Page 34

291 20 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 34

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Satin su Yaa Alkasim daya a Kano suna aikin cigiyar Maryam amman ba wani labari, wanda Ammi ta sa ya samar musu visa suka tafi, lokacin da Ammi taje gida yan uwan ta sunyi murna da zuwan ta duk da daga kallo daya suka gane tana cikin damuwa bayan an bata waje tai wanka taci abinci ta shirya ne, da yamma ta nufi dakin Mahaifiyar ta, Ummu na zaune ta shiga Ammi ta zauna, Ummu tace
"Ina Maryama na zata tare zakuzo ai, tinda ba lafiya ce da ita ba."

Damuwar dake kan fuskar Ammi ce ta kara daduwa tace
"Mahaifin ta ya korata duniya Ummu, bamu san inda Maryam ta shiga ba, na taho akan ba zan koma ba har sai ya nemo min diya ta."

"Me yake faruwa ne?"
Zama Ammi ta gyara tace
"Bayan doguwar jinya da Maryam tayi, mun dawo gida jikin yaki dadi gaba daya wannan yasa muka koma asibiti ana zuwa aka gane tana da ciki har na wata uku da kwanaki."

Shiru duk sukai can Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Ummu, wai ace Abbi ni yake zargi da daurewa Maryam gindin yin ciki ki fada min tayaya zan bar Maryam ta zubar da mutuncin ta, shin ya manta daga gidan da na fito ne ko? Bayan kwana biyu da aka sallamo mu yace sam bai yadda Maryam ta zauna masa a gida ba, ki fada min tayaya haka zata faru, bama wai gidan sa ba har gidan yan uwan sa, a ranar na tura ta gidan Fadima kam na shrya mata tahowa nan, to shine fa tinda ta tafi ba a ganta ba ba duban da ba ai ba, amman ba a ganta ba."

"Innalillahi waina illahir rajiun me ya samu Muhammad ya yanke wannan danyan aikin da ilimin sa da sanin sa?"
"Shaidan."

Mahaifin Ammi ya fada yana shigowa dakin, zama yayi yana kallon Ammi yace
"Shine a lokacin kika kasa kiran kowa ki fada masa sai a yanzu da abin ya lalace, kun batar da yarinyar ku me kika zo yi anan to?"

"Abbu ba zan koma ba har sai ya nemon 'yata."
Wani murmushi Abbu ya saki yace
"Kinsan dai ba a yaji bare saki a gida na ko?"

Kai ta gyada yace
"Yauwa."
Ya mike ya fita, Ummu tace
"To yanzu cikin waye da Maryam din?"

"Ummu nima ban sani ba bamuyi maganar ba ina son muyi ba lokaci."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Na yadda da Maryam, alamarin cikin nan tabbas akwai wani boyayyen abu a ciki, Muhammad bai kamata yai haka ba ya kamata ya bata dama ta fadi na wane in ma nemo sa ne ayi amman ba ace ita taje ta nemo sa ba sam wannan bai yi ba. Ina Malam shi me yace?"

"Daga can muka taho nan yace lallai su nemo Maryam cikin kwana biyu ransa ya baci sosai."
"Dole ai hukuncin da Muhammad ya yanke sam bai dace ba Allah ya kyauta Allah ya bayyana min Maryam dole a tashi da rokan Allah, Allah ya kare ta ya bayyana ta Amin."

Shiru sukai, Ummu tace
"Amman kema baki kyauta ba da kika taho me kike nufi kenan?"
"Ummu tayaya zan iya zama ba Maryam yarinya karama shekarar ta duka duka nawa ko sha takwas fa batai ba Ummu na kasa samun nutsuwa kullum tunani na tana ina, wane waje take, wane hannu ta fada, kar abinda ake zato taje ta aikata dan na tabbata Maryam ba a son ranta ta aikata abinda ta yadda ta aikata ba."

"Haka ne duk da ance ba'a shedar yaro amman nima ina ji a jikina Maryam ba zata taba aikata abinda ake zargi ba wannan boyayyen abun dai Allah ya kawo mai bayyana shi."
"Amin."
Ammi ta fada tana hade kai da gwiwa, dafata Ummu tayi tace
"Ba kuka zaki ba addu'a zaki mata kinji?"

Kai ta gyada tana mikewa ta shiga daki, kwana ta biyu Abbi yazo, zuri'a Alhaji Ahmad suka amshe shi hannu bibbiyu ba tare da nuna komai ba, sai da aka bashi masauki, da dare suna tare da Abbu, Abbi ya dukar dakai yace
"Abbu nayi kuskure wanda tin ba aje ko ina ba nayi nadama wanda bansan har yaushe zan daina wannan nadamar ba."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now