💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 2By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa akan ta, ji take kamar me, baki ya dan cije kamar ba zai magana ba yace
"Jeki."Ta dan durkusa tace
"Nagode."
Ta fita Ummi ta sama a falo ta mike mata ledar tace
"Ummi Yaa Aliyu ne ya bani."Amsa Ummi tai ta leka tace
"Madallah angode."
Sannan ta mika mata tace
"Jeki ajiye."Tayi sama akan gado ta zazzage kayan da wata riga tai arba wacce tin jiya ta burge ta sai dai ganin kudin ta ya hanata dauka sai wasu rigunan da atamfofi da wasu cover shoe masu kyau kamar yasan tana so kamar yasan su suka burge ta, ta d'auka ta ajiye tana murmushi ita kadai.
Kasa ta sauka wajen Ummi suna hira har aka kira magariba. Suka wuce dan yin sallah.
*
Ranar lahadi da dare ya shigo falon, sanye da bakin wando jean sai riga longsleeve mai mabballi blue black ba karamin kyau kayan sukai masa ba sai hasken sa ya kara fitowa gashin kan nan nashi kwance sai shekki yake, fuskar sa tai wani fresh sai kyalli yake, kamshin sa kuwa ya gama cika dakin, Ummi da Maryam ne zaune Maryam na kallon Bollywood da suke wani indian film mai kyau. Akan kujera ya zauna Haidar ya karasa ya zauna kusa da Maryam yana mata surutu. Ta dago ta kallli Aliyu ta dauke kai tare da fadin
"Sannu da zuwa.""Yauwah!"
Ya fada yana lumshe idon sa, sai kuma ya dago ya kalli Ummi yace
"Ummi dole fa yarki ta rage kallon nan in har karatun take son yi dan karatun su ba wasa a ciki."Dagowa Ummi tayi ta kalli Maryam tace
"To ai gaka ga ta nan sai kai mata fadan ko?"Ya juyo ya kalle ta, wanda yai saurin dauke idon sa yace
"To ban da kule kulen samari ki tsaya kiyi abinda ya kai ki."
"Insha Allahu."Ya mike yana fadin
"Bari na shiga daga ciki Ummi."
"Kaci abinci ne son?"Ciki ya shafa ya girgiza kai yace
"Ummi yau ciki na a cunkushe yake sam bana son cin komai.""A'ah fadi me kake so sai ai maka yanzu."
"A'ah zan ci komai kukayi ma.""Yauwah to"
Ta kalli Maryam tace
"Hada masa abinci ki kai masa."Ta mike ta fara hadawa ta gama ta nufi dakin nasa. Ba kowa a ciki dan haka ta ajiye ta juyo tana kaiwa kofa ya fito juyowa tayi ta kalle shi sanye da jallabiyya yake blue black tace
"Ga abincin ka nan inji Ummi."Tana fada ta juya ta fita. Shima daki ya koma ciki, gado ne kato wanda yake lullube da farin bedsheet dakin sai kamshi kan gado ya fada yana mai lumshe idon sa. Can ya mike ya dauki wayar sa ya fara neman layin sitti. Ba a jima ba ta dauka ya kai kunnen sa yace
"Ni dai sam yanzu Sitti bata so na bare ta damu dani.""A duk duniya kana daya daga cikin wanda na fi kauna ba ranar Allah da zata bude ban yi maganar ka ba Abin so. Ina kaunar ka da tausayin ka, ina fatan kuma Allah ya baka mai kula da kai kamar marigayiyar matar ka. In ban kula da kai ba da wa zan kula Abin so?"
Kai ya langwabe kamar tana kallon sa yace
"Nayi kewar ki har ba adadi."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...