💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 73By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
_Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani da maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko da nono suyi bul² nono ko yakai silifas yamushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu bashi da side effect mun hadashi da tsirrai da saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state da yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606_'''Mota ya saka Maryam ya dawo wajen Ahmad yace
"Thank you so much friend."
Ahmad ya murmushi yace
"Never mind, yanzu dai matsala ta 'kau, amman please abi da yarinyar nan a hankali kaji?"Wani kallo ya watsa masa yace
"Baka fini son abata ba ai."
Yai gaba yace
"Sai na kira ka.""Ok aci amarci lafiya."
Daga nan ya shiga motar ya tada ta, suka fita daga unguwar, wani super market yai parking ya kalli Maryam da ta lafe jikin kujera yace
" *Matar Haidar* "
Dagowa tai tana kallon sa, hannun ta ya kamo ya dan murza yana sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar masa, yace
"Ina zuwa kinji?"Kai kawai ta gyada ya mata kiss a kumatu ya saki hannun nata tare da fita, super market din ya shiga bai jima sosai ba ya fito aka biyoshi da manya manyan ledoji boot ya bude aka saka kayan ya shiga ya tada mota ya juyo ya kalli Maryam da ya kasa gane a halin da take, hannun ta ya kamo ya fara murzawa a hankali ta d'an d'ago ta kalle shi, ido suka hada tai saurin kawar da idon ta gabanta na faduwa yace
" *Matar Haidar* !"Ido ta lumshe domin kuwa yau ta yadda ta tabbata *Matar Haidar* burin ta kenan a rayuwa Allah ya amsa amman kuma babu iyaye a ciki anya kuwa sunyiwa iyayen su adalci? Abinda ya tsaya mata kenan.
" *Matar Haidar* ya naganki wani iri ne shin bakya murna da wannan ranar da kika zama mallakin Haidar?"
Ya fada yana kamo hannun ta, kai ta girgiza ya kawo hannun ta wajen bakin sa yai kissing din sa yace
"Yau kin zama mallaki na halali na komai zai faru tsakanin mu sai samun lada a cikin sa, so damuwar fa? Fada min uhmmm?"Murmushi ta dan saki tace
"Bani da damuwa Yaya sai tunanin iyayen mu shin mun kyauta musu?"
"A gaba in sukaji abinda mukai sai dai su sa mana albarka tinda ba mu biyewa shaidan ba muka samar wa kanmu mafita mai kyau, yau ko d'a muka samu kinga d'an sunna ne, kuma duk abinda zamu aikata lada zamu samu, na zama naki kin zama tawa kina da hakki akai na nima haka sai muyi fata da addu'a Allah ya cika mana burin mu ya bamu ikon sauke hakkin kowa."Ido ta lumshe ji tayi yana mata wani irin abu a hannu wanda ya kara kashe mata jiki, yace
"Zan kai ki gidan mu na shirya mana shi, ko bayan auren mu zamu cigaba da zuwa muna sha'katawa."Murmushi kawai ta saki, wani mai kaji ya gani ana gasawa wajen har da resturant, parking yayi ya sauka yaje ya siyo ya dawo da ledoji ya saka a baya ya ajiye, ya tayar da mota, lokacin da suka karasa shida saura dan haka suna zuwa ya sauka ya bude gate ya shigar da motar ya dawo ya rufe.
Kofar motar yazo ya bude mata ta fito tana kallon harabar gidan ba sabo bane a wajen ta amman wancan zuwa duk da ana aikin gidan ne sai da aka gama yau gata ta shigo gidan a matsayin matar mai gidan, hannun ta ya kamo ya janyo ta ya rungune ta yana fadin
"Alhamdulillah!"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...