Page 22

361 14 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 22

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

*
Maryam na zaune sakon ya shigo hawaye ta fara na farin ciki da sauri ta mike ta tada sallah godiya ga Allah ta idar ta jima tana addu'a su Aisha sai huto da vedio suke mata.

In kaga Aliyu bakin sa ya kasa rufuwa sai Allah sanya alheri ake masa yana ta washe baki a ka'ida sai 3pm za a tafi reception dan haka daga nan gidan su Maryam suka isa. Bangaren Ammi suka fara shiga suka gaisheta da godiya Yaya Fadima tai musu jagora bangaren Yaa Muhammad.

Suna shiga ya dinga baza ido dan ya gano Maryam a tsakiyar Aisha da Rukayya ya hango ta an rufe mata fuska da sauri ya karasa ya rumgume ta tsam a jikin sa yana fadin
"Alhamdulillah finally jama'a sun shaida abin boye,  Maryam ta zama *Matar Haidar* farin cikina,  hakika ko yau na mutu buri na ya cika mutane sun shaida ke din Matata ce."

Yan dakin suka hau Kabbara suna fadin
"Allahu Akbar Allah ya bada zaman lafiya ya bada zuri'a mai albarka."

Fuskar Maryam ya dago yaga hawaye hannu yasa ya goge mata yace
"Kice Alhamdulillah Maryam komai ya faru dake mai kyau ko akasin haka kice Alhamdulillah Allah zai kara miki sama da abinda  kika sama."
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
Ta furta tana jin wani sanyi a zuciyar ta.

Haka aka dinga daukar su picture masuyi nayi masu vedio nayi anan suka jima dan sai uku sannan suka tafi kamar kar su rabu ya tafi yana daga mata hannu itama haka. Wanda yana tafiya taji zuciyarta, ta tsinke gaban ta na faduwa.

Nan aka fara yinin gida inda Amarya ta shiga dan canja kaya ta saka wani less mai kyau sea green ta yafa babban mayafi batai makeup ba yan matan amarya suka sha ankon atamfa green and blue sunyi kyau sallah la'asar sukai sannan suka fito suka zauna a inda akai decoration aka fara raba abinci ana ci ana sha ana kida da rawa mata ne kadai ke yini kamar yadda gidan Mamah ma suke can suke yi.

Su Aliyu kuma suna can Meena event centre ana reception abokai sai abinci suke ci shi kuwa yana zaune a takure waje daya. Alkasim ne ya karasa yace
"Ya dai Angon Maryam?"

Hannun sa ya kamo suka fita a wajen yace
"Buden mota na kwanta ciki na ke ciwo."
Bude masa yai ya shiga baya yace
"Ko mu tafi asibiti ne?"

"A'ah kaje ka kula da sauran abokan mu kace musu bana jin dadi ne."
Kwanciyya yayi Alkasin yace
'Ba matsala?"

Kai ya gyada Alkasim ya juya ya tafi Aliyu ya rufe kofar motar ya kunna AC amman gumi yake dan haka ya mike ya zare Babbar rigar sa. Wayar sa ya dauko ya fara rubuta sako
" *Matar Haidar* ki yafewa Haidar, Haidar yana son ki burin sa ya rayu dake har karshen rayuwar sa."

Ya ajiye wayar yana dafe cikin sa dake juya masa wanda ya jike da gumi ya jingina kai yana fitar da numfashin sa da kyar.

Maryam dake wajen biki hankalinta gaba daya baya wajen dan yadda zuciyar ta ke bugawa sakon Aliyu ne ya shigo ta karanta ta kuma karantawa amman ta kasa daina karantawa kuma gaban ta bai daina bugawa ba.

Alkasim kuwa yana can yana fama da mutane wanda suke da yawa dan ka rantse lokacin aka daura aure kowa yana sha'anin gaban sa wasu na cin abinci wasu hira dan haka duk ba su lura da rashin Aliyu ba.

Wani juyi da cikin sa yayi wanda yasa ya saki salati tare da lumshe idon wanda nan take numfashin sa ya fara masa wuya dawowa,  haka ya dinga jan sa da kyar wanda in yaja baya iya dawo da wanda ya shiga sai dai ya nemi wata iska,  dan haka abun sai ya hadar masa goma da ishirin ga ciwon ciki ga numfashin sa dake neman daukewa. Hannun sa akan cikin sa yana juyi ba abinda yake sai ambaton Allah

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now