayan da ya cire.
A gaban sa ta durkusa tace
"Kayi hakuri gani?"
Bai kula ta ba ta marairaice kamar zatai kuka tace
"Dan Allah kada kai fushi dani."Dagowa yai ya kalle ta sai ya mika mata hannu ta kama ya janyo ta ya zaunar akan cinyar sa. Yace
"Yaushe ne daurin auren mu?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...