💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 72By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
''' "Maryam....."
Ya kira sunan ta a hankali da sauri ta dago tana kallon sa, dan kan Haidar ya kira sunan ta ana dadewa in kuwa ya kira ta tabbata babban abu ne, dan haka ta mika masa hankalin ta gaba daya tace
"Na'am Yaya.""Maryam ina da matsala ina da damuwa."
"Amman Yaya baka fada min ba.""Bana son hankalin ki ya tashi bama in kika kasa magancen."
"Allah ba zai kawo abinda zan kasa magance maka ba.""Ko menene?"
Kai ta gyada, ya dago yana kallon ta sai ya dauke ido sa yace
"Maryam ina bukatar ki."Murmushi ta saki tace
"Nasan da haka Yaya."
"Wannan bukatar daban da waccan, a kwanakin baya ina fama da wani ciwon ciki wanda da kai na na gano dalilin sa, aure nake so, mace nake so, da farko na dauki ciwon da wasa amman a yanzu ciwon na neman ya kwantar dani, in yaci jiki na zan iya rasa rayuwa ta a ko da yaushe, solution daya ne Maryam shine nayi aure na tara da iyali na, nayiwa Ummi maganar a matso da auren mu tace wata nawa ne ya rage, a yadda nake ji na Maryam ba zan iya kai wannan lokacin ba ina bukatar mace a tare dani, na sani ko wanne namiji yana da bukatar mace amman ni nawa na yanzu abun yai yawa bansan ya akai haka ba.
A duk lokacin da nazo na ganki na koma hankali na na bala'in tashi nakan rasa nutsuwa ta na kan shiga wani mawuyacin hali wannan yasa na yanke shawarar rage zuwa sai dai shima bata haifar min da d'a mai ido ba dan koyaya naji sautin muryar ki ni kadai nasan halin da nake shiga ga kewa da son ganin ki, Maryam yaya zanyi na rasa madafa."Ya fada idon sa na canja launi, saukowa tayi daga kan kujera ta kama hannayen sa hawaye na zubowa a idon ta na tausayin Aliyu, ya kalle ta, yana share mata hawayen sannan yace
"Matsalar mu kusan daya ce domin kema wannan ciwon marar naki ba zai taba barin ki ba in ba aure kikai ba."Kai ta hau girgizawa tace
"Yaya kana kuma azumin?"
Hannun ta ya kama yace
"Ina yi, amman yanzu da kyar yake kaiwa.""Yaya to ya ya zamuyi?"
"Yaya ko Ammi zanwa magana?""A'ah!"
"To yaya zamuyi? Ka samo mana mafita."
Shiru yayi tace
"Kaji Yaya.""Shikenan zan samo insha Allahu,"
Ya mike yana fadin "Bari na tashi."
"Ina? daga zuwan ka.""Babyyy."
Ya kira sunan ta da wani sauti da yasa sai da tsigar jikin ta ta tashi, ido ta lumshe tana fadin
"Uhmm uhmm Yaya..."
Tai maganar kamar zatai kuka."Ki barni na tafi kar nai abinda ba kyau."
Tai murmushi tace
"Ina kaunar ka Yaya na.""Nima ina kaunar ki Baby na."
Ya nuna mata hanya yace
"Muje!"Ba musu tabi bayansa ya dauki ledar da ya kawo musu abu ya fita, a bakin office din ya tsaya tace
"To Yaya sai gobe ko jibi?"Wani kallo ya aika mata yace
"Sai kin ganni dai."
"Please Yaya kada ka dade kamar yanzu.""To Baby na, wannan shagwabar kara zautani take."
Ta dago tana masa wani kallo ya matso daf da ita yace
"Kina son ki haukatani ko?"Juyawa tai tana girgiza kai hadi da murmushi yace
'Ungo sai munyi waya."
Ya mika mata ta rissina ta amsa tace
"Thank you Yaya."
"Ba godiya hakkinane."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...