💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 3By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Tana sauka taga wasu mata dayar babbace amman wacce zatai shekara hamsin saura sai ta gefen ta wacce ba zata wuce shekara talatin ba zaune suna hira, daga gani kasan jini daya ne dan kamar su daya dukka sai dai Ummi da Dayar da suke manyanta, da fara'a ta karasa tana fadin
"Mami."Wacce aka kira Mami ta dauke kai tana fadin
"Ba wani Mami."
Jikin Mami ta kwanta tana fadin
"Kiyi hakuri Mami wallahi makaranta shiyasa bana shigowa."Wacce take zaune ta kalla tace
"Kinji ko? Wai makaranta Muna gida daya sai nai wata ko satituka ban ganta ba in ba fita zanyi ba ko na shigo nan."Jikin Mami ta shige tana fadin
"Mami na kiyi hakuri Ummi ki sa baki "Ummi na murmushi tace
"In zata yadda amman Wallahi Yaya tin kan exam Maryam bata dawo sai magariba, ko Inna kullum sai ta shigo ta min mita."Baki ta gefen Ummi ta tabe tace
"Bare ni dake nesa ko ziyara ta batayi a shekara bai fi tazo sau daya ko biyu ba.""Haba Anty Asiya ai da cewa nai gidan ki zan zo hutu ko Ummi."
Kai ta dauke. Ummi tace
"Haka tace."Mami tace
"To ya jarabawar Daughter?"
"Mami Alhamdulillah.""Allah kawo sakamako mai kyau "
"Amin!"
Duk suka amsa.Mami ta taba jikin ta tace
"Ya naga duk ta rame?"
"Jarabawa Mami.""Gata nan ko abinci bata ci kwana take karatu."
Ummi ta fada. Mami tace
"Ah Daughter kina cin abinci da bacci kinji zakici jarabawa ai kina karatu.""Allah yasa."
"Amin."Sallama suka jiyo ta Aliyu da Haidar duk suka amsa, Haidar ya shigo a guje yai wajen Ummi, Ummi ta dauke shi ta rungume Mami tace
"Au mu ba asan damu ba ko mai gida?"Saukowa yayi ya tafi wajen Mami a guje yana fadin
"Oyoyo."
Ta dauke shi tace
"Ya makaranta Mai gidan?""Fine."
Ta shafa kan sa. Kallon Anty Asiya yayi ya mike a guje yai wajen ta tace
"Yaro na ya girma."Ta sumbaci goshin sa yace
"Ina yini Anty?"
"Lafiya lou Son ya school?""Lafiya lou. Ina su Abid"
"Suna can gidan Garnny din su."Ya tashi ya nufi Maryam yana fadin
"Addah ya exam?""Alhamdulillah!"
"Allah bada sa'a."
Ya fada da kalar bakin sa da magana bata fita sosai.Kallon sa tayi tana murmushi. Aliyu ya karaso sanye yake da milk kalaf wando sai riga longsleeve coffe kala, sai tashin kamshi yake, Ummi a kalla yace
"Ummi barka da gida.""Yauwah ya aiki?"
"Alhamdulillah!"Anty Asiya ta dago tace
"Sannu da zuwa Yaya."
"Yauwah ya gidan da yara?""Lafiya lou."
Ya kalli Mami yace
"Mami Ina yini?""Lafiya lou ya gida?"
"Lafiya lou ""Sannu da zuwa Yaya."
Maryam ta fada tana wasa da Haidar."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...