💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 32By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
*
Wani babban waje ta gani gefe wani katon masallaci wanda yake da bangaren maza da mata ga motoci da alama wasu matafiya ne suka tsaya yin sallah da cin abinci dan lokaci daya saura na rana. Ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta zaga bayi sannan ta shiga cikin masallacin ta tada sallah, tana ta zaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo ya buga karfe daya da rabi ta mike a hankali ta fita ta don duba abinda zata siya ta ci, tuwo da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta zauna ta bude ledan abincin tana gutsura guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar zata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari ta koma cikin masallacin ta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan tuwon ba, tana mayar da numfashi, ta kwanta ta dukunkunewa waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da zazzabin da ya rufeta lokaci daya, sai la'asar ta farka jin ana kiran sallah. Daren ranan a masallacin Maryam ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da zata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanzu, cike da fada take maganan, jikin Maryam yayi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lokacin saboda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga zazzabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda zata je ba, ganin ba zata kara ko da taku daya ba don kafafuwarta sun ma gaza daukar ta kuma ta fara tunanin ta nemi wani masallacin ta samu ta dan kwanta ko na kwana daya ne daga nan in sun kore ta ta kuma samun wani a bakin titi ta tsaya tana son samun napep dan bata jin zata iya yin tafiya kuma. Dayan hannun ne na tafiya dan haka ta nufi kan titin dan ta tsallaka wata mota ta taho da uban gudu tana dannan horn juyowa tayi duk sai ta rikice wanda me motar yana dannan burki amman yaki ya tsaya sai da yazo daf da ita sannan motar ta tsaya. Wanda Maryam ta durkushe a kasa dan ta rasa ina zatayi.Driver ne ya fito da sauri sannan masu motar da ake tukawa wasu dattawan Mata da Miji suka fito da sauri. Matar babba ce dan a kalla zatai shekara arbain da takwas haka, fara ce sosai wacce ke sanye da doguwar riga ta less army green ta saka milk mayafi akan ta. Indon ta sanye da farin glass, Wanda kana ganin su zaka san manyan mutane ne. Mijin ma manyan kaya ne a jikin sa milk shadda sai kyalli take ya saka yar ciki da babbar riga haka ya saka hula mai kyau da tsada sai tashin kamshi suke. Motar bayan su da take basu tsaro suma suka fito da sauri sukayo kan Maryam. Matar ce ta karasa ta dago Maryam wanda Maryam tayi baya zata fadi, da sauri matar ta kamo ta tana fadin
"Suma tayi!"Mijin ta, ta kalla tace
"Samo mana ruwa suma tayi!"
Daya daga cikin security ta ne yai maza ya karasa ya dauko ruwa a mota ya kawo, amsa tayi ta zuba a tafin hannun ta, ta shafa mata tayi a fuska amman bata farfado ba. Dago ta tayi ta nufi mota da ita tana fadin
"Ado a samar mana asibiti nan kusa please.""Ok Maah!"
Ya fada ya shiga mota sauran ma suka shiga cikin mota. Mutumin da suke tare can gidan baya ya shiga matar da Maryam kuma suna gidan tsakiya.Sai da sukai tafiya mai nisa sannan suka samu wani private asibiti mai kyau ciki suka shiga Matar ta fito da ita da sauri suka shiga ciki. Nurses ne suka amshe ta suka wuce da ita emergency, nan da nan suka shiga wani daki da ita suka kwantar da ita suka fara ceto rayuwar ta. Ko da numfashin ta ya dawo allurar bacci sukai mata saboda sun gane bata cikin nutsuwar ta kuma tana bukatar hutu sannan suka saka mata ruwa.
*
Maryam bata sake sanin abinda ya faru ba sai bayan kusan awa takwas da faruwar abun. A hankali ta bude idonta da yayi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yayi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe kirjin ta dake mata zugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lokaci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wannan matar da ta fito a mota wacce ke zaune d'an nesa da ita idanuwan ta da hankalin ta gaba daya na kan wayar dake hannunta, kokarin mikewa zaune take da kyar har lokacin tana dafe da kirjin ta dake mata azaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, motsin ta da taji yasa ta kallo direction dinta, mikewa tayi da sauri ganin ta tashi ta karaso kusa da ita tace
"Sannu ya kike ji?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...