💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 80By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ido ta zaro tana mai girgiza kai kamar zatai kuka tace
"Ni dai dan Allah Yaya kayi hakuri Allah ba zan iya ba."
Mikewa yayi batai aune ba sai jin tayi ya dauke ta gaba dayan ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa yasa ta hakura sai hannun ta da ta zuro ta wuyan sa, tana fadin
"Dan Allah Yaya kayi hakuri ni wallahi kunya nake ji dan Allah ka sauke ni.""In baki min shiru ba har dakin Ummi zamu a haka."
Take tai dif kamar ruwa ya cinye ta a haka suka shiga falon, Allah yaso ba kowa har wata ajiyar zuciya ta sauke zasu shiga dakin kenan Ummi ta fito daga kitchen basu ganta ba dan sun juya mata baya, ita ce ta gansu kai kawai ta girgiza tana mai addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa yasa Aliyu yaso ta su zauna lafiya ya basu zuri'a ta gari.Har bedroom ya shiga da ita ya ajiye ta, akan gado matsawa tayi karshen gado tana takurewa ya karasa wajen kofa ya saka key sannan ya shige bandaki, sai da ya dauki wajen minti ashirin sannan ya fito sanye da armless riga da three quarter sai zuba kamshi yake, kayan sun masa kyau, wajen ta ya karaso ya zauna a gefen ta ya dagata ya daura akan kafar sa, motsu motsu ta fara dan duk ta kasa sakewa, kanta ya dago yana kallonta, ido ta lumshe sai ga hawaye na zuba a idon ta, harshen sa yasa yana share mata su yanayi wasu na zubowa, a hankali yace
"Menene?"
"Dan Allah Yaya ka bari kar Inna taje taga bana nan tazo kuma taga bana nan.""Naga matata ce."
"Dan Allah ka bari Yaya ai ban tare ba."Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Kin fiso na kwana ina fushi dake."
Jikin sa ta shige tana girgiza kai, yace
"To ki shiru ni ba abinda zan miki kawai ina son na kwana a jikin matata ok?"Ido kawai ta lumshe ya kwantar da ita ya tashi ya kashe fitila tana ji ya hawo gadon ya jata jikin sa, rumgume ta kawai yayi yana cusa kan sa a wuyan ta a haka sukai baccin dan ya ga duk ta takura taki sakewa, sai asuba suka tashi, ya shiga bandaki, kan ya fito ta fice ta bar masa dakin, sama ta wuce da sauri ta shiga dakin Haidar karami acan tai wanka tai alwala tai sallah. Sai karfe bakwai ta fita ta gaishe da su Ummi sannan ta koma dakin Inna.
Rukayya ta sama tana ta baccin ta, Inna kuwa na kitchen tana ta hada kayan karyawa a falo ta zauna tana sauraron azkar din da ake yi a TV, idon ta a lumshe bataji shigowar sa ba sai kamshin turaren sa da taji tana bude idon ta ta ganshi durkushe a gaban ta, zama ta gyara tace
"Ina kwana Yaya?"Ido ya lumshe ya bude a hankali yace
"Matar Haidar ta gudu ta bar mijin ta ko?"
Kai ta girgiza ya dan saki murmushi dai dai fitowar Inna da tray ta ajiye, tace
'Menene haka nake gani?"Fuska Aliyu ya hade ya koma ya zauna, baki Inna ta tabe tace
"Kazo zaka takurawa yar mutane me ya kawo ka sashe na da sassafen nan?""Wajen Matata nazo."
"To ba a sashe na ba tashi ka fitar min tinda ka zama marar kunya.""Sai na ciyar da ita tukkuna Inna kawo na bata taci ta koshi sai kici sauran ta."
"Tinda Aisha ce ta girkan ba, Ja'iri."
Ta shiga ta fito da kayan ta shiga daki dan taso Rukayya tea ya hada mata mai kauri dan sosai yaiwa Inna ta'adin madara ya debi dankalin da ta suya da pepper soup ya zuba a bowl ya kalli Maryam yace
"Sauko kici.""Dan Allah Yaya ka tafi ni zanci da kaina."
"Da yawa?"
Yai mata tambayar yana binta da wani kallo wanda yasa duk jikin ta yai sanyi. Kai ta gyada yace
"To shikenan."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...