Page 41

327 17 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 41

By
*MARYAM S INDABAWA*

Hakuri da Juriyya Online Writer's ✍
HAJOW

File din da ya ajiye ya dauka ya fara dubawa a nutse sai da ya dauki kusan 1 hour yana duba file din da nazarin abinda ke ciki sannan ya dauki bag din medicine duba su yayi ya ajiye. Kan gado ya hau ya bude hannun yai addu'a ya tofa ya shafe dukka jikin sa. Ya kwanta yana mai ambaton Allah a zuciyar sa da saman leben sa.

Karfe 3:30am ya mike bandaki ya shiga ya watsa ruwa ya fito daure da towel, ya fito yai rolling din sure ya dauki wata brown kalar jallabiya wacce take a goge ya saka ta sannan ya dauki hula, tashi ka fiya naci ya saka ya shafa turare mai dadin kamshi.

Kan sallaya ya hau yin sallah sannan ya zauna yana tasbihi ga Allah. A haka aka kira sallah ya tafi massalaci yana zuwa yai rala'atanil firij sannan aka tada sallah asuba. A masallaci ya zauna yai karatun Alkur'ani da azkar. Karfe bakwai ya fito daga masallacin dake jikin gidan su wanda masallacin ma a cikin gidan su aka cire shi.

*
Ummi kuwa daki ta koma tai wanka ta shirya cikin kayan bacci dakin Abbah ta nufa ta same shi yana aiki a system zama tayi tace
"Ranka ya dade bakai bacci ba?"
"Banyi ba wallahi aikin nan nake son na karasa!"

Kai ta karya tace
"Daman nazo nai maka sai da safe ne!"
Dagowa yayi yace
"Ina zaki?"

"Alfarma nake nema zani wajen yarinyar can kaga halin da take ciki in da mutum a kusa da ita zata fi jin dadi!"
"Ni kuma sai ki barni."

'In ka barni in kace a'ah kuma ba zani ba. Amman nasan ka da taimako."
Hannun ta ya kama yace
"Bazan hanaki ba amman tayaya zakina kula dani?"

"Baka da matsalar wannan insha Allah!"
"Shikenan tashi kije ki kula da ita."

"Nagode sai da safe!"
Ta mike ta fita. Maryam tana ta bacci kan gadon ta hau ta kashe wuta ta kwanta. Can dare Maryam ta tashi da yunwa da ishi mikewa tayi ta kunna fitila sannan ta diro kafar ta kasa. Basket din dazu ta gani ta nufa ta bude ta dauki spoon ta fara shan faten, tana cikin sha Ummi ta mike ta tsaya kallon ta tasha da yawa ta shiga bandaki ta dinga kakarin amai amman batai ba. Can ta fito ta zauna a bakin gado tana rawar sanyi.

Ummi tace
"Zazzabi kuma kike ji?"
Kai ta gyada ta miko mata bargo ta lulluba baccin da basu koma ba kenan dan yadda jikin Maryam yai zafi.

Sai asuba bacci ya dauke ta Ummi tai sallah ta tashe ta tayi sallah ta koma bacci mai nauyi ya dauke ta

A hankali yake taku cikin kamala da nutsuwa a haka ya karaso cikin gate din nasu da yake gaisawa da securies din gidan nasu sannan ya nufi sashen Ummi kai tsaye. Ummi daga nan dakin Abbah taje suka gaisa sannan ta sauka ta fara aikin gidan duk da ba datti yai ba ta saka turare mai dadin kamshi sannan ta shiga kitchen

Ba kowa a babban falon dan haka dakin sa ya wuce kai tsaye yana shiga ya cire tattausan jallabiyar dake jikin sa ya shiga bathroom daga shi sai gajeren wando da singlet.

Wanka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi. Yana fitowa, ya wuce gaban dresing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikin shi ya karato.

Gaban wardrobe ya karasa ya shirya cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wando kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue black color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi, hular itama farace sai ratsin blue black, hakama takalman sawunshi da suka kasance half cover,  Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai. Yai wanka da turare wanda nan da nan kamshi ya kara cika dakin.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now