Page 59

283 15 3
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 59

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

Da asuba da ya fito zai tafi masallaci ya ganta kwance akan kujera kai ya dauke ya fice kawai, Ummi ce ta sauko ta ganta sosai tai mamaki ta zauna tana tashin ta, ido ta bude wanda suka dan daga saboda kukan da ta sha. Ummi tace
"Me ya samu idon ki fuskar ki duk tai ja, idon ki ya kumbura."

Mutsuka idon ta take tace
'Ummi Yaya ne, Ummi wacce irin mace Yaya yake so?"
"Kije alwala kiyi sallah tukkunan."

Ta mike ta wuce sama wanka ta farayi sannan ta fito ta canja kaya, Maryam na zaune akan sallaya tana karatun Alkur'ani ta fito, ta tada sallah sannan ta koma kam gado ta kwanta.

Da safe Maryam na falo kwance akan kujera sanye da hijab har kasa, hannun ta daure da counter tana yin tasbihi, Ummi na kan two sitter, Tasleem ce ta fito sanye da dogon wando da riga karama kan ta ba dankwalli, ta zauna a kan hannun kujerar da Ummi take, Ummi ta kalle ta yace
"Abinci fa."

Cikin ta ta shafa tace
"Tukkuna Ummi ki fada min Ummi meyasa Yaya baya so na, wai wacce irin mata yake so?"
"Me ya kawo wannan to?"

"Shi yace na tambaya."
"Hmm Aliyu kenan, to shi Aliyu yana da wuyar sha'ani miskili ne bai son mutum mai surutu da rawar kai, yana son mace mai kamun kai da shiga ta mutunci duk kyale kyalen nan basa gaban sa fatan sa ya samu salihar mace, ai ke shaidace akan yar uwar ki ba ruwan ta ba sawa ba sakawa to dalilin da yasa ya so ta kenan kuma har yau yake kan son ta, kiyi kokari ki koyi wasu halaiyar nata in kina son Aliyu ya so ki."

"Ummi ai Yaya Maryam bata waye ba gaba daya tayi rayuwar waje amman kullum bata waye ba, da ba dan Yaa Aliyu ya aure ta ba da ina zaton ba mai auren ta a zamanin nan."
Ummi tace
"A haka kuma yaso ta yaki ki fa, ku kun dauki wayewa a zubar da mutunci ai zubar da mutunci mana, kalli fa yadda kika sauko kanki ba dan kwallin kuma ina tunanin acan ma zaki iya fita kusan haka, bayan a addini bai kamata wanda ba muharramin ki ba ya ganki a haka, bansan me yasa Yaya yake barin ku a haka ba, ga Maryam nan dai a gidan nan ko da mayafi ba zaki ganta ba kullum hijab amman ke kalli yadda kika sauko ba ruwanki wani ya ganki a haka wanda ba dai dai bane."

"Ummi Yaya ne fa."
"Yayan muharramin ki ne? Naga da aure a tsakanin ku."

Baki ta turo, Ummi tace
"Zagi na zaki?"
"Nifa Ummi a'ah ba abinda nace."

"Uhmm wallahi ki kula ace duk Yaya ya barku haka sai abinda kukayi, ko da yake laifin mahaifiyar taku ce tinda shi ba zama yake ba."
Fuska ta daure. Sallamar Aliyu ita tasa Ummi tayi shiru, suka amsa sallamar, a gefen Ummi ya zauna, Ummi ta kalle shi tace
"Ni sai naga duk ka rame Yaya bata kular min da kai ko?"

Yaya da take saukowa tace
"Allah yaso nazo da sai dai ai min sharri, wannan yaron naki dai yana da damuwa nayi nayi dashi ya fada min yaki, ko dan ni ba uwar sa bace, nasan ke ya fada miki, kullum bai cin abinci sai ya raba dare idon sa biyu sam bai hutawa ke daga kallo daya zaki gane yana da damuwa amman yaki ya fada kullum sai munyi fada dashi akan abinci sai kace wani yaro."

Ummi ta juyo tace
"Haba yaron kirki "
"Ummi nifa kewar ku nake kawai."

"Jika sai kace karamin yaro, Aliyu ka rage wannan kwulaficin naka ka girma fa in da ba dan kaddara ba ai kaima da yanzu kana da iyalai wanda zasu na maka haka amman kai kake yi, mufa tamu ta kusa karewa in kuma muka mutu fa shikenan zaka ce ka daina rayuwa ne? Dan Allah My Son kana ragewa kaji yaro na."
Kansa ya daura akan kafadar ta yace
"Ummi ba yanzu zaku tafi ku barni ba bana so Ummi dan Allah ki daina maganar nan, Maryam ta tafi ta barni so kike kema ki tafi ki barni?"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now