💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 49By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Dakin da Maryam take ya koma ya same ta tana bacci fitowa yayi falo ya zauna yana tunanin me to Mama ta fadawa Maryam lallai yasan halin Mama sosai.
Zaune yake har Ummi ta dawo ta kalle shi, shi kadai a dakin tace
"Ina Maryam kuma?"
Sama ya kalla yace
"Tana daki!""Lafiya dai ko?"
"Eh na tashe ta dai tayi sallah ban sani ba ko ta koma."Sama tayi tana fadin
"Amman kuma ai yamma tayi ta sauko."A haka ya cigaba da kula da Maryam na tsawon sati biyu shi ke bata magani na safe, rana da dare haka nan Ummi in ta fita taga dan abu ta kawo mata shi kuma yan kayan kwadayi in suna gida yake hada mata duk da wasu da ta ci take yin aman su. Haka nan Inna ba ta daina kawo mata abun ba wani taci wani ko kalla bata yi.
Jikin dai da sauri dan maganin da ya daura ta akai kuma sun koma asibiti jinin ta yai kasa, zuciyar ma da sauki, kuma ta fara samun sauki dan sai ta kusan yini tana bacci.
A haka aka Fara azumi wanda Maryam taso tayi amman Aliyu ya hanata sam. Da azumi Ummi ko ta fita kafi karfe 2 ta dawo da ta dawo take shiga kitchen duk yadda Maryam ke son taimakawa Ummi a kitchen da ta shiga taji kauri ko wani abu za tai ta amai wannan yasa Ummi ta hanata.
Aliyu kuwa a daki yake yini karatu Alkur'ani wanda da anyi la'asar baya dawowa gida sai an sha ruwa dan a can masallacin alfurqan yake jin tafsir. Ana tashi zasuyi sallah da ya sha ruwa yake tahowa gida ko ya dawo ba wani abun kirki yake ci ba.
Tea ne sai dabino kawai. Daga nan in ya tafi masallacin sai goma zai dawo. Da ya dawo zai wanka ya dan kwanta karfe daya yake tashi kwana yake akan sallaya haka rayuwar su take gudana a koda yaushe.
A haka azumi ya Kai goma sha biyar lokacin tafiya Umrah Ummi hakura tai da zuwa saboda yanayin jikin Maryam. Abbi da Abba da Aliyu ne suka tafi. Mami sai saura sati daya sallah ta tafi. Gidan sai ya rage daga Inna sai Mama da Ummi da Maryam. Aliyu ma acan ba zama yai ba kullum yana harami yana sallah da addu'a ga matar sa da Maryam akan Allah ya bata lafiya. Kullum zai kira Ummi sau uku ya tambaye ta ya jikin Maryam kuma a tafiyar sa taje an kara dubata tare da cigaba da shan maganin ta. Sosai ta dan samu sauki dan cikin ya kara kwari.
*
Bayan Sallah da sati daya su Aliyu suka dawo, Ummi ce ta hada musu abinci na tarba, kala kala, lokacin da Aliyu yaga Maryam yai mamaki domin kuwa ta dan murmure ba kamar da ba.Inna ta mike ta fita tana fadin
"Bari naje na bar wajen nawa ba kowa!""To Inna sai anjima angode! Maryam tai ma mata godiya ta tafi. Ummi tace
"Kina shiga kuna gaisawa da safe kinji?"Kai ta gyada. Suna zaune a haka Aliyu ya shigo ya hangi Maryam zaune da dan cikin ta a gaba. Kai ya dauke dan ganin ta a wannan yanayin ya tino masa da Maryam matar sa. Ido ya dauke da sauri ya shiga dakin sa. Da kallo Ummi da Maryam suka bishi, yana shiga ya fada saman gado yana lumshe idon sa. Maryam kawai yake gani tana masa gizo a indon sa. Ido ya runtse yana fadin
"May your gentle soul continue to rest in peace Hayyaty"Da kyar ya mike ya shiga ya watsa ruwa ya dauro alwala kiran sallah yaji ana yi ya fita da sauri, rike da ledar da ya shigo da ita. Ba kowa a falo Dan haka ya ajiye akan dining ya fita.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...