💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 30By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
HML KHADIJA SANI DAUDA (MAMA) ALLAH SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN
Tana fita taji kirjin ta ya hau dukan uku uku ga kan ta da ya wani sara wanda hakan yasa ta durkusa tana dafe kan ta. Ta jima a haka sannan ta mike ta fara kalle kallen wajen sai kuma ta mike ta nufi babban titi tana tafiya tana haki a haka ta karasa kallon ababen hawa ta tsaye yi napep sai zuwa suke suna tsayawa a gaban ta amman ta kasa tsayar da daya a cikin, sam bata san me ko wanne hali take ciki ba a hankali ta fara taku wanda bata san kan titin ta hau ba wata mota ce taho a guje wanda tana ganin Maryam yasa ya danna wani uban horn tare da taka burki. Da sauri ta dago dan jin horn din shi ya dawo da Maryam daga tunanin da tatafi ta dago da sauri ganin yadda ya taho da gudu yasa ta rude sai kawai ta fadi a sume. Motar yai parking ya fito yayo wajen ta tare da mutanen dake bakin titin ganin bata numfashi yasa ta dauko ruwa aka yayyafa mata amman bata farfado ba da sauri yasa ta a mota ya bar wajen da sauri wani private asibiti ya gani nan ya shiga da ita nurses suka amshe ta. Cikin hukuncin Allah nan da nan ta farfado. Suka duba sukaga ba wata matsala bayani sukai masa sannan sukace zasu iya tafiya.
Dakin da take ya shiga ya same ta zaune ta hade kai da gwiwa tana kuka. Karasawa yayi yace
"Akwai inda yake miki ciwo ne?"Kai ta girgiza ba tare da ta dago ba. Yace
"Kukan me kike to?"
Kai ta kuma girgizawa. Kallon ta ya tsaya sai kuma yace
"Tashi mu tafi"Da sauri ta dago sai ta zuro kafafun ta, ta mike tabi bayan sa. A haka suka fita compound din asibitin wajen motar sa. Mota ya bude mata sai ta tsaya kallon sa yace
"Shiga mana!"Kallon sa ta tsaya sai ta girgiza kai. Murmushi yayi yace
"Na miki kama da barawon mutane ne? Shiga na kai ki inda zakije."
Addu'a tayi ta shiga sannan ya tada motar kallon ta yayi yace
"Ina zakije?"Shiru tayi dan ita sam bata san ina zata je ba. Shiru tayi can sai ta dauko papper da pen a jakar ta ta rubuta masa. Amsa yayi ya karanta yace
"Tafiya zakiyi?"
Kai ta gyada yace
"Wanne garin?"Kai ta dauke dan kuma me zai dame ta da tambayoyi tinda dai ta fada masa inda zata ba shikenan ba.
"Fada min mana."
A paper ta sake rubuta masa. amsa yayi yace
"Yan uwan ki ne acan ko kece can!"Kai kawai ta gyada. Tasha ya nufa da ita sannan yai parking suka fito tana ta kallon tashar daman haka tasha take tamkar kasuwa, a tsorace ta dinga bin bayan sa har sukaje wajen motocin ya saka ta a mota ya biya sannan ya juya ya kalle ta yace
"Allah tsare hanya kina kula in zaki tsallaka titi in ba zaki iya ba ki nemi taimakon wani kinji!"Kai ta gyada sannan tai masa godiya da hannu. Tana zaune a motar har ta cika aka tashi mota suka fara tafiya. Tafiya sukai mai nisa dan bata san hanyar ba kwata kwata bata taba yo nan wajejen ba a rayuwar ta to dan me zataje inda bata sani ba amman ta rasa amsar da zata bayar a hankali tana nesa da gida a hankali take manta komai dake tare da ita. Abu daya kawai take ji da jin zata kara nesa dashi shine Yaa Haidar shikenan garin da kabarin sa yake ma ta barshi, hawaye ne ya zubo mata ta daura hannu akan cikin ta da taji yana dan motsi a zuciya take fadin
"Yaa Haidar yasan da cikin jiki na kenan kome? In bai sani ba tayaya yake min zancen dan sa na kula dashi nace yana son sa, saboda me yake ce min insa yana masa addu'a kuma na fada masa Dadyn sa na son sa, kenan Yaa Haidar yasan da cikin!"Zancen da take da zuciyar ta kenan.
" *Ummu Haidar* "
Zuciyar ta, ta ambata. Ido ta runtse tana fadin
"Na tashi daga *Matar Haidar* na koma *Ummu Haidar* "Da sauri ta runtse idon ta tana fadin
"Ba zan taba tashi daga *Matar Haidar* ba zan kasance matar ka har a aljanna da izinin ubangiji na yadda na amince ni *Matar Haidar* ce kuma *Ummu Haidar* "
Sai ta saki murmushi wanda take yi hawaye na zubo mata a idon ta.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...