Page 18

359 16 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 16

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Ya mike ya nufi kofa ya fita. Gidan ya nufa ya shiga Babban falo ba kowa dakin Ammi ya shiga ya same ta zaune gaban ta gashin nama da madarar Ammi zaune tana duba wasu kaya. Zama yayi ya gaishe da Ammi sannan ya zauna a gefen ta yana fadin
"Kayan dadi aka samu ashe!"

"Muci!"
Cikin sa ya shafa yace
"Na koshi!"

Tace
"Shikenan!"
"Goben zaku gyaran kai ko?"

"Eh!"
"Karfe nawa zan zo na kai ku.?"

"A'ah kaje aikin ka ko driver ya kai su."
Ammi ta fada.
"Ammi na dauki hutu ai!"

"Au to shikenan. Allah ya taimaka."
Ta mike tayi cikin dakin ta. Ya kalli Maryam yace
" *Matar Haidar* kinga Haidar din naki?"

Kai ta gyada yace
"Zan iya tafiya?"
Fuska ta bata tace
"Bamuyi hira ba fa."

"In na zauna kar naje....."
"Kar kaje me?"

"Shikenan!"
"Naga sako dazu Amman Yaya yai yawa!"

Hannu ya daura akan lips din sa masu taushi pink kala yace
"Kada kice haka sunyi kadan ma nake gani."

Tai murmushi jin Ammi zata fito ya mike yace
"Zanje na kwanta gobe wajen 10am zanzo sai mu tafi."
"Allah kaimu nagode!"

Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kara kallon ta, mikewa tayi yace
"Muje na rakaka!"
Suka fita. Bakin gate taga yayi tace
"Ba anan zaka kwana ba?"

Kai ya gyada, idon ta ne ya kawo ruwa tace
"Saboda me to? Saboda jiya ko? Baka yafe min ba ko Yaya?"
"Na yafe miki *Matar Haidar* ni namanta da wani abu ya faru ma jiya, kawai ina hada kayana da wasu abubuwan ne me kike so na baki?"

"Ni da zaka kawo abin gidan mu in akwai abinda nake so in ka kawo na dauke."
"Shikenan sai da safen ko?"

Kai ta gyada ta daga masa hannu tana masa bye bye har ya juya ya fita. Juyawa tayi ta koma ciki. Dakin Ammi ta koma ta dauke kwanon dan kai wa kitchen Ammi tace
"Amman naga baki ci ba fa!"

"Ammi na koshi ne!"
Kallon ta Ammi ta tsaya yi tace
"Zo nan Maryam!"

Karasawa tayi ta zauna, Ammi ta bita da kallo sannan tace
"Meyake damun ki ne? Tinda kika dawo daga makaranta bakya cin abinci sosai ga tsurfar zabar abinci."

Cikinta ta shafa tace
"Nima Ammi ban sani ba."
Ta karasa magana tana hamma alamar bacci takeji.
"Je ki kwanta sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
"Amin!"
Ta fita ta ajiye plate din sannan ta shiga tai wanka tare da brush tazo ta kwanta. Tana kwanciyya bacci ya dauke ta.

Aliyu na shiga ya isa kan gadon sa, kwanciyya yayi yana mai lumshe ido, juyi ya fara akan gadon wanda sam ya kasa baccin har wajen karfe dayan dare mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa yayo alwala sannan ya fito ya hau kan sallaya nifala ya fara wanda har karfe uku idon sa biyu yana karatun Alkur'ani. Sai da yaji an fara kiran sallah sannan ya mike ya kuma watsa ruwa ya nufi masallaci.

Ba mutane sosai ya shiga ya zauna yana karayin karatu, sai kusan rabin awa sannan Abbi da Alkasim suka shiga daga can aka kara kiran sallah sannan mutane suka fara shiga dan yin sallah, ana idarwa suka gaisa da Abbi sannan ya tafi. Alkasin ya zauna a gefen sa yana kallon sa yace
"Ahmad yana ta kiran ka baka dauka ba."

"Bansan inda wayar ma take ba, me ya faru!"
"Zancen zuwan sa ne."

Mikewa sukai suka fita, a kofar gida suka tsaya yace
"Me yace maka?"
"Ba zai samu damar zuwa bane saboda wani aiki da ya tasar masa aka tura shi wani waje kuma a cikin week din nan ake son ya kai report yace kayi hakuri da ya gama zai zo yaci girkin amarya."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now