Page 45

339 13 2
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 45

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Karfe takwas da kwata Aliyu ya shigo tare da Abbah a falo suka zauna Abbah ya kalli Maryam yace
"Ya jikin?"
Tai masa alama da sauki. Sannan ya kalli Aliyu yace
" ya jikin nata kuwa?"

"Abbah da sauki sosai!"
"Allah kara sauki ta ci abinci kuwa?"

"Ai kasan sai a hankali zatana ci a sannu zata daina duk aman nan da rashin cin abincin insha Allahu."
"Allah ya yadda!"

Ya mike yai sama. Ummi tabi bayan sa, sun jima sannan suka sauko Abbah sanye da jallabiya daga gani wanka yayi dining suka shige. Ummi tace
"Ku taso muci abinci!"
Aliyu ya mike yana kallon Maryam dake girgiza kai. Yace
"Bazaki ci ba!"

Kai ta gyada ya nufi Ummi ta fara zuba masa ya dakatar da ita wai ya ishe shi. Ta kalli dan abincin tace
"Haidar what wrong with you!"
"Nothing Ummi!"

Abbah ya dago ya kalle su yace
"Me yake faruwa?"
"Abbah baya son cin abinci fa sam!"

Kai yai kasa dashi yace
"Ciki na ne ya cunkushe two days kuma ban jima da shan youghurt ba."
"Alright kadai na kiyayewa bana son rashin cin abinci da girman ka."

"Insha Allahu Abbah zan kiyaye!"
Suna Dining suka jiyowa Inna, Ummi ta mike tana fadin
"Barka da zuwa Inna!"

Aliyu da ya gama ya mike ya shige dakin sa. Inna ta bishi da kallo tace
"Yaron nan ya nuna min iko akan yarinyar nan yanzu dan Allah abinda yai min dazu ya kyauta."
Abbah ya mike yace
"Me Aliyun naki yayi?"

"A'ah naku dai. Wallahi yaron nan muna tare da uwata yazo ya dauke ta dan na bata abinci ni fa tsurfar sa na damuna ace mutu ba zai ci abincin gargajiya ba sai na zamani rayuwa ta tafi a haka kuwa. Yana yaro dai kato dashi amman yanzu rashin cin abinci da tsurfa duk tasa ya kare."
"Kiyi hakuri Inna."

"Wai me yasa baku da aiki sai nayi hakuri karfin ku Aliyun yafi da zai abu baza ana masa fada ba."
"Kiyi hakuri Inna za ai masa."
Ummi ta fada. Inna tace
"To Allah yasa."

Ta nufi Maryam da ta jingina da kujera tana fadin
"Sannu Uwata ya jikin?"
Dagowa tayi ta sakar mata murmushi tai alamar da sauki.

Inna ta mika mata cup din kunun da tayo mata tace
"Maza sha abin ki kan wancan bokan turan ya fito ya hanaki sha bana son ki kwan da yunwa sam!"
Amsa tayi ta kafa kai kadan ta sha ta ajiye cup din dan bata so tasha yadda zai saka ta amai.

Inna tace
"Yai dadi ko?"
Kai ta gyada. Inna tace
"Ai nasan zai miki dadi."

Ta mike tace
"Bari naje na kwanta sai da safe ko?"
"Allah bamu alheri Ummi da Abba suka fada."

Abbah ya bita suka fita. Suna fita Aliyu ya fito yana bata fuska. Ummi tace
"Zo nan!"
Aliyu ya karasa tace
"Bana so daga yau ka kara hanata cin abun Inna naga ba wani cin abincin take ba bare ace zai mata illa da ace bata ci ba ai gwara taci ko yaya ne ko? Kana gani anan baci take ba na Innan take dan tabawa kadan fa."

"To shikenan Ummi ba zan sake ba."
"Allah maka albarka."

"Amin ya hayyu ya qayyum tasha maganin ta taje ta kwanta ko?"
Da kan sa ya bata sannan ya nufi dakin sa.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now