Page 14

452 18 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 14

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


Karfe shida duk sun fito suna parking space sun rumgume juna ita da Aisha da Rukayya. Sai kuka suke. Yaa Aliyu ne ya karasa yace
"Ma'ul Ayn menene na kukan?"

Kukan take bayan ta sake su. Ya kalle ta cikin so da kulawa yace
"Amman kinsan bana son kukan ki ko?"
Kai ta gyada yace
"To stop it in bakya so nima na fara!"

Hannu tasa ta fara goge hawayen duk da tana gogewa yana kara zubowa ya sa handkerchief yana goge mata sai da ta daina kukan yace
"To ku menene na kuka naga next week kuna tare fa."

"Haka ne Yaa Haidar,  Besty yaushe zamuje rabon?"
"Rabon me?"
Yaa Aliyu ya tambaya.

"Kati man."
"No My Queen ba rabon da zatai zan kawo muku kuje ku raba ku bar min Mata ta huta yadda take kwana bata bacci dis week ramuwar bacci zatayi ko Baby?"

Kai ta gyada. Aisha tace
"Mu kuma kada muyi?"
"No ku da ita da bambanci ita aure zatayi gwara ta huta kan mu tare ko? Ku kuwa kullum zakuyi ta baccin ku,  ku yini ku kwana kuna yi."

Yaa Alkasim ne ya karaso yace
"Please Aliyu ka barta suyi sallama kafiya jaraba kai kam."
"What?"

Ya fada yana kamo hannun sa sukai can gefe ya murda hannun sa yace
"Ai Matata ce ina ruwan ka."
"Za dai ta zama matar naka ka bari in ta zama sai ka takura mata,  wallahi irin kune ke sa mace ta rame dan jarabar ku."

A can kuwa Rukky ce tace
"Allah Besty kinji dadi kin samu mai son ki."
Murmushi tayi ta kalli gefen su Yaa Haidar sai ta saki murmushi tace
"Alhamdulillah! Kuma zaku samu masu son ku da yaddar Allah."

Aisha tace
"Allah yasa. Amman fa naga Yayan namu zai yi naci Besty!"
Rukayya ce tace
"Itama ai da alama."

"Kuji sharri mu ba ruwan mu."
"Ku din kada ki manta ko ya yazo sai kin canja ki ta wani lumshe idanu kamar....."

Duka ta kai mata tace
"Iyee kace ido kika sa min."
"Hmmm ni ai last dawowar da yayi da ita nan da taje ganin likita nasha mamaki naga love wallahi kamar ya dauke ta haka ya dinga yi. Gaskiya zan zo ina koyar course na soyayya."

"Ji ku,"
Ta fada tana nuna su
"Ku wa yasan ya kuke dan dai ni kullum yana zuwa shiyasa kuka saka mana ido."

"Hmmm Allah Maryam ki godewa Allah Yaa Haidar na son ki kinyi dace sai dai muce Allah tabbatar da alheri. *Matar Haiydar* in the next seven days,  Allah nuna mana."
"Amin. Allah ya kaimu next week musha shagali mu mika ki dakin Yaa Haidar sai ku cinye kan ku."

"Ai kam ko kadan bazamu rage kan mu ba."
Maryam ta fada
"Ku ba?"
Rukayya ta fada.

Kanwar Aisha ce ta karaso tace
"Yaya Aisha wai kizo mu tafi"
"Toh!"

Ta fada tana fadin
"Sister bye!"

Har ta juya Maryam tace
"Larabar zaki taho ko?"
"Insha Allah sai munyi waya anjima."

"Ok muje nayiwa su Mum sallama."
Suka karasa sukai musu sallama sannan sukaje wajen Momy Rukayya sukai sallama ta juyo ta dawo kowa ya shiga mota. Motar Yaa Alkasim suka shiga,  shi da Yaa Fadima a gaba,  Ita da Yaa Aliyu a baya. Su Ammi da Ummah da sauran yayyane nata a mota daya masu aikin su a dayar motar.

Kai ta jingina a jikin kujera tace
"My Hayyat!"
"Na'am Ma'ul Ayn!"

"Na gaji!"
"Na sani Bae taho in miki tausa!"

Kallon sa tayi ta make kafada murmushi yayi ya matso da kan sa wajen kunnen ta yai mata rada,  da sauri ta matsa tana rufe fuskar ta da hannunta dan ya bata kunya sosai. Shima murmushin yayi ya dan cije lips dinsa na kasa yace
"Kika shigo hannu na ko?"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now