💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 85By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
A mota ta same shi ta shiga ta zauna ta dauke kai tana kallon waje, murmushi kawai yayi ya tada mota suka fita a gidan, hannun ta ya kamo yana murzawa a hankali yace
"Wai yau dani ake fushi."Bata juyo ba a haka ya dinga murza hannun ta har suka karasa gida yana bude kofa ta bude ta fita tare da dauka flask din da ta shigo dashi, a falo ya same ta zata shiga daki ya karasa ya rumgume ta yace
"Tab Allah baki isa ba ki ma daina tin wuri kuma abu daya zan fada miki kada ki soma sawa a ranki zan iya barin ki zuwa wani waje kwana dan ba zan taba iya kwana ba a jikin ki ba ki tausayawa dan Babyn ki mana, kema kinsan komai dai."Dariya da tausayi ya bata dan tabbas tasan ba zai iya ba, yini daya in bai yi da ita ba ma ya ba lafiya bare ace kwana. Haka ya dinga lallashin ta da kalamai masu dadi da nuna mata illar barin sa shi kadai din da haka ta hakura ta taya shi sukai wanka ta bashi abinci da kanta sannan suka zauna suna shan soyayyar su.
Tin ranar da Najwa ta haihu kullum daga makaranta can yake kai ta sai dare suke dawowa, ana ya gobe sunane da kyar ya yadda zata kwana.
Duk abinda take bukata ta saka a cikin akwati, tana cikin hada kaya ya shigo ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda take ta zuba kaya a cikin akwati, dagowa tayi ta saki murmushi tace
"Yaya in ta so mu tafi?"
"Ba zaki lecture ba?"Baki ta turo tace
"Yaya ba dole ne yayi ba ni kawai ka kaini gidan Ummi."
Ya karaso ya amshi akwatin yana rufewa yace
"Wannan uban kayan fa?""Kala uku ne fa Yaya."
"Gobe dai zamu dawo.""Naji."
Ya dauke akwatin ya ajiye, a kasa yace
"Dauko mayafin naki."
Ya fita da akwatin.Har gida ya shiga ya dauki kayan ya shiga dasu sama ta wuce dakin Najwa acan ta samu Aisha tana shiga Baby ta dauka suka gaisa sannan ta tafi wajen Ummi da Babyn
A can ta samu Yaa Haidar, gaisawa sukai da Ummi sannan ta koma dakin Maryam, da kallo Haidar ya bita, har Ummi ta gane, yana dagowa suka hada ido da sauri ya mike yana sussunne kai yace
"Ummi bari naje sai na dawo.""Allah kiyaye hanya Allah bada sa'a."
Yana fita ya fara neman layin Maryam, tana zaune cikin su Aisha kiran ya shigo, dauka tayi tace
"Yaya.""Matar Haidar zan tafi."
"To Yaya Allah kiyaye hanya.""A'ah a'ah ban yadda ba."
"To me zan maka Yaya?""Maza ki zo ki wa mijin ki bye bye common my dear.'
Babyn ta mikawa Aisha tace
"Honey ba dai rigima ba bari naje."Dariya sukai ta mike ta fita, a kasa ta same shi zaune, ta karasa tana fadin
"Honey gani."
Hannun ta ya janyo ta fada saman sa ya rumgume ta kallon dakin ta fara tace
"Yaya a gidan Ummi fa muke.""Bake kika zaba ba."
Baki ta turo ya matso da face din sa ya fara kissing lips din ta, kofa sukaji an bude da sauri ta zare bakin ta tana barin jikin sa, Mami da ta gansu ta dauke kai kamar bata san da mutane a falon ba, Maryam ce tace
"Ina yini Mami?"Mami ta juyo tana fadin
"Ah yaushe kuka shigo?"
"Dazu."Aliyu ya mike ya sauka kasa yana gashe da Mami ta amsa tana yin sama, mikewa tayi ta nufi stairs tana fadin
"Ni dai Yaya sai ka dawo."
Hannun ta ya kamo, ta juyo kamar zatai kuka tace
"Yaya ni dai ni dai."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...