Page 50

346 15 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page  50

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Tana shiga ta cire mayafin jikin ta ta juyo tana kallon sa. Kai yai kasa da shi tace
"Kai me ya hada ka da wannan yarinyar?"
"Nifa ba komai. Kawai Hamma Dr ne yace na kai ta super market!"

Wani kallo ta jefa masa tace
"Kada na kuma ganin ka tare da yarinyar nan."
"Mama..."

"Mama me? Kada na kuma nace!"
"To Mama!"
Ya mike yace
"Bari naje nai wanka."

Bata kalle sa ba ta shige daki ya mike ya fice shima.

*
Tinda cikin ta ya shiga wata takwas kuma sai hankalin ta ya fara tashi dan da ta kwanta bacci ba abinda take sai mafarkan Yaa Haidar da Ammi. Dan haka bata bacci sam, kwana take sallah duk ta shiga damuwa da ka ganta zaka ga tana cikin damuwa da kuma ta kadaita sai kuka.

*
Yau lahadi yawancin kowa yana gida yana hutun karshen mako, tin safe Maryam bata sauko ba Ummi ce ke ta aikace aikacen ta Aliyu na dining area tinda ya gama breakfast yake aiki a system din sa shi kan sa da yaji motsi a stair yake daga kai yaga ko Maryam ce amman shiru har wajen 12. Dan ba karamin sabo sukai da Maryam duk da bai fiya magana ba amman a irin wannan lokacin suna tare wani lokacin tana kwamce akam kujera shi kuma yana zaune a dining ko tsakiyar falo yana aiki duk wani motsi da za tai akan idon sa abu kadan zai juya ya kalle ta, sannan duk abun na bukatar mai ciki na kwadayi bata rabo dasu shiga dari fita dari sai ya shigo mata da abu.

Ummi ce ta fito a kitchen ta kalle shi tace
"Wai lafiya har yanzu bata sauko ba?"

"Kila bacci take."
Ya fada yana pressing system dinsa. Kallon sama tayi tace
"Let me go and check dai!"

Ta nufi sama ya bita da kallo. Dakin ta nufa ta bude kofar dakin, acan kuryar dakin ta hango ta akan sallaya ta hade kanta da gwiwa. Karasawa tayi a hankali ta dafa ta, da sauri ta dago idon ta duk hawaye. Zamewa Ummi tayi ta zauna tana fadin
"Lafiya meyasa kike kuka ko wani abu kike ji?"

Kai ta girgiza ta hau goge hawayen idon ta. Ummi tace
"A yanzu baki da kowa sama dani ki dauke ni as your Ammi, u should call me Ammi, come to me with all ur problem i promise to help you out insha Allah. So now tell me what is wrong with you?"

Hawayen idon ta, ta kara gogewa tana girgiza kai. Paper Ummi ta miko mata tace
"Fada min kinji!"
Amsa tayi tace
"Ummi i miss my past, i want to recall back."

"Dole kiji haka Maryam amman fada min wani abu akai miki?"
"No Ummi bana son na mutu ban gansu ba, ina tsoro kada wajen haihuwa na mutu."

Hannun ta Ummi ta kama tace
"Wa yace miki zaki mutu. Mutane nawa ne suka haihu shin mutuwa suke. Bazaki mutu ba insha Allahu sai kin tuno kowa kin koma gida cikin yan uwan ki. But before than ki dauke mu as your family kinji mu kan mu mun dauke ki yar mu kinji ko? Ki kwantar da hankalin ki."
Rumgume Ummi tayi tana kuka sosai. Ummi na lallashin ta da kyar tai shiru.

"Me kike so?"
Kai ta girgizawa Ummi.
"Akwai abinda kike ji?"

Nan ma ta girgiza kai. Tace
"To ki sauko kasa zama waje dayan ba dadi ai ko?"
Mikewa tayi ta dauko Alkur'ani da carbi ta biyo bayan Ummi. A dining ta hange sa bata kalle sa ba ta nufi falo ta zauna akasan carpet dan tafi jin dadin zaman kasa ta mike kafafun ta ta fara karantun Alkur'ani  idon ta kan Alkur'anin take karantawa a zuciyar ta.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now