💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 6By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Jawahir tai murmushi tace
"Yaya nane fa sunan sa Yaa Khalifa."
"Tabbas kina min maganar sa amman ba sosai ba kin fi yin na Yaya Khalid."
"Yaa Khalid dan yayar Momy ne wanda ta jima da rasuwa so yana wajen Momy as u can see am the only female daugther to my father sai kanne biyu da nake dasu maza, Yaa Khalifa is my stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu za ki fara gani, bai zama a kasar nan yanzu haka bai fi shekara da dawowa ba so shiyasa bamu wani shaku ba dan acan yai study nasa tin primary har yanzu da yake likita so kinga dalili but i love my brother "Maryam tace
"Ayya!"
A haka suka karasa conpound Jawahir na biye da ita, a compound suka same shi Jawahir ta karasa tace
"Yaya Momy na kiran ka."Maryam ya kalla yai ciki kawai, bai jima ba ya fito yace
"Muje to."
Maryam ta tsaya a baya, Jawahir ta kamo hannun ta tace
"Feel free sis Yaya nane fa."Ta fada tana mata wani murmushi itama mayar mata tayi ta bude mata gaban mota ta shiga aka bude baya aka zuba mata kayan da wanda Jawahir ta bata da na wajen Momy. Jawahir ta rufe kofar tace
"Byee Besty sai mun hadu Monday, nagode sosai"
murmushin karfin hali Maryam ta mata bata ce komai ba, Jawahir ta kalli Yaa Khalifa tace
"Yaya ka kular min da Besty na."Hararar wasa yai mata bai ce komai ba yayi horn ya bar wajen, a haka suka fita a gidan, har suka hau saman titi babu wanda yace komai cikinsu, bayan wani lokaci yace
"Wacce unguwar za ki?"
Kan ta a kasa tana wasa da yatsun ta ta fada masa, bai ce komai ba, sai da suka shiga unguwar sannan yace
"Wane layin?"
Ta gaya masa, daga nan kuma ta dinga nuna masa Inda zai bi har suka shigo gate din layinsu, dai dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ya danna horn mai gadi ya leko yana ganin Maryam ya bude gate din suka shiga, sai da ya tsaya ta bude motar ta fita tace
"Nagode"Ciki tayi ya bita da kallo zai reverse yaga kayan ta masu aikin ya bawa, sukai mata. Ciki ta nufa bakin gate din su, Aliyu ta gani bakin gate din alamar fita zai yi don makullin motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar da ta ajiye ta ya sake kallonta, kai tayi kasa dashi tai ciki da sauri gabanta na faduwa, sai da ta kai kofar falon su ta juyo ganin sa tayi tsaye har lokacin yana kallon ta kai ta dauke tare da turo baki ta shiga da sallama, Ummi na sama dan haka itama can ta wuce direct dakin Ummi ta shiga, Ummi tace
"Ah Daugther sai yanzu ko?""Ummi kiyi hakuri kinsan Halin Jawahir kememe taki ta barni na taho wai sai na gaida da Dady kiyi hakuri."
"Daman Yayan ki ne yake ta fada yanzu ma gidan na fada masa ya tafi tahowa dake Allah yasa bai fita ba dan saukar sa kenan, sai fada yake dare yayi kuma baki fita da kowa ba driver ma haka, gashi ina kira baki dauka ba.""Na ganshi a kasa kinsan wayar tawa tana silent amman komi lafiya, Yayan tane ai ya kawo ni."
Mai aikin su ce ta shigo da kayan ta ajiye Ummi tace
"Na menene?""Baba Anas yace a kawowa Maryam."
"Oh nagode."
Maryam ta fada tana fadin
"Ummi ji uban kayan da suka bani."Nan ta hau babbudewa Ummi tace
"Angode Allah ya saka da alheri ya jikin nata?"
"Taji sauki.""Allah kara sauki."
Motsi ta jiyo ta mike da sauri tai daki dan bata son ma ya shigo su hadu, zama yayi ya kalli Ummi yace
"Waye ya kawo ta?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...