💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 67By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Suka shiga a gefen Abbi Aliyu yai sallah. Ana idar da sallah liman ya nemi shaidun madaura auren da za ayi, Abba da Abbi da Yayan su Ummi suka karasa wajen Liman, nan aka bada health status din amarya da ango Abba ne ya zaro kudi a aljihun sa ya ajiye a take aka daura aure.
Aliyu dake zaune a inda yake bai taba zaton sunan da yaji an kira na angon ba ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba da Abbi ko kiftawa babu, Farouk ma cike da mamaki yake kallon su Abbi. Aliyu kuwa ko motsi ya kasa, can ya lumshe ido ya bude zuciyarsa na bugawa.
Abba ne ya karaso wajen ya sakar ma Aliyu murmushi yace
"Ina fatan ba zaka bani kunya ba. Allah ya taya ka riko."
Kasa gane inda zancen Abba, Aliyu yayi.....*
Maryam ce kwance akan gado bayan ta idar da sallah counter ce a hannun ta tana dannawa tare da motsa bakin ta, idon ta a lumshe yake, Jawahir da Najwa na falo suna zazzaune, Basma ce kadai zaune a gefen gadon, kamar ance ta bude idon ta ya sauka akan agogon dakin su wanda ya nuna biyu da yan mintuna, bugawar zuciyar ta ce ta dadu tai saurin mai da idon ta, ta rufe tabbas tasan by this time an riga da an daura auren shikenan ta zama matar Muhammad Auwal, wani yanayi ta fada wanda ta kasa gane wane iri ne, mamakin ta daya zuwa biyu, shine na rashin ganin sakon Muhammad wanda tasan a duk halin da yake yai alkawarin shi zai fara shaida mata daurin auren su, to amman meyasa bai fada mata ba ko da yake dama fada ce tasa kawai tayaya yana cikin mutane zai samu damar sanar mata.Guda taji ana yi a kasa wanda ya kara sawa faduwar gaban ta, dan har sai da ta dafe kirjin ta, ta runtsa idonta, tana karanto addu'a a ranta ko zata samu natsuwa daga bugawan da zuciyarta ke yi,
Daga masallaci gaba daya gida suka yo, Aliyu kasa tukin ma yayi gaba daya, Abba da Abbi na mota daya a haka suka shigo cikin compound din wanda yake cike da yan uwan su dan yadda suka dauki Maryam tamkar yar Ummin ce dan haka tai gayya abokan ta da yan uwa haka ma Mami, ga Hajiya Inna gasu Anty Asiya da Hanna kowa da tawagarsa, Mami ce ta fara hango su Abba daga ganin yanayin su ya nuna mata basa cikin nutsuwar su ba tin yanzu ba tin kafin su fita ma, tana ganin Aliyu ya fito a mota ya nufi bangaren Ummi, Abba yace
"Aliyu!"Juyowa yayi yace
"Zo muje bangaren Abbin ku akwai maganar da zamuyi."
Suka juya suka nufi bangaren Abbi, da sauri Mami tabi bayan sa, a falon Abba da Abbi ne da Yayan su Mami zaune akan kujera sai Aliyu da Farouk dake kasa, Mami ce ta shigo da sallama a bakin ta, suka amsa ta karaso tana fadin
"Lafiya kuwa?"Kai Abbi ya girgiza ya fada mata duk abinda ya faru, Zama Mami tayi cike da damuwa tana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"Aliyu ta kalla wanda yake jingine da kujera ta kasa gane a wane hali yake amman tabbas yana cike da shock din abunda yaji. Abbi ya kalli Mami yace
"Kije ki kira Aisha da Maryam har da Inna da Sitti dan suji ko me yake faruwa."Mami ta mike ta fita, Mama ce ta shigo kamar an jefo ta dan hankalin ta a matukar tashe yake bata son wannan auren ya tabbata taki jinin taga Maryam cikin jin dadin rayuwa dan haka ganin shigowar su Abbi ya sa tasan lallai da akwai damuwa, magana zatai Abbi ya daga mata hannu tare da nuna mata waje yace
"Zauna."Zama tayi tana kallon yan dakin, ba a dauki mintina ba Ummi ta shigo dakin tare da Anty Nusaiba autar Inna, ba a jima ba sai ga Inna da Sitti nan sun shigo, cikin kaya iri daya wanda Aliyu ya dinka musu dan yin fitar biki.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...