💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 56By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Bayan wata hudu.
Tsaye take a kitchen tana karasa miyar da ta daura, Ummi na gaban sink tana wanke kwanuka, gas din ta rage ta rufe miyar sannan ta tafi wajen Ummi tana fadin
"Ummi nace ki bari na karasa dan Allah!"Ta dauki kwanon tana dauraye wa. Ummi tace
"Ai na kusa bari kawai na karasa."Haka suka cigaba dayi Ummi na wankewa Maryam na daurayewa. A haka har suka gaba Maryam ta kwashe ta kai ma'ajiyar, Ummi kuma ta dauraye wajen.
Sallamar Aliyu suka jiyo suka amsa Ummi na fadin
"Mai gida ya dawo."Ta fita Maryam ta karasa wajen miya ta kashe gas din ta zuba a flask sannan ta dauraye hannun ta. Fita tayi zuwa falo.
Haidar ta gano yana daddafa kujera yana tafiya tare da gwaranci. Aliyu na zaune ya jingina da kujera Ummi na kallon Haidar tana fadin
"Wato Haidar dai ya dage kan ya shekara sai ya taka."Yana ganin Maryam ya fara daga mata hannu yana fadin
"Ammmmiii Mommmi Annnttti."
Karasowa tai ta dauke shi tana fadin
"Oyoyo yaron Ummi."Ta dauke shi tare da kallo Aliyu da tin da ta haihu ya daina sakar mata duk wannan kulawar ya daina sai dai Haidar ita daga gaisuwa shikenan. A hankali tace
"Sannu da zuwa Yaa Aliyu!""Yauwah!"
Kawai ya fada ba tare da ya kalli inda take ba ya cigaba da danna wayar sa. Ummi dai bata tanka ba itama sai ta cigaba da kallon Haidar dake tai mata gwale gwale shi alallai labari yake bata ita kuma tana ta biye masa can Aliyu ya mike yai daki dukkan su da kallo suka bishi.Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Zo nan Maryam!"
Mikewa tayi rike da Haidar suka karasa, Ummi tace
"Kada ki damu da halin yayan ki, haka yake wani irin miskili ne ba kasafai aka fi gane abinda yake so ba, amman zan fada miki Aliyu bai son rawar kai sam duk da nasan ke ba ruwan ki, yana son nutsatsen mutum kamar yadda kike bai son hayaniya dan haka please kar ki sa damuwa kinji?"Murmushi Maryam ta kwakwalo dan sam bata son wannan canjin daga gareshi da safe da rana da dare sai ya dubata da lallashin ta me take so da matsa mata akan abu ko zuwa motsa jiki in tana damuwa yafi kowa damuwa amman yanzu ya canja bai damu da ita ba ko zasuyi kwana nawa bai ganta ba bai damu ba, sam bata son haka amman ya zatayi tinda haka yake zata daure ta daina damuwa insha Allahu. Dagowa tayi ta kalli Ummi tace
"Ba komai Ummi na jima da gane hakan.""Yauwah Maryama."
Ta mike sukai sama ita da Haidar tana fadin
"Bari nai masa wanka kan ai magariba."*
8:15pm
Dakin sa ta Shiga da sallama, ya amsa ta Shiga, yana zaune akan carpet gaban sa system Haidar na kan gado gaban sa biskit, alawa da chocolate."Ummi!"
Haidar ya fada yana mika mata wata alawa.
"A'ah Haidar kayan zakin nan ai sai ku."Ta zauna tana fadin
"Shiyasa kake gudowa nan, dan sai abinda kake so kake yi ko?"Aliyu ya kalli Haidar dake shan alawa, murmushi yayi ya juyo yace
"To Ummi ai gwara abarshi yai abinda yake so ko?""Hmmm wajen ka nazo Doctor."
Dagowa yayi yace
"To Ummi lafiya dai ko?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...