Page 75

454 21 4
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 75

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Washe gari da daddare wajen karfe tara ta fito daga bangaren Ammi zata wajen Ummi, tinda ya fito daga compound ya hango ta wannan yasa ya koma ciki da sauri ya buya a jikin flowers din dake wajen, ta karaso wajen ta shiga, hannu yasa ya janyo ta jikin sa baki ta bude zatai ihu yai saurin daura tafin hannun sa akan bakin ta yana fadin
"Ke kar ki taran mutane."

Ido ta zaro tana kallon sa kirjin ta na dukan uku uku, ta marairaice ta zame bakin ta tace
"To Yaya ba tsoratar dani kayi ba."

Ya dan harare ta yace
"Shine zaki min ihu to."
Baki ta dan turo, yana kallon ta yace
"Wato ke yanzu baki iya gaisuwa ba ko? In kinga mutane ma sai ki fara baccin karya ko?"

Baki ta dan turo ta juya tace
"To ni yaushe na ganka tinda kuka zo ma ko nema na bakai ba sai ta yaron ka kake."
Tai magana hawaye na taruwa a idon ta ya zagayo gaban ta yana kallon yadda hawayen ya taru a idon ta, hannun ta ya kama suka karasa wani waje da yake da dakali suka zauna yace
"Yanzu ni dake waye me laifi?"

Da hannu ta nuna sa, yace
"To ni menene laifin nawa?"
"Gashi nan baka nemana ko son ganina bakayi ina ta murna zaku zo amman shine kai baka neman na."

Tai maganar tana sunkuyar da kanta dan bata san yadda akai ta fada masa ba kawai abin na ranta ne bata ji dadi ba ace wai yazo kwana biyu amman basu hadu ba bai kuma damu da neman ta ba, sai Haidar tare suke yini gaba daya fa sai jiyan nan ta ganshi ai dai ko kiranta yayi ashe saboda Haidar yake kiranta.

"To shikenan am sorry nayi laifi amman ke meyasa bazaki neman ba."
Ido ta dan zaro tace
"Mata ita ke zuwa wajen namiji?"

"Menene a ciki, naga yanzu kin zama matata."
Kai tayi kasa dashi yace
"Ko dan ni ba a so na, ai da Muhammad ne da zaki nemesa ko a waya ne, amman ni fada min tin da kuka zo Kano kin neman in bani na neme ki ba."

Baki ta dan turo tace
"Uhmm kai ma ai Haidar kake nema."
"Ohk naji na nemi Haidar amman ai ta wajen ki ko? Kuma sai mun gaisa in naso zan kira Aunty Nusy ta kira min shi ko Alkasim."

"Uhmm uhmm to kayi hakuri ni bansan me zan kira nace ba."
"Oh har gaisawa."

"Uhm uhmm to naji kayi hakuri."
Kamo hannun ta yayi ya juyo da ita yace
"To na hakura, yanzu gani kalle ni shikenan gani."

Ta dago ta dan kalle sa sai ta dauke kan ta, yace
"Oh har kin gama kallon nawa."
Mikewa tayi tace
"Uhmm ni wajen Sitti zani sai da safe."

Ta juya zata tafi ya kamo hannun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kamshin turaren su na tashi, dagowa yai yana kallon ta, itama shi take kalla, Yaa Farouk ne ya shigo kamar ance ya juyo ya gansu baki ya saki yana kallon love wayar sa ya zaro ya fara snapping nasu picture hasken flash din shi yasa suka juyo a tare da sauri Aliyu ya sake ta yana hade rai ya kalli Farouk yace
"Menene haka?"

"Alhaji Yaa Hamma tuba nake soyayya na gani kuma abun yai kyau shiyasa na tsaya koya."
Ya fada yana murmushi Haidar ya karasa yana kama kunnen sa yace
"Gidan ku."

Da sauri Maryam ta bar wajen, Farouk ya hau ihu yana fadin
"Tuba nake Yaya, Dr Hamma."

Ya rankwashe shi ya amshi wayar yana kallon screem din picture din yayi kyau sosai, sun shagala kallon junan su ba karamin kyau sukai da dacewa da juna ba. Ya mika masa wayar yace
"Tafi ka ban waje."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now